Connect with us

Manyan Labarai

Rashin tsari ya sanya gwamnati rusau a Farm Center- Tijjani Musa

Published

on

Shugaban Kasuwar waya ta Farm Center mai rikon kwarya a jihar Kano, Tijjani Musa Muhammad, ya ce, sun fuskanci matsala da gwamnati ne a sakamakon zama da suke a kasuwar ba bisa ka’ida ba.

Tijjani Musa, ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da Gidan Rediyon Dala, a yau Alhamis.

Yana mai cewa, “Dalilan da ya haifar da rikici a kasuwar shi ne, zama da suka yi ba akan tsari ba, kuma za su yi duk me yiwu wa, wajen ganin gwamnatin jihar Kano ta janye kudurinta na tashin mutane daga kasuwar domin canza musu waje.”  Inji Tijjani

Ya kara da cewa, “Suna bukatar gwamnan jihar Kano da ya taimaka domin barin su a wannan waje, su ci gaba da gudanar da kasuwanci, a kasuwar ta farm center kan doka da oda kuma cikin tsarin da ya kamata.”

Tijjani Musa ya kuma tabbatar da cewar, har yanzu babu mutane a wajen da aka tashi ‘yan kasuwar.

 

 

Manyan Labarai

Mun sami karamar hukumar birni a cikin mawuyacin hali:Hon Bashir Chilla

Published

on

Shugabancin ƙaramar hukumar Birni na riƙo dake nan jihar Kano ya ce bayan karɓa wannan ƙaramar hukumar sun same ta cikin muhuyacin hali, kasancewar yadda sakatariyar take babu gyara babu kuɗi.

Shugaban karamar hukumar na riƙo Hon Bashir Baba Chilla ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a wani ɓangare na samarwa da ƙaramar hukumar Birni ci gaba.

Chilla ya kara da cewa sun sanya idanu kan ma’aikatan da suke aiki a wajen domin zuwa aiki akan lokaci da kuma gudanar da aiki yadda aka tanada domin sauke hakkin al’umma.

Akwai matsalar huta da wannan sakatariyar take fuskanta ta yadda a kullum takan zama babu huta sakamakon rashin kula da injin da yake bayar da huta,amma kawo wannan lokacin an samu gyara shi, inda yanzu haka huta ta samu a cikin sakatariyar, A cewar Chilla.

Akwai matsalar ƴan kilisa da wannan ƙaramar hukumar take fuskanta, adon haka ya zama wajibi shugabancin ƙaramar hukumar ya dau mataki domin kawo ƙarshen wannan ɓarna da ake yi a yayin hawan kilisar.

Haka kuma muna so musamar da kyakkyawan tsaro a ƙaramar hukumar shiyasa yanzu haka muka kafa wani kwamiti wanda zan sanya idon ko ta kwana musamman a wannan lokaci na ƙaratowar sallah karama.

Muna kira ga iyaye da su sanya idanu kan ƴaƴan su domin kaucewa rikice rikice da ake samu na yau da kullum a wannan ƙaramar hukumar.

Zamu tabbatar mun sanya idanu kan asibitocin mu da suke ƙaramar hukumar Birni domin bayar da kulawar lafiya ga dukkanin al’ummar da suke yankin ƙaramar hukumar.

Akwai tsarin da ƙaramar hukumar Birni tayi wajen bayar da tallafin abinci ga al’ummar ƙaramar hukumar ƙarkashin jagorancin gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf domin rage matsin rayuwa da al’umma suke ciki.

Hon Bashir Baba Chilla ya ce a wannan lokaci Ramadan an sami matsalar ciyarwa a wata santa da take ƙarƙashin sa wanda hakan baiyi daɗi ba kuma cikin ƙanƙanin lokaci aka sami canji, domin gudanar da abin da gwamnati ta tsara.

Ina kira ga al’umma duk abin da zasuyi su kasance sunyi abin su tsakanin su da Allah domin hakki ne da aka ɗorawa mu ku.

Domin wannan tsarin na ciyarwa a buƙatar ya isa ga kowa da kowa musamman bamuƙata da suke faɗin jihar nan.

Continue Reading

Manyan Labarai

Yan baro a kasuwar sabon gari sun gudanar da zanga – zangar lumana a titin gidan gwamnati.

Published

on

Ƙungiyar ƴan baro dake kasuwar sabon gari a jihar kano, sun gudanar da zanga-zangar lumana akan titin gidan Gwamnatin jihar Kano, inda suke zargin shugabancin kasuwar da tilasta musu tashi daga guraren da suke gudanar da kasuwancin su a kasuwar, lamarin da hakan ke barazana da rayuwar su.

Shugaban ƙungiyar Tasi’u Ibrahim, ne ya jagoranci zanga-zangar lumanar a yau Laraba, inda suke kira ga mahukunta wajen duba halin da za su shiga idan har aka tilasta musu tashi daga kasuwar sabon garin a wannan lokaci, inda suka ce sun kwashe tsawon lokaci suna gudanar da kasuwancin su a nan amma sai gashi lokaci guda an hanasu.

Da yake nasa jawabin jim kaɗan bayan zanga-zangar lumanar shugaban kasuwar ta Sabon Gari Alhaji Abdul Bashir Hussain, ya ce ana yawan samun matsala da yawaitar korafe – korafe akan yan baron wanda hakan tasa shugabancin kasuwar ya zauna da masu ruwa da tsaki daga ciki harda jami’an tsaro domin shawo kan lamarin.

Abdul Bashir ya kara da cewa akwai wani tsari da shuagabancin kasuwar ya yiwa ƴan baron na sama musu makoma, wanda hakan zai kawo karancin samun cinkoso a cikin kasuwar ta sabon gari.

Continue Reading

Manyan Labarai

Manufarmu shine habbaka harkar noman kayan lambu:Horti Nigeria

Published

on

Kungiyar nan mai rajin habbaka noman kayan lambu ta Horti Nigeria ta horas da manoman kayan lambu da dilolin da ke sayar da kayan amfanin gona su 23 daga wasu kananan hukumomi dake sassan jihar kano.

Kananan hukumomi dai sun hadar da Kumbotso, Rimin Gado, Dawakin Kudu, Dawakin Tofa, Tofa, Garko, Bichi, da kuma Minjibir.

Horon dai ya biyo bayan kokawa da manoman kayan lambu keyi, na fama da kwarin da ke lalata musu amfanin gona.

Hakan tasa kungiyar ta Horti Nigeria ta fito da horon ga manoman da kuma dilolin da ke sayar da Iri da takin zamani da magungunan da ake amfani dasu a gona.

Haka zalika manoman an nuna musu hanyoyin da zasu ringa sayar da kayan amfanin gona idan sun kwashe daga gona a horon da suka amfana na kwana biyu.

“Munnir Abdulmiminu Yawale daga karamar hukumar Kumbotso wanda yana daya daga cikin dilolin da ke sayar da kayan magunguna na gona ya ce horon yazo akan gaba duba da tinkarar damuna da akeyi, hakan zai kawo karshen matsalar kwari da manoman kayan lambu ke fama dashi kuma sun amfana da abubuwa da dama a horon da suka samu na kwana biyu”.

Continue Reading

Trending