Connect with us

Manyan Labarai

An harbe matashi har lahira a Kano

Published

on

Wasu ‘yan fashi da makami da ba a iya gane su ba dauke da bindigogi a na zargin sun shiga gidan wani mutum mai suna Alh. Munir Na’iya a unguwar Hotoron Maradi dake karamar hukumar Tarauni.

‘yan fashin sun karbe masa tarin kudi masu yawa a cikin jaka kafin daga bisani su ka tafi suna harbe-harbe a iska a yammacin ranar Laraba.

A zantawarsa da gidan rediyon Dala Alh. Munir ya ce, “Ina kwance na ji su na buga min gidana, sun tadda mata a daya gidan, na za gaya na fita sai su ka shigo da ni, su na harbe-harbe, su kace kudi na ce to, kafin ma na  hau sama wani ya shiga su ka ta harbe-harbe su ka fita”. A cewar sa.

Ita kuwa ‘yar mai gidan Fatima Munir ta ce, “Mu na zaune sai na ga baban mu ya fito da sauri, fitowar da za mu yi bakin kofa sai na ga sun rike baban mu, sai na ce mai za ku yi wa baban mu, me ya yi muku? Sai babar mu ta riko wuyanta sai ya sakar ma ta bindiga, ni kuma ganin ya sakar ma ta bindiga sai na riko wuyan dayan, sai ya kifa min mari”.

Bayan ‘yan fashin sun fito daga gidan ne su ka fara harbe-harbe wanda sanadiyar hakan ne a ka yi zargin sun harbe makocin Alhajin, mai suna Ali Usman har lahira kamar yadda abokin sa da su ke tare a lokacin ya shaida mana, “Mu na dakina mu na kallo da wanda ya rasu, sai wani abokina ya shigo ya ce unguwar nan babu lafiya ya ce ya ga wasu mutane sun yi sallama da makocin mu su na harbe-harbe sun shiga gidan, mun fito bayan sun wuce sai mu ka ga an harbi abokin namu”. Inji abokin marigayin.

Kazalika mun tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bakin Kakakin ta DSP Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya ce, za su bincika al’amarin.

Manyan Labarai

Za’a ɗauki mataki akan duk wanda yake da hannu Gini ya ruftawa mutane a Kuntau – Ƙaramar hukumar Gwale.

Published

on

Yayin da wani ginin Bene mai hawa biyu ya danne aƙalla sama da Leburori goma a unguwar Kuntau kusa da KEDCO, a safiyar yau Juma’a, Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwale Abubakar Mu’azu Mojo, ya ce za’a ɗauki mataki akan dukkan wanda aka samu da laifi har al’amarin ya faru.

Abubakar Mu’azu Mojo, ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da manema labarai, yayin da ya ziyarci gurin da lamarin ya faru lokacin da ake ci gaba da aikin ceto mutanen.

Mojo, ya kuma ce babu makawa za’a ɗauki matakin doka akan duk wanda aka samu da hannu akan faruwar lamarin, kama daga ɗan kwangilar da aka bai wa aikin ginin, zuwa kuma mamallakin gidan.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa tsakar ranar yau aƙalla mutane bakwa aka ciro daga ƙasan ginin shida daga cikin su basa iya motsa jikin su, yayin da hukumomi suka ci gaba da gudanar da aikin ceto sauran mutanen da ginin ya danne.

Continue Reading

Manyan Labarai

Sulhu da ƴan Bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba – Human Rights 

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasa da ƙasa wato International Human Rights Commission, ta ce sulhu da ƴan bindiga ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasar nan.

Babban daraktan ƙungiyar Kyaftin Abdullahi Bakoji Adamu mai ritaya, shi ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.

Ya ce kasancewar ƴan bindigar basu da wata manufa bai kamata ayi sulhu da su ba, mai-makon hakan yafi dacewa a rinƙa ɗaukar tsauttsauran mataki akan su duba da yadda suke cutar da al’umma.

Ya kuma ce batun da mai bai wa shugaban ƙasa akan sha’anin tsaro Malam Nuhu Ribaɗo, ya yi a baya baya nan, kam cewar an fara samun fashimtar juna da wasu daga cikin ƴan Bindigar da suka addabi mutane a sassan ƙasar nan, a wani ɓangare ma kama da yin sulhu da su, ya faɗi hakan ne kawai amma hakan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta kulle wata makaranta mai zaman kan ta a jihar

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wata makaranta mai suna Golden Crown International School a jihar, da ke yankin Sabon gari, bisa zargin an fake da sunan makarantar ana haɗa magani mara inganci mai-makon koyar da karatu a ciki.

Shugaban kwamitin yaki da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya na jihar Kano General Gambo Mai Aduwa Mai ritaya, ne ya bayyana hakan, a lokacin da Kwamitin ya kai wani sumame da karfe uku da rabi na daren jiya Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa makarantar tana kan titin Zungero da ke cikin ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano, wanda bayan samun bayanan sirri aka ɗauki matakin kulle ta.

Mai Aduwa, ya ƙara da cewar tsarin gurin ta waje ya nuna makaranta ce amma kuma sai ake sarrafa magani da ake zargin ingancin sa da bai kai yadda ya kamata ba, tare da ajiye Allurai da kayan haɗa magani cikin ajujuwan mai-makon ɗalibai.

“Za mu faɗaɗa bincike akan al’amarin dan sanin matakin da za mu ɗauka na gaba, “in ji shi”.

Suma masu gadin gurin da muka zanta da su sun bayana cewar, aikin gadi kawai suke yi amma basu da masaniyar abubuwan dake gudana a cikin makarantar, da ake zargin ana sarrafa magani mara ingani da ajiye shi a muhalin da ake zargin bai yi dai-dai da tsarin doka ba.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa shugaban kwamitin ya ce, zai ci gaba da bibiyar guraren dake yin abubuwan da za su kawo koma baya ga harkokin lafiya, da ci gaban jihar Kano, musmman wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya.

Continue Reading

Trending