Connect with us

Manyan Labarai

An cigaba da sauraren karar matashin da ya yada auren shugaba Buhari

Published

on

Kotun majistret mai lamba, (72) mai zamanta a unguwar Noman’s land a jihar Kano, ta dage sauraron karar nan wadda hukumar tsaro ta farin kaya DSS suka gurfanar da wani matashi mai suna Kabiru Muhammad wanda hukumar take zargin sa da yada labarin kanzon kurege dangane da batun cewar shugaba Buhari zai auri Minista Sadiya Faruk.
Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il, ya rawaito cewa, koda yake har a yau dinnan ma hukumar bata gabatar da kunshin tuhumar a gaban kotun ba.
Yanzu dai haka matashin, Kabiru Muhammad, wanda a ke zargi da yada labarin auren shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a shafukan sada zumunta, wanda ya jawo ce-ce-kuce a fadin Nijeriya yanzu haka dai ya na ci gaba da zaman sa a gidan ajiya da gyaran hali, har sai an kara sauraron karar a nan gaba.

Manyan Labarai

DPO’s ɗin mu duk wanda ya zo belin ƴan Daba ku riƙeshi – Kwamishinan ƴan sandan Kano.

Published

on

Rundunar ƴan sandan Kano ta ce ta samar da rundunar yaƙi da ƴan Daba da ƴan Fashi da makamai, da suke addabar mutane a unguwar Ɗorayi ƙarama, tare da samar da gwangwanin Barkonon tsohuwa guda dubu ɗaya dan fara kakkaɓe ƴan Daba a yankin.

Kwamishinan ƴan sandan jihar CP Muhammad Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan yayin wani taro na musamman da suka gudanar da masu ruwa da tsaki na unguwar Ɗorayi, da ya gudana yau a yankin wanda Kwamishinan ya jagoranta, domin lalubo hanyoyin magance matsalar tsaro a yankin.

CP Gumel, ya kuma umarci baturan ƴan sanda a faɗin jihar Kano, da su riƙe duk wanda yazo karɓar belin ƴan fashi da makamin da ta kama, kamar yadda wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito.

A ƴan tsakanin nan ne dai wasu rukunin matasa suka addabi al’ummar yankin na Ɗorayi, inda aka zargi sun yi kan mai uwa dawabi akan mutane da sara, tare da ƙwacen wayoyin al’umma, bayyana da aka ce sun rarraba takardu kan cewar za su kai harin tare da hana yin sallar Tarawi.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun sami karamar hukumar birni a cikin mawuyacin hali:Hon Bashir Chilla

Published

on

Shugabancin ƙaramar hukumar Birni na riƙo dake nan jihar Kano ya ce bayan karɓa wannan ƙaramar hukumar sun same ta cikin muhuyacin hali, kasancewar yadda sakatariyar take babu gyara babu kuɗi.

Shugaban karamar hukumar na riƙo Hon Bashir Baba Chilla ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a wani ɓangare na samarwa da ƙaramar hukumar Birni ci gaba.

Chilla ya kara da cewa sun sanya idanu kan ma’aikatan da suke aiki a wajen domin zuwa aiki akan lokaci da kuma gudanar da aiki yadda aka tanada domin sauke hakkin al’umma.

Akwai matsalar huta da wannan sakatariyar take fuskanta ta yadda a kullum takan zama babu huta sakamakon rashin kula da injin da yake bayar da huta,amma kawo wannan lokacin an samu gyara shi, inda yanzu haka huta ta samu a cikin sakatariyar, A cewar Chilla.

Akwai matsalar ƴan kilisa da wannan ƙaramar hukumar take fuskanta, adon haka ya zama wajibi shugabancin ƙaramar hukumar ya dau mataki domin kawo ƙarshen wannan ɓarna da ake yi a yayin hawan kilisar.

Haka kuma muna so musamar da kyakkyawan tsaro a ƙaramar hukumar shiyasa yanzu haka muka kafa wani kwamiti wanda zan sanya idon ko ta kwana musamman a wannan lokaci na ƙaratowar sallah karama.

Muna kira ga iyaye da su sanya idanu kan ƴaƴan su domin kaucewa rikice rikice da ake samu na yau da kullum a wannan ƙaramar hukumar.

Zamu tabbatar mun sanya idanu kan asibitocin mu da suke ƙaramar hukumar Birni domin bayar da kulawar lafiya ga dukkanin al’ummar da suke yankin ƙaramar hukumar.

Akwai tsarin da ƙaramar hukumar Birni tayi wajen bayar da tallafin abinci ga al’ummar ƙaramar hukumar ƙarkashin jagorancin gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf domin rage matsin rayuwa da al’umma suke ciki.

Hon Bashir Baba Chilla ya ce a wannan lokaci Ramadan an sami matsalar ciyarwa a wata santa da take ƙarƙashin sa wanda hakan baiyi daɗi ba kuma cikin ƙanƙanin lokaci aka sami canji, domin gudanar da abin da gwamnati ta tsara.

Ina kira ga al’umma duk abin da zasuyi su kasance sunyi abin su tsakanin su da Allah domin hakki ne da aka ɗorawa mu ku.

Domin wannan tsarin na ciyarwa a buƙatar ya isa ga kowa da kowa musamman bamuƙata da suke faɗin jihar nan.

Continue Reading

Manyan Labarai

Yan baro a kasuwar sabon gari sun gudanar da zanga – zangar lumana a titin gidan gwamnati.

Published

on

Ƙungiyar ƴan baro dake kasuwar sabon gari a jihar kano, sun gudanar da zanga-zangar lumana akan titin gidan Gwamnatin jihar Kano, inda suke zargin shugabancin kasuwar da tilasta musu tashi daga guraren da suke gudanar da kasuwancin su a kasuwar, lamarin da hakan ke barazana da rayuwar su.

Shugaban ƙungiyar Tasi’u Ibrahim, ne ya jagoranci zanga-zangar lumanar a yau Laraba, inda suke kira ga mahukunta wajen duba halin da za su shiga idan har aka tilasta musu tashi daga kasuwar sabon garin a wannan lokaci, inda suka ce sun kwashe tsawon lokaci suna gudanar da kasuwancin su a nan amma sai gashi lokaci guda an hanasu.

Da yake nasa jawabin jim kaɗan bayan zanga-zangar lumanar shugaban kasuwar ta Sabon Gari Alhaji Abdul Bashir Hussain, ya ce ana yawan samun matsala da yawaitar korafe – korafe akan yan baron wanda hakan tasa shugabancin kasuwar ya zauna da masu ruwa da tsaki daga ciki harda jami’an tsaro domin shawo kan lamarin.

Abdul Bashir ya kara da cewa akwai wani tsari da shuagabancin kasuwar ya yiwa ƴan baron na sama musu makoma, wanda hakan zai kawo karancin samun cinkoso a cikin kasuwar ta sabon gari.

Continue Reading

Trending