Connect with us

Nishadi

Anyi shagalin bikin jaruma Maryam Ceeter

Published

on

A ranar jumu’ar da ta gabata ne aka daura auren fitacciyar Jarumar fina-finan Hausar nan Maryam Isah Ceeter, a masallacin jumu’a na Alfurkan dake nan Kano.

Jaruma Maryam Ceeter ta wallafa hotunan bikin a shafin ta na Facebook inda masoyanta suka rika yi mata sakon fatan alkhairi.


Nishadi

Na yi asarar dala biliyan 2 a rana ɗaya kuma har yanzu ina raye – Mawakin Amurka

Published

on

Ba’amurke kuma mawaki, Kanye Omari West, wanda aka fi sani da Kanye West ko Ye, ya yi asarar dala biliyan 2 a cikin sa’o’i 24, bayan wasu kamfanoni da dama sun yanke alaka da shi saboda kalaman kyamar Yahudawa.

Wannan na zuwa ne kasa da sa’o’i 48, bayan wata mujallar kasuwanci ta Amurka, Forbes, ta sanar da cewa Kanye ba shi da wani matsayi a cikin jerin masu kudi a yanzu bayan da yarjejeniyarsa mai tsoka da Adidas ta yanke hulda da shi.

Kamfanonin da suka yanke alaƙa da Kanye ya zuwa yanzu sun haɗa da Balenciaga, MRC (dakin nishaɗin da aka riga aka gama Ye Documentary), hukumar baiwar sa CAA, Adidas, Jaylen Brown da Aaron Donald, Foot Locker, The RealReal, T.J. Maxx, Madame Tussauds.

Da yake mayar da martani kan asarar, mawakin, a wani sako da ya wallafa a shafin Instagram, ya bayyana cewa mutanen shi ne, ba kudin ba.

Ya rubuta, “Na yi asarar dala biliyan 2 a rana ɗaya, kuma har yanzu ina raye. Wannan maganar soyayya ce, har yanzu ina son ku; kudin ba ni ba ne, jama’a su ne ni.”

Har ila yau, makarantarsa, Donda Academy, abun ya shafa ta, yayin da aka fitar da su daga gasar makarantar sakandare saboda maganganun Kanye.

Continue Reading

Ƙasashen Ƙetare

Magen gidan Firaministar Birtaniya na dakon uwar dakin ta

Published

on

A yau ne iyalan tsohon firaministan Burtaniya Boris Johnson ke tattara komatsansu a shirye-shiryen da suke yi na bankwana da gidan firaministan wanda ke Downing Street, domin bayar da waje ga sabuwar firaministar Mrs Liz Truss tare da iyalanta, wacce za ta ci gaba da zama a gidan na tsawon mulkinta,

To sai dai yayin da ake wannan shiri na ficewa daga gidan Kyanwar gidan mai suna ‘Lary’ na nan daram a gidan tana jiran isowar sabuwar firaministar

A rahoton BBC sun ce, Lary wacce ba mallakin kowa ba ce, ta zama babbar Kyanwar gidan firaminstan Birtaniya.

Kyanwar mai shekara 15, wacce ta yi zamani da firaministocin Burtaniya har guda uku, na shirin zama da iyalan Mrs Truss.

Continue Reading

Labarai

Na saka takalmi Sneakers da shirin ko ta kwana – Kashim Shettima

Published

on

Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima, ya mayar da martani kan sukar sa da aka yi masa a lokacin da ya halarci taron kungiyar lauyoyin ta kasa NBA a jihar Legas.

Hotunan Shettima dai sun yi ta yawo a dukkanin kafafen sada zumunta na zamani, wanda aka caccake shi a kan takalmin da ya saka da rigar Kwat.

Sai dai Shettima, a cikin wani faifan bidiyo da yake zagayawa a halin yanzu, ya bayyana cewa da gangan ya sanya takalmin sneakers a wajen taron wanda ya gudana a ranar Litinin.

Ya ce ya sanya sneakers ne a wajen taron, saboda akwai wani shiri da dan takarar shugaban kasa da magoya bayansa suka yi nayin barna a wurin taron.

A cewar Shettima, “Daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa, tawagarsa sun gudanar da tarurruka na tsawon kwanaki uku a jere, wanda hakan za su iya tayar da rikici a wajen, lokacin da aka ce min jama’a ne masu adawa. Ni ma’aikacin banki ne, wanda ɗayan manyan ma’aikatan banki ne a duniya ya horar da ni. Ni ɗan Jim Ovia ne. Da gangan na sanya sneakers zuwa taron NBA don yin izgili a kansu. “

Continue Reading

Trending