Labarai
Zubda jini masufa ce a cikin al’umma –Malam Ibrahim Tofa

Limamin masallacin juma’a na Masjudul Quba dake unguwar Tukuntawa a karamar hukumar Birnin Kano, Malam Ibrahim Abubakar Tofa, a hudubar sa ta yau ya bayyana irin mummunar illar da yawan kashe-kashen da a ke samu, ba karamar musifa ba ce a tsakankanin al’umma.
Malam Ibrahim Abubakar Tofa, a hudubar sa ta juma’a, ya ce” kashe ran mumini ba tare da hakkin shari’a ba, ya na daga cikin manyan-manyan laifuka wadanda suke jefa mutum cikin wutar jahannama tare da dauwama a cikinta, mafita ita ce al’umma su koma ga Allah ta hanyra kauracewa sabo da kuma yawaita tuba a wurin ubangiji, saboda kaji yau an fito cikin al’umma an harbe mutum ko an sa bam ko anyi garkuwa da kai an kuma kasha ka”. Inji Malam Ibrahim Tofa.
daga bisani limamin na masallacin juma’a na Masjudul Quba dake unguwar Tukuntawa, Malam Ibrahim Abubakar Tofa, ya kuma gargadi iyaye da su kara maida hankali wajen kulawa da tarbiyyar ‘ya’yan su ta hanayr basu ingantaccen ilimin addini dana zamani, tare da gargadin su wajen yin biyayya ga iyayen nasu.

Labarai
Cutar mashako ta bulla a wasu sassan Jigawa

Akalla mutum goma ne suka mutu bayan ɓarkewar cutar mashaƙo a kananan hukumomi 14 na jihar Jigawa.
Ma’aikatar Lafiyar jihar ce ta sanar wa manema labarai haka a Dutse, a yau Lahadi. Ta ce ana kuma zargin cewa mutum 91 sun kamu da cutar.
Babban sakatare a ma’aikatar, Dr Salisu, Mu’azu, ya ce zuwa yanzu, an tabbatar da mutum biyu da suka kamu da cutar a kananan hukumomin Kazaure da Jahun yayin da aka Ɗauki jinin wasu zuwa Abuja domin yin gwaji da tantancewa.
Mu’azu ya ce ɓarkewar cutar abin damuwa ne musamman ma ganin cewa ta ɓulla a yankunan da ba su taɓa yin riga-kafin ta ba.
A cewarsa, tuni ma’aikatar ta fara bincike domin tattaro bayanai daga yankunan da abin ya shafa.
Ya ce gwamnatin jihar tuni ta fara shiri don yin riga-kafi a yankunan domin kaucewa yaɗuwar cutar.

Hangen Dala
Hukuncin kotu:- Zamu daukaka Kara – Abba Gida Gida

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yace zasu ɗauki matakin ɗaukaka ƙara zuwa gaba domin tabbatar da adalci kan hukuncin da kotun sauraron korafe-korafen zabe ta yanke inda ta ayyana Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan da aka gabatar a watan Maris din 2023.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana a fadar gwamnatin Kano a daren laraba.
Gwamnan ya ƙara da cewa sun umarci lauyoyin su da su hanzarta wajen ɗaukaka ƙara ba tare da ɓata lokaci ba.
Ka zalika ya kuma ce wannan hukuncin bazai sanyar musu da gwiwa ba wajen ci gaba da gudanar da ayyukan da suka fara.
A ranar Laraba ne dai 20 ga watan Satumba 2023 kotun sauraron korafe-korafen zabe ta tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin Wanda ya lashe zaben Gwamnan Kano da aka gabatar a watan Maris. (more…)

Hangen Dala
Hukuncin zaben Kano:- An Kori ‘yan Jarida daga harabar kotu

Jami’an Ƴan Sanda sun hana ƴan Jarida shiga harabar Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe ta Kano.
Duk da asubanci da ƴan jarida suka yi, jami’an ƴan sanda sun yi ƙememe sun hana su shiga.
Ƴan sandan sun koro wakilan kafafen yaɗa labarai da dama zuwa can nesa da Kotun.
A yau ne dai za’a Yanke hukunci Kan karar da jam’iyyar APC ta shigar gaban kotun tana kalubalantar nasarar Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Ƙarin bayani na tafe.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano