Connect with us

Labarai

Aiki tare da al’umma ne jigon nasarar tsaro- AIG Ahmad Iliyasu

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta shiryawa tsohon Kwamishinan ‘Yansandan Kano liyafar bankwana a karshen makon da ya gabata a shelkwatar rundunar dake Bomfai a jihar Kano.

Kwamishinan ‘yansandan Kano Habu Ahmad Sani, ya bayyana cewar, “Bisa al’adar rundunar ta na shiryawa kowanne kwamishina makamancin taron da zarar ya samu sauyin wurin aiki domin kara bashi kwarin gwiwa.”  Inji CP Habu Sani

Habu Sani, ya kuma bayyana tsohon kwmishinan Ahmad Iliyasu wanda likafarsa ta daga zuwa mataimakin babban Sifeton ‘yansanda mai lura da shiya ta biyu dake jihar Lagos, a matsayin wanda ke bayar da muhimmiyar gudunmawa ta fannin tsaro.

Da yake nasa jawabin tsohon Kwamishinan ‘Yansandan, Ahmad Iliyasu, cewa yayi, “Aiki a tsakanin ‘yansada da jama’a shi ne jigon cimma nasarar samar da tsaro.”                                             

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewar, AIG Ahmad Iliyasu, ya kuma gargadi ‘yansanda wajen sanya gaskiya da tsoron Allah (S.W.T) yayin gudanar da aikin su na tsare rayuka da dukiyar al’umma.

Labarai

Rahoto: Addu’a ce babbar hanyar magance matsalar tsaro – Dagaci

Published

on

Dagacin Sharada Alhaji Iliyasu Mu’azu Sharada ya ce, al’umma su yawaita yin addu’a domin ita ce babbar mafita wajen magance matsalolin rashin tsaro.

Alhaji Iliyasu Mua’azu, ya bayyana hakan ne yayin da wata kungiya mai suna Sharada Foundation ta mika masa na’urar over-over guda takwas a rabawa kungiyar ‘yan sintiri ta Bijilante da ke yankin domin inganta harkokin tsaro.

Saurari Abba Isah Muhammad domin jin cikakken rahoton.

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Ana zargin ‘yan ta’adda sun yi wa matashi yankar Rago a Kano

Published

on

Ana zargin wasu matasa a unguwar Danrimi, Rijiyar Lemo da ke karamar hukumar Ungogo, sun shiga dakin wani mutum sun yi masa yankar Rago daga bisani kuma dauke wayar sa.

Marigayin mai suna Shu’aibu Bichi mai sana’ar adaidaita sahu, ‘yan ta’addan da ba a san ko su waye ba sun shiga dakin sa bayan sun lura bai rufe dakin ba, su ka yanka shi, sannan kuma suka dauke wayarsa.

Saurari Abubakar Sabo domin jin cikakken rahoton.

 

 

 

 

 

 

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Zaman gidan gyaran hali ya sa na daina shaye-shaye – Matashi

Published

on

Kotun majistiret mai lamba 1 da ke Kofar Kudu, wani matashi ya sake gurfana a gaban kotun kan zargin shiga gidan mutane bayan sha kayan maye ya na tsammanin gidan su.

Matashin bayan an karanta masa kunshin tuhumar ya amsa laifin sa, sai dai ya bayyanawa kotun cewar, bai sai ya shiga gidan mutanen ba domin ya yi tunanin gidan su ne.

Domin jin cikakken rahoto saurari Ibrahim Abdullahi Sorondinki.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!