Connect with us

Labarai

Dalilan da ya sa mata suka wuce maza a karatun kur’ani -Farfesa Isa Hashim

Published

on

Farfesa Isa Hashim ya ce mata sun fi maza basira, juriya da hakuri a bangen karatun addini, wanda hakan ya sanya ko a yaushe matan ke wuce maza a lokutan saukar karatun alkur’ani mai girma a makarantun Islamiyyu.

Farfesa Isah Hashim wanda shi ne Jarman Kano a yanzu, ya bayyana hakan ne a lokacin saukar karatun alkur’ani mai girma na dalibai maza 25 da Kuma mata 37 ciki harda wadda ta haddace alkur’anin a makarantar Imamu Dalhatu Islamiyyu sorondinki wanda wannan shi ne karo na 3 da saukar da a ka yi a cikin karshen makon da ya gaba.

Ya Kuma ce” Basirar da juriyar da kuma hakuri na daga cikin manyan sharudan samun ilimi, wanda kuma da yawa daga cikin maza basu da su, sabo da yadda suke shagaltuwa wajen sauke nauyin da Allah ya dora musu na gwagwarmayar nemo abun bukatar yau da kullum”. Inji Jarman Kano.

A nasa bangaren shugaban makarantar Habibu Abbas ya ce” Kamata ya yi mazan su rinka mayar da hankali a kan karatun su musamman ma a lokacin da suke matakin kuruciya, tun kafin su girma nauyin rayuwa ya yi musu yawa”.

Ita kuwa dalibar guda daya tilo da ta samu haddar alkur’anin daga cikin dalibai 65 din da suka sauke, Fari’atu Yusuf Yakubu, ta ce “duk da cewar haddar daga Allah ne amma, hakuri da juriyar sune sirrin samun haddar ta wa”. Inji Fari’atu.

Wakilin mu Ibrahim Abdullahi Sorondinki ya rawaito cewa, daga cikin daliban akwai wadanda suka fara haddar inda suke kan matakin izufi talatin a halin yanzu.

Ilimi

Mun shirya yin aiki tare da masarautar Gaya – SEDSAC

Published

on

Kungiyar bunkasa ilimi da ci gaban demokradiya ta SEDSAC ta ce masarautar Gaya itace masarauta ta farko da kungiyar za ta yi hadin gwiwa da ita, domin ci gaba da samar da shirye-shirye da ya shafi rayuwar al’umma.

Sanarwar ta fito ne ta hannun daraktan kungiyar, Kwamrade Umar Hamisu Kofar Na’isa, ta na mai cewa, za ta yi hadin gwiwa da dukannin masauratu Biyar na Kano, domin bunkasa rayuwar al’umma tare da samar da ci gaba a kasa.

SEDSAC ta kuma yabawa gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma ma su zaben sarki a Gaya, bisa nada Alhaji Ali Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin sabon sarkin Gaya, wanda kuma ya na daya daga cikin jigon iyaye na kungiyar SEDSAC.

Haka zalika SEDSAC ta kuma taya sabon sarkin murnar sarautar da ya samu tare da yi wa marigayi tsohon Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir Gaya, addu’ar neman gafara a wajen Ubangiji.

Continue Reading

Labarai

Ba ma samun kulawa a wajen Gwamnati – Masu sana’ar Shuke-shuke

Published

on

Kungiyar masu Shuke-shuke ta kasa reshen jihar Kano ta koka dangane da rashin kulawa daga gwamnati wajen siyan tsirrai daga wurin su.

Shugaban kungiyar, Aliyu Shehu Kabara, ya bayyana hakan, yayin taron shekara da suka gudanar a jihar Kano a karshen makon da ya gabata.

Ya na mai cewar, “Yawancin lokuta gwamnati kan tashi masu sana’ar Shuke-shuke ba tare da samar musu da wasu wuraren ba”. Inji Aliyu Shehu Kabara.

A nasa jawabin, wani masani a kan harkokin tsirrai daga Jami’ar Bayero ta Kano, Malam Hassan Usaini, ya ce, “Akwai gudunmawa mai tarin yawa da masu lambuna ke bayarwa, a fannin muhalli da kuma ilimi, wanda suma mata akwai bukatar su shigo cikin harkar domin bayar da gudunmawa”.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya ruwaito cewar, masu lambunan sun yi fatan gwamnati da sauran hukumomi, za su hada hannu da su, domin samar da ingantaccen muhalli.

Continue Reading

Labarai

Za mu hana shan Shisha a bainar Jama’a – Hukumar yawon bude ido

Published

on

Hukumar yawon bude ido ta jihar Kano ta ce, za ta hana shan Shisha a bainar Jama’a tare da hana kananan yara zuwa Otel da zarar gwamnati ta sanya wa dokar hannu.

Babban Manajan Daraktan hukumar, Yusuf Ibrahim Lajawa ne ya bayyana hakan,  a ganawar sa da gidan radiyon Dala a ranar Litinin.

Ya ce, “Tsofaffin wuraren da ake gudanar da Rini, dama wuraren da ake gudanar da Jima, na daya daga cikin ababen da mu ka sanya, a cikin  kasafin kudin hukumar a Bana”. A cewar Lajawa.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa, Yusuf Ibrahim Lajawa ya kuma ce, aikin hukumar ta su ya ta’allaka ne kadai wajen janyo ra’ayoyin al’umma, daga ko’ina domin zuwa jihar Kano domin yawon bude ido.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!