Connect with us

Manyan Labarai

Wasu matasa sun fada tarkon NDLEA

Published

on

Hukumar Hana she da safarar miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA ta tabbatar da kama wani mutum mai suna, Emanual Okasia, da a ke zargin yana safarar tabar wiwi daga kudancin Nijeriya zuwa jihar Kano da kuma wani mai suna Anas Wada Adamu, da ya fake da sana’ar wasan Sunuka ya na sayarda tabar wiwi a karamar hukumar Kura.

Kwamandan hukumar a jihar Kano Dakta Ibrahin Abdul, ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da gidan rediyo Dala Fm da safiyar Laraba a shelkwatar hukumar dake kantitin zuwa filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.

Ibrahim Abdul, ya kuma kara da cewar” Hukumar ta tashi tsaye wajen kawo karshen masu safarar miyagun kwayoyi, kuma za mu gurfanar da wadanda muka kama a gaban kotu domin yanke musu hukunci da zarar sun kammala bincike”.

Da yake zantawa da wakilin mu Abba Isah Muhammad, Emanual Okasia, ya tabbatar da cewar” Hukumar ta kamani da buhun tabar wiwi fiye da buhu ashirin wanda na yi safarar ta zuwa Kano”.

Shima Anas Wada Adam, da ake zargin ya na fakewa da Sana’ar wasan buga Sunuka, yana sayar da tabar wiwin, ya ce” Cesarean abokin na ne ya bani tabar domin na siyar na gyara wurin sana’a ta”.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad, ya ruwaito cewar kwamandan hukumar ta NDLEA, Dakta Ibrahim Abdul, na yabawa masu bawa hukumar bayanan sirri wanda hakan ke taimakawa kokarin hukumar.

 

 

 

Ilimi

Mun shirya yin aiki tare da masarautar Gaya – SEDSAC

Published

on

Kungiyar bunkasa ilimi da ci gaban demokradiya ta SEDSAC ta ce masarautar Gaya itace masarauta ta farko da kungiyar za ta yi hadin gwiwa da ita, domin ci gaba da samar da shirye-shirye da ya shafi rayuwar al’umma.

Sanarwar ta fito ne ta hannun daraktan kungiyar, Kwamrade Umar Hamisu Kofar Na’isa, ta na mai cewa, za ta yi hadin gwiwa da dukannin masauratu Biyar na Kano, domin bunkasa rayuwar al’umma tare da samar da ci gaba a kasa.

SEDSAC ta kuma yabawa gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje da kuma ma su zaben sarki a Gaya, bisa nada Alhaji Ali Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin sabon sarkin Gaya, wanda kuma ya na daya daga cikin jigon iyaye na kungiyar SEDSAC.

Haka zalika SEDSAC ta kuma taya sabon sarkin murnar sarautar da ya samu tare da yi wa marigayi tsohon Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Abdulkadir Gaya, addu’ar neman gafara a wajen Ubangiji.

Continue Reading

Labarai

Ba ma samun kulawa a wajen Gwamnati – Masu sana’ar Shuke-shuke

Published

on

Kungiyar masu Shuke-shuke ta kasa reshen jihar Kano ta koka dangane da rashin kulawa daga gwamnati wajen siyan tsirrai daga wurin su.

Shugaban kungiyar, Aliyu Shehu Kabara, ya bayyana hakan, yayin taron shekara da suka gudanar a jihar Kano a karshen makon da ya gabata.

Ya na mai cewar, “Yawancin lokuta gwamnati kan tashi masu sana’ar Shuke-shuke ba tare da samar musu da wasu wuraren ba”. Inji Aliyu Shehu Kabara.

A nasa jawabin, wani masani a kan harkokin tsirrai daga Jami’ar Bayero ta Kano, Malam Hassan Usaini, ya ce, “Akwai gudunmawa mai tarin yawa da masu lambuna ke bayarwa, a fannin muhalli da kuma ilimi, wanda suma mata akwai bukatar su shigo cikin harkar domin bayar da gudunmawa”.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya ruwaito cewar, masu lambunan sun yi fatan gwamnati da sauran hukumomi, za su hada hannu da su, domin samar da ingantaccen muhalli.

Continue Reading

Labarai

Za mu hana shan Shisha a bainar Jama’a – Hukumar yawon bude ido

Published

on

Hukumar yawon bude ido ta jihar Kano ta ce, za ta hana shan Shisha a bainar Jama’a tare da hana kananan yara zuwa Otel da zarar gwamnati ta sanya wa dokar hannu.

Babban Manajan Daraktan hukumar, Yusuf Ibrahim Lajawa ne ya bayyana hakan,  a ganawar sa da gidan radiyon Dala a ranar Litinin.

Ya ce, “Tsofaffin wuraren da ake gudanar da Rini, dama wuraren da ake gudanar da Jima, na daya daga cikin ababen da mu ka sanya, a cikin  kasafin kudin hukumar a Bana”. A cewar Lajawa.

Wakilin mu Nasir Khalid Abubakar ya rawaito cewa, Yusuf Ibrahim Lajawa ya kuma ce, aikin hukumar ta su ya ta’allaka ne kadai wajen janyo ra’ayoyin al’umma, daga ko’ina domin zuwa jihar Kano domin yawon bude ido.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!