Manyan Labarai
Matar da ta gudu a hannun Gandiroba ta shiga hannu.

Wata mata mai suna Poul Messay, daga cikin wadanda ake zargi da satar yara a yankin unguwar Hotoro zuwa jihar Anambara ta arce daga hannun Gandiroba da ankwar da take hannunta, lokacin da ta zagaya bandaki bayan an kai ta asibitin Kwararru na Murtala.
Matar an kai ta gidan ajiya da gyaran hali dake Kurmawa, saboda laifin da ake tuhumarta da shi, na satar yara, kuma ta na cikin gidan ne sai jini ya balle mata matsalar kuma ta fi karfin asibitin dake cikin gidan daurarrun, domin haka aka kai ta asibitin Murtala cikin dare domin a sama mata lafiya, aka kuma hada ta da wata Gandiroba, inda a can din ne ta bukaci a bata dama ta je bandaki.
Bayan kuma taje bandakin ne da ankwar a hannu, sai ta yiwa Gandirobar kwanta-kwanta ta arce, tun a ‘yan kwanakin baya kadan na farkon shekarar nan, saboda haka jami’an gidan ajiya da gyaran halin suka shiga farautar ta.
A wannan karon kuma su ka samu nasarar kamota a unguwar Panshekara, inda aka yi zargin acan din ne ta boye, ta na waya da irin mutanenta masu kawo ma ta ziyara, sai suka hada kai da sauran jami’an tsaro na musamman DSS, su ka yi Tracking din lambar wayar wani da suka yi waya da ita da karshe suka kama shi, shi kuma ya kai su inda take a acan Panshekarar, su ka kama ta shi kuma suka sallame shi, a cewar, Kwantirolan hukumar a jihar Kano Magaji Ahmad Abubakar.
Wakilinmu Abubakar Sabo ya rawaito cewar, tuni jami’an gidan ajiya da gyran halin su ka sake garkame ta, tare da sake tuhumarta da sabon laifin arcewa daga hannun, a hannu guda kuma dokar tasu ta ce, duk Gandiroban da daurarre ya gudu a hannusa za’a buncika, in har akawai sakaci, to akwai yuwuwar rasa aikinsa.

Manyan Labarai
Gawuna ya taya Abba Gida Gida murna

Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023 Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana karbar kaddara tun bayan da ya Fadi zaben 18 ga watan Maris.
Cikin Wani Sakon murya, Dakta Nasiru Gawuna ya godewa magoya baya, tare da yin fatan alkhairi ga sabuwar gwamnati.
” Wannan sabuwar gwamnati Allah ya Bata ikon yiwa al’umma adalchi, mu Kuma Allah ya bamu ikon yin biyayya.”

Manyan Labarai
Abba Gida Gida ya karbi shaidar lashe zabe

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida gida ya karbi shaidar lashe zaben Gwamnan Kano.
Ya karbi wannan shaida ce yayin wani taro da hukumar INEC ta shirya domin bashi shaidar satifiket, bayan nasarar da ya samu a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.
Taron dai Wanda ya samu halartar da dama daga cikin manyan jihar Kano dama shiyyar arewa maso yamma, ya gudana ne a dakin taro na ofishin hukumar zabe INEC na jihar Kano.

Labarai
Marayu na buƙatar tallafi sosai – Kwamared Abu Saleem

Shugaban ƙungiyar tallafawa Marayu da ci gaban al’umma ta ƙaramar hukumar Birnin Kano Kwamared Adam Umar Abu Saleem, ya ce ƙarancin samun tallafi daga masu ƙarfi ne ke sanyawa Marayu ke faɗawa cikin mawuyacin hali.
Kwamared Adam Abu Saleem na wannan jawabin ne yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM, lokacin musabaƙar Alƙur’ani mai girma na marayu ƴan ƙaramar hukumar Birni 5 yayin da ɗalibi dake Karkasara Ja’afar Aliyu Abubakar ya zama gwarzon shekara na ƙaramar hukumar wanda aka ɗauki nauyin al’amuran rayuwarsa baya ga kyaututtuka da ya samu, wanda Musabaƙar ta gudana cikin Firamen Salanta a ranar Asabar.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Adam ya ce sukan shirya Musaɓakar ne domin zaburar da Marayu akan harkokin karatun Alkur’ani mai girma, da kuma rage musu wani tunanin maraici da suke kasancewa a maban-banta lokuta.

-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya10 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano