Connect with us

Manyan Labarai

Zabe: An jefa kuri’a a kan budurwa domin zabar miji

Published

on

Wasu samari biyu sun jefa kuri’ar zabe kato bayan kato, bayan tsawon kwanaki uku ana yin kamfen, akan son wata bakar budurwa, ‘yar Bauchi dake garin Giyade, Hajara Muhammad.

Samarin, Yunusa Muhammad da Ibrahim Adamu, sun kamu ne da kaunar budurwar, wadda itama ta kamu da kaunar tasu, ta kuma umarce su da suje su kada kuri’ar zabe.

Bayan da aka sanar da Dattawan garin, sai aka kuma bude kofar kamfen tsawon kwanaki uku, wanda aka yi zaben karkashin kulawar jami’an tsaron garin, inda itama budurwar ta kai ziyarar gani da ido filin zaben.

Bayan kammala zaben, Yunusa Muhammad, shi ne ya yi nasara, an kuma ba shi tikiti, sakamakon lashe zaben da ya yi, sai dai amma shi wanda bai samu nasara ba, Ibrahim Adamu ya ce, “Bai yarda da zaben ba, tun da dai dama a kofar gidan abokin karawar ta wa a ka yi zaben, domin haka ya zama Inconclusive.”  Inji Ibrahim.

Sai dai bamu samu zantawa da ango mai nasara Yunusa Muhammad ba, amma Aminsa Tajuddin Umar ya bayyana cewa, “Wanda ya fadin, ya rage nasa mu dai mun riga mun yi nasara, har ma mun fara shirye-shiryen fati.”  A cewar aminin ango

Shima Sakataren zaben, Ibrahim Taldo Giyade, ya ce, “Tsakani da Allah mu kai zaben mu, domin dai har da jami’an tsaro ma a wajen, amma dai wanda ya fadin, mun ba shi wa’adin mako guda ya daukaka kara wurin mahukunta.”

Itama amaryar Hajara Muhammad, ta ce, “Koda dai nima ya sanar da ni bai gamsuba, amma dai a wurina zaben ya kammala, saura kuma sai abun da hukumar zaben ta aiwatar.”

Malam Aminu Kidir limamin masallacin Usman Bin Affan dake Kuntau karamar hukumar Gwale, ya yi bayanin matsayin irin wannan aure da  samarin suka yi zasu zaben kuri’a a mahangar addinin musulinci da cewa, “Musulunci ya haramta nema cikin nema, domin haka ba ya halatta wani na neman aure wani kuma ya shigo, sai in wancan ya yi ikirarin ya janye, kuma wannan zaben da suka yi a kan budurwa babu aibu a kansa ko auren a ka yi ya yi, abun da a ke bukata kenan, yayin da samari suka hadu a kan budurwa to su yi kuri’a domin a fitar da mutum daya kwakkwara.” Inji Malam Kidir

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Manyan Labarai

Da Ɗumi-Ɗumi! Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers da mataimakin sa da ƴan majalisar jihar na watanni 6.

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, da mataimakiyar sa Mrs. Ngozi Odu, har na tsawon watanni 6.

Shugaba Tinubu ya bayyana daukar matakin ne a cikin wani taƙaitaccen jawabin sa da ya gabatar a cikin daren Talatar nan, ya ce ya yi amfani da damar da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen sanya wannan doka wacce ta kwace mulkin jihar daga hannun gwamnan jihar Siminalayi Fubara da mataimakin sa har sai lamura sun dawo dai-dai a jihar.

Kazalika, shugaba Tinubu ya kuma bayyana dakatar da dukkanin ƴan majalisar dokokin jihar suma na tsawon watanni shidan, tare da sanya dokar ta ɓaci a jihar.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan rikicin siyasar da ya daɗe da kunno kai a tsakanin gwamna Fubara da ministan birnin tarayya Abuja Nyesome Wike, al’amarin da ya janyo takun saƙa tsakanin sa da ƴan majalisar dokokin jihar.

Continue Reading

Manyan Labarai

Isra’ila ta kashe sama da mutane 200 bayan karya yarjejeniyar tsagaita Wuta a Gaza

Published

on

Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, tare da ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Falasdinawa.

Jaridar TRT Hausa ta ruwaito cewa, aƙalla Isra’ila ta kashe fiye da mutum 200 tare da jikkata ɗaruruwa a yayin da ake ci gaba da kai gawawwaki asibiti, kamar yadda majiyoyin wani asibiti a yankin Gaza suka bayyana.

Continue Reading

Trending