Connect with us

Manyan Labarai

KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai

Published

on

Wani Lauya mai zaman kansa Barista Rabi’u Sa’id Rijiyar Lemo ya baiwa shugaban hukumar Karota wa’adin kwanaki bakwai da ya janye umarnin da ya baiwa ‘yan kasuwar Waya ta Farm Center cewar su ta shi su koma Dangoro nan da kwanaki casa’in.

Barista Rab’iu Rjiyar Lemo, ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da gidan rediyon a juma’ar nan, ya na mai cewa” Hukumar Karota ba ta da hurumi na tashin ‘yan kasuwar, gwamna ne kawai ko hukumar kasa da kuma hukumar tsara burane suke da ikon yin hakan, matukar bai janye ba zamu kara yin karar sa a kotu nan da kwanaki bakwai”. Inji Barista Sa’id.

A baya dai ya shigar da shugaban hukumar ta Karota Baffa Babba Dan Agundi da gwamnan Kano da kuma Kwamishinan shari’a a gaban kotu dangane da nada Baffan cewa ba bias ka’ida a ka nada Baffan, inda goma ga watan gobe za a ci gaba da sauraron karar.

Manyan Labarai

Gididdiba burtalan garuruwan mu da akayi ka iya haifar mana da barazana – Fulani mazauna ƙaramar hukumar Tofa

Published

on

Fulani Makiyaya na garuruwan Yanoko, da Gajida, da kuma garin Dindere da ke ƙaramar hukumar Tofa, sun koka tare da neman ɗaukin mahukunta, bisa yadda suka ce sun wayi gari da ganin wasu mutane tare da yanka burtalan garuruwan su,

Fulanin sun ce zargi ya nuna yadda aka godiddiba burtalan inda aka siyarwa da wasu shafaffu da mai, lamarin da suka ce hakan babbar barazana ce a gare su, kasancewar babu wajen da za suyi kiwon shanun su.

A zantawar Dala FM Kano, da shugaban ƙungiyar Fulani Makiyaya reshen ƙaramar hukumar Tofa, ta Gan Allah, Mallam Ahmad Shehu, ya ce gididdiba burtalan ka iya haifar musu da gagarumar matsala a rayuwa, a dan haka ne ma suke kira ga gwamnatin Kano da ta kawo musu ɗauki.

Alhaji Mamuda mazaunin Dawakin Tofa, na ɗaya daga cikin waɗanda aka yankarwa burtalin a yankin Dindere, aka kuma siyar masa, ya ce wasu ne suka siyar masa kuma an bashi takarda hakan ya sa har ya fara aiki a wajen

Wakilin dagacin garin Dindere Isah Sulaiman ya ce, lamarin yaje ga ofishin hakimin Tofa, a dan haka ne muka zanta da Turakin Tofa, Alhaji Sunusi Abubakar Tofa, kuma wakilin Makaman Bichi hakimin Tofa Alhaji Dakta Isyaku Umar Tofa, ya ce sun san da al’amarin ana ci gaba da ɗaukar mataki, kuma masarautar yankin bata bai wa kowa damar yankar burtalin ba, ko da kuwa mai unguwar Yalwal Rimi da ke garin Dindere da akace shima ya yanki burtalin.

Al’amarin gididdiba burtalin dai wasu sun danganta shi da shugabancin ƙaramar hukumar Tofa mai ci a yanzu, a dan haka ne muka yi duk mai yiyuwa wajen ji daga shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Abubakar Sulaiman Mai Goro, sai dai bai samu damar ɗaga wayar mu ba, kuma mun aike masa da saƙon karta kwana sai dai har wannan lokaci ba muji daga gareshi ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Bama goyon bayan ƙirƙiro ƴan sandan jahohi dan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasa – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce akwai buƙatar duba na tsanaki gabanin sahale ƙirƙirar ƴan sandan jahohi, domin gujewa abinda ka je ya dawo.

Daraktan ƙungiyar a nan Kano Kwamared Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, a yau Talata.

Galadanci, ya kuma ce duba da a mafi yawan lokuta ake samun baragurbi a harkar samar da taro, kamata ya yi a wadata jami’an tsaron da ake da su da kayan aiki na zamani, ta yadda za’a ƙara musu Gwiwa akan aikin su.

“A ɓangaren ƙungiyar mu bama goyon bayan samar da ƴan sandan jahohi, domin hakan ka iya haifar da koma baya; kuma ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a sassan ƙasar nan, “in ji shi”.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Umar Sani Galadanci, ya ƙara da cewa akwai buƙatar gwamnatin tarayya da ta jahohi, su kula da al’ummar su tare da samar musu kayayyakin more rayuwa, dan rayuwar su ta tafi yadda ya kamata.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mutane uku sun rasu yayin ciro Waya a cikin Masai da ceto mutum ɗaya a Kano – Hukumar Kashe Gobara 

Published

on

Hukumar kashe Gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu mutane uku, ciki har da Uba ɗan sa, a unguwar Ƴar Gwanda da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobarar PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya bayyanawa gidan rediyon Dala FM, faruwar lamarin a daren jiya Lahadi.

Tunda fari dai mutum na farko mai suna Mallam Ɗan Juma mai laƙabin Black, wayar sa ce ta faɗa a cikin Masai, ya shiga domin ya cirota, sai dai gaza fitowar sa ke da wuya sauran mutane ukun suka bishi domin ceto shi lamarin da suma suka gaza fitowa.

Sauran mutane ukun akwai ɗan mutumin mai suna Ibrahim Ɗan Juma mai shekaru 35, sai na ukun mai suna Aminu T Gaye, da na huɗu mai suna Abbas Alhassan, ɗan shekara 28, amma shi an ciroshi a raye.

PSF Saminu Yusuf, ya kuma ce bayan faruwar lamarin ne jami’an su, suka ceto mutum na ƙarshe a raye, amma ukun farko basa cikin hayyacin su baki daya.

Ya ƙara da cewa tuni jami’an nasu suka miƙa mutanen a hannun jami’in hukumar ƴan Sanda, kuma babban baturen ƴan sanda da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano mai suna SP Ibrahim Lado, inda suka kai su asibitin ƙwararru na ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano.

Continue Reading

Trending