Connect with us

Manyan Labarai

Kano :Gobara ta tashi a gidaje daban-daban lokaci guda

Published

on

Wata gobara da ta kama a garin Tugugu dake karamar hukumar Bunkure a jihar Kano, ta yi sanadiyar kona gidaje guda hudu tare da tarin dukiya a ciki.

Gobarar dai wadda ta fara tashi da misalign karfe goma sha biyu na ranar Alhamis, ta kuma rinka yi wa gidajen dauki daidai da suke nesa da juna, har kusan karfe tara na daren ranar.

Wasu mazauna garin sun shaidawa Dala FM cewa ba a taba samun irin wannan annobar ta tashin gobara a yankin sai a wannan lokacin.

Yahaya Muhammad Rubben mazaunin garin ya ce” Har kawo yanzu ba mu san abun da ya haddasa gobarar ba, kuma ta lakume tarin dukiya mai yawa”. Yahaya.

Sagiru Ali ya na cikin wadanda suka taimaka a ka kasha gobarar ya ce” Mun sha wahala kafin mu kasha wutar, sakamakon muna nesa da cikin birni”.inji Aliyu.

Guda daga cikin magidancin da gobarar ta kama gidan sa, Muhammad Sani Danlami, ya ce” Gobarar ta kone ma na dakuna biyu, kuma tarin kayan mu ya na ciki tun daga kan kayan sawa da kayan abinci ba mu tsira da komai ba”. A cewar Muhammad.

Kan wannan batun ne muka tuntubi limamin masallacin Usman Bn Affan dake unguwar Kuntau a karamar hukumar Gwale a jihar Kano, Mallam Aminu Kidir Idris, ya ce”Wala Allah ko a na aikata sabo ne a yankin Allah ya jarrabe su”. Inji Kidir.

 

 

Labarai

Rahoto: Ma’aikatan jinya su kare kan su a kan Corona – Kungiyar ma’aikatan jinya

Published

on

Kungiyar ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta kasa reshen jihar Kano, ta bukaci ma’aikatan Jinya da Ungozoma da su ci gaba da kulawa da kan su yayin jinyar masu dauke da cutar Corona.


Shugaban kungiyar reshen jihar Kano, Kwamared Ibrahim Mai Karfi ne ya gargadi ma’aikatan yayin da kungiyar ta kai ziyara ma’aikatar lafiya ta jihar Kano a ranar Laraba.


Ya kuma ce, “Kamata ya yi idan al’umma sun ji yanayin su ya sauya, su yi kokarin tuntubar masana lafiya maimakon su je su sayi magani kai tsaye su sha”.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashi ya gurfana a kotu da zargin kisan kai

Published

on

Babbar kotun jiha mai lamba 3 karkashin mai shari’a Dije Abdu Aboki wani matashi ya gurfana akan zargin kisan kai.


Tun a ranar 24 ga watan Mayu na shekarar da ta gabata ne aka yi zargin matashin mai suna Muhammad Abdulmumin Dan Boy ya cakawa wani malamin makarantar Islamiyya wuka a kirji, sai dai a zaman kotun na baya matashin ya musanta zargin.


Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Za mu ci gaba da tallafawa marayu da marasa ƙarfi – Sarkin Kano

Published

on


Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce, masarautar Kano ta na nan kan ƙudirin ta na ci gaba da tallafawa marayu da marasa ƙarfi.


Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar tallafawa marayu da mabuƙata ta Green Pasture and Home Innitiative.


Sarkin wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin lafiya na masarautar Kano, kuma Ɗan Kaden Kano Dr. Bashir Ibrahim Muhammad Ɗan Kade ya ce, dama haƙƙin masarautar ne kula da mabuƙata.Mista Ayo da Madam Comfort O-William na cikin jami’an ƙungiyar sun yi ƙarin haske kan dalilin kai ziyarar ta su ga mai martaba sarkin.

BS

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!