Connect with us

Manyan Labarai

Kano: Ana zargin wasu mata da sace kayan daki

Published

on

Ana zargin wasu mata masu zaman kansu a wani gida dake unguwar Kwajalawa, a yankin Dakata Kawaji, da sace kayan daki da suka hada da Katifa da Matasan kai, Sutturu, Takalma, Kudade, da kuma Tukwanen miya.

Gungun matan, ana zargin kowacce ta kama dakin ne a wannan gida tare da wasu mata masu sana’ar siyar da abinci, ya da kanwa, da su ka zo daga jihar Adamawa, suma kuma su ka kama daki su biyu, inda aka yi zargin matan ‘yan Adamawa, sun hada kai sun balle dakin masu sana’ar sayar da abincin.

An gurfanar da su a gaban kotun shari’ar musulunci dake unguwar Birget PRP, karkashin mai shari’a Mujittafa Abdulkadir, bayan kuma an karanta musu tuhumar, sai su ka mu sa  zargin su ka ce, ba su su ka yashe dakinba.

Kotun ta sanya su a hannun beli, tare da yi musu wa’azin, su ji tsoran Allah su daina abin da su ke yi su koma mata na gari, su nemi mazaje su yi aure.

A zantawar wata da ake ganin jagora ce a cikinsu Zainab Ibrahim da wakilinmu Abubakar Sabo, ta ce, “Mun ji dadi mun gode, kuma tunda dai, mu din an same mu ta hanyar aure ne, to za mu yi duk mai yuwa muma mu ga mun yi auren, domin dai ba za mu so dawwama a layin da muke kai ba.”  A cewar Zainab

Labarai

Rahoto: Harbi 6 mu ka yi wa Kadar kafin mu kama ta – Baushe

Published

on

Wasu mafarauta mutum biyu sun yi nasarar kama katuwar Kada a wani kududdufi da ke unguwar Jakada, Dorayi babba a karamar hukumar Gwale.

Baushe Liti daya daga cikin wadanda suka kama Kadar ya bayyanawa wakilin mu Tijjani Adamu cewar, sun dauki lokaci suna harbin katuwar Kadar kafin daga bisani su ci nasarar kama ta.

Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

 

Continue Reading

Labarai

#SecureNorth: Mun gaji da salon mulkin Buhari – ‘Yan Najeriya

Published

on

Ƴan Najeriya sun fara kosawa da salon mulkin gwamnatin kasar da suka ce ta yi biris da sha’anin tsaro.

Wannan na zuwa ne yayinda al’amauran tsaro a arewacin kasar ke kara tabarbarewa, a dai-dai lokacin da alhinin mutuwar manoma 43 da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka yi musu yankan rago a jihar Borno.

Al’ummar kasar dai na ganin munin matalsar tsaro na kara ci musu tuwo a kwarya, lamarin da ya sanya da dama daga cikin al’ummar kasar suka fusata, inda suke bayyana ra’ayoyinsu a kafafen sada zumunta.

Abinda kuma ke yawo a kafafenn sada zumunta baya ga batun sai Buharin ya sauka daga mulkin kasar, shine batun a sallami hafsoshin tsaro, akan abinda ‘yan Najeriya ke cewa sun gaza magance matsalar tsaro da ke kara kamari musamman, a arewacin kasar.

Haka zalika al’ummar Najeriya sun ce shugaban ya gaza cika musu alkawuran da ya dauka a lokacin da yake neman kujerar shugabancin kasar, a yayinda tsadar rayuwa ke ci musu tuwo a kwarya.

Yanzu haka dai hankulan mazauna arewa maso yamma da ke fama da matsalar fashi da makami da kuma garkuwa da mutane a tashe yake, yayinda mazauna yankin arewa maso gabashin kasar ke cikin tashin hankali.

Tun bayan yankan ragon da aka yiwa manoma a kauyen Zabarmari na jihar Borno ne, hankulan jama’a ya kara karkata, yayinda ake ganin mazauna arewacin kasar na cikin tashin hankali, sakamakon tabarbarewar tsaro.

Rundunar sojin Najeriya ta ce har yanzu ana neman wasu daga cikin mutanen da harin ya rutsa da su, yayin da wasu ƴan ƙasar ke ganin ko shugaba Muhammadu Buhari ya tashi tsaye wajen magance matsalar tsaron ko kuma ya sauka daga mulki.

Me ke faruwa a Arewa maso Yamma?

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya ce manoma 110 ne aka kashe a Zabarmari na jihar Borno, ba 43 ba kamar yadda hukumomin tsaron kasar suka ce.

Majalisar ta bayyana wannan harin a matsayin abu mafi muni da aka yiwa fararen hula, cikin shekarar 2020 a duniya.

A dai-dai lokacin da ake zaman makokin mutuwar manoman ne, kuma rikici ya balle a jihar Kaduna da ke Arewa maso Yammacin Najeriya, inda rahotanni suka tabbatar da mutuwar mutum bakwai, sai kananan yara da suka tsere bayan da wasu na daban suka jikkata.

Bayan kwana guda da barkewar rikicin ne, wasu ‘yan bindiga suka tare hanyar Zaria zuwa garin Kaduna, inda suka jikkata mutane, ko da yake kawo yanzu ba a tabbatar da mutuwar ko da mutum guda ba.

Continue Reading

Labarai

Rundunar sojin Najeriya ta karyata rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan kisan manoma a Borno

Published

on

Rundunar sojin Najeriya ta nanata cewa manoma 43 aka kashe, ba 110 da Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe.

Mai Magana da yawun rundunar, John Enenche a wata hira da ya yi da gidan talibijin na Channels, ya ce har yanzu suna tattara bayanai kan mutanen da harin ya shafa domin tabbatar da adadin wadanda suka mutu.

Sai dai rundunar ta ce abinda yake kara ta’azzara batun matsalar tsaro shine, yadda mazauna yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula ba sa kai rahoto ga sojoji da sauran hukumomin tsaro kan halin da suke ciki.

“Mutane da dama basa kawo mana rahoton abinda ke addabar su kan sha’anin tsaro, kuma ba dole bane ka tilastawa mutane su sanar maka abinda ke faruwa.” In ji shi

Ko da yake John Enenche ya ki bayyana yanda rundunar sojin ke tattara bayanata akan wuraren da fama da yake-yake a arewacin Najeriya.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!