Connect with us

Labarai

Kowa ya dawo da kujerar da ya yi karatu a kanta: WTC Kano

Published

on

Shugabar kungiyar tsofaffin daliban makarantar horas da malamai mata ta WTC wadda ta koma GGC KANO a yanzu Farfesa Fatima Muhammad Umar ta ce kungiyar ta dauki tsarin ne kowaccensu ta dawo da madadin kujerar da tayi karatu akanta lokacin tana daliba da nufin Samar da isassun kujerun Zama a tsohuwar makarantar tasu.

Farfesar ta bayyana hakan ne a lokacin babban taron kungiyar Mai shekaru 73 da kafuwa yau Asabar a harabar makarantar.

Ta Kuma ce da tsarinne na kowa ya dawo da kujerarsa me taken (bring back your chair) yanzu haka suka samu nasarar samarwa da makaranatar Karin kujerun Zama 1380, a hannu guda Kuma suka Samar da rijiyar burtsatse da Kuma gyaran wadanda suka lalace, Baya ga sada zumunci da suke yi a tsakanin su ta dalilin kungiyar.

A nata bangaren tsohuwar daraktar makarantar Dr. Mariya Aliyu Waziri, tace dukda irin gudunmawar da manyan fitattun matan da makarantar ta yaye irinsu matan gwamnoni dama wadanda suka rike ko Kuma suka rike manyan mukamai suke bayarwa wajen bunkasar makarantar, akwai bukatar su ringa Sanya ‘ya’yansu a makarantar maimakon su ringa kaisu manyan makarantun kudi koma kasashen waje, ta yadda makarantar zata ci gaba da Zama a zuciyarsu su Kuma ci gaba da taimaka mata a koda yaushe.

Wakilinmu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito cewa a taron ya samu halartar wasu dada cikin manyan tsofaffin daliban makarantar irin su Mai dakin gwamnan Kano hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje da Kuma Mai dakin gwamnan jihar Jihagawa, harma da sauran tsofaffin dalibai dama sauran masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi inda aka gabatar da jawabai daban-daban kan muhimmancin kungiyoyin tsofaffin dalibai na taimakawa gwamnati kan ci gaban ilimi dama Kuma muhimmancin ilimin baki daya musammanma na ‘ya’ya mata.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending