Connect with us

Manyan Labarai

KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai

Published

on

Wani Lauya mai zaman kansa Barista Rabi’u Sa’id Rijiyar Lemo ya baiwa shugaban hukumar Karota wa’adin kwanaki bakwai da ya janye umarnin da ya baiwa ‘yan kasuwar Waya ta Farm Center cewar su ta shi su koma Dangoro nan da kwanaki casa’in.

Barista Rab’iu Rjiyar Lemo, ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da gidan rediyon a juma’ar nan, ya na mai cewa” Hukumar Karota ba ta da hurumi na tashin ‘yan kasuwar, gwamna ne kawai ko hukumar kasa da kuma hukumar tsara burane suke da ikon yin hakan, matukar bai janye ba zamu kara yin karar sa a kotu nan da kwanaki bakwai”. Inji Barista Sa’id.

A baya dai ya shigar da shugaban hukumar ta Karota Baffa Babba Dan Agundi da gwamnan Kano da kuma Kwamishinan shari’a a gaban kotu dangane da nada Baffan cewa ba bias ka’ida a ka nada Baffan, inda goma ga watan gobe za a ci gaba da sauraron karar.

Labarai

Hisba ta kama wani malamin bogi dake tara mata a gidansa

Published

on

Wani mutum da aka yi zargin ya kira kansa da Malami kuma Shehi, an yi zargin ya rabo wasu tarin mata daga kauyukansu suka tare a gidansa dake Yankin Gwale.

Mutumin dai ya tara matan ne da zummar zasu rinka daukar darasi a gidan nasa, karshe akai zargin yana basu wani irin darasi na musamman, don haka alummar yankin suka kai korafi hukumar Hisaba.

Bayan kuma Hisbar sun kai sumame gidan sai gashi sun samu tarin matan a gidan, wasu har da kullin kayayyakinsu sun yo hijira daga kauyukansu daban-daban sun tare a gidan.

Mutumin dai ya ce, wai shi Alaramma ne kuma Shehi, koda dai hukumar Hisbar ta bakin matamakin babban kwamanda kan ayyuka na musamman Malam Albukari Mika’il ya ce, “Wannan fa ko malami bai kai ba ballema har ace masa Shehi, ya dai fi kama da magaji abokin magajiya”. A cewar Albukari

Continue Reading

Labarai

Wani mai ikirarin shugaban masu sayar da abinci ya shiga hannu

Published

on

Ana zargin wani mutum yayi gaban kansa, ya fitar da sanarwa cewar, an rufe gidajen siyar da abinci baki daya a jihar Kano saboda cutar Coronavirus.

Mutumin yayi ikirarin cewar, shi ne shugaban kungiyar masu siyar da abincin a jihar Kano, kuma kwamishina ‘yan sanda jihar Kano yana da masaniya akan sanarwar tasa.

Sai dai daga bisani mutumin ya shiga hannu kuma mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya yi karin haske akan al’amarin inda ya ce, kokadan kwamishin ‘yan sandan jihar Kano bai san da mutumin ba bare kuma sanarwar tasa, abinda ya aikata yayi ne a radin kansa .

Yusuf Ibrahim Lajawa shi ne shugaban hukumar harkokin yawon shakatawa da bude idanu ta jihar Kano, ya magantu, yana  mai cewa, mutumin ba shi ne shugaban kungiyar masu sayar da abinci a jihar Kano ba, kuma gwamnatin jihar bata bada sanarwar rufe gidajen abinci ba..

 

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Malaman islamiyya sun koka kan rufe makarantu

Published

on

Malaman makarantun islamiyya sun yi korafin ana nuna masu banbanci tsakaninsu da sauran malaman makarantu na gwamnati.

Shugaban kungiyar hadakan malaman makarantun isalamiyya da tsangayu a jihar Kano, Malam Kamalu Sa’idu Habibu ne ya bayyana haka a zantawarsu da gidan rediyon Dala.

Ya ce, “Tun bayan da aka dakatar da gudanar da makarantu mu ka shiga haliin tasku, kasancewar mun dogara ne da kudaden wata da na Laraba da muke karba daga iyayen yara, yanzu kuma tunda ba makarantun, to babu kudaden watan da Larabar”. Inji Malam Kamalu.

Kazalika, suma wasu daga cikin malaman makarantun islamiyar sun ce yanzu ta kai ga sun fara shiga wani mawuyacin hali, saboda rufe makarantun nasu.

Shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Right Foundation of Nigeria, Alhaji Muhammad Bello Gadon Kaya ya ce, “Idan dan talaka ya sauke hakkinsa na yin biyayya ga dokar gwamnati, to shima fa yana da nasa hakkin a wajen gwamnati, kuma kwamitin nan na tattara tallafi wanda gwamnatin jiha ta kafa, to idan an tara tallafin kamata yayi a mayar da hankali wajen talakwa musamman ma wadanda suka shiga cikin rudani, sakamakon kullen na korona”. A cewar Alhaji Muhammadu

Babban kwamanda hukumar Hisba Sheikh Harun Ibn Sina daya ne daga cikin ‘yan kwamatin tattara tallafin, ya bayyana cewar, “Zamu mayar da hankali wajen talakawan, tunda dai al’umma sun amsa kiran, alat din shigar kudi kawai suke jira su ji ta kowacce fuska”. Inji Ibn Sina.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish