Connect with us

Labarai

Gobara ta kona shaguna a kasuwar Singa

Published

on

Wata gobara ta kama a Kasuwar Singa dake jihar Kano, bayan da a ke zargin wata wutar lantarki ta haddasa a yau Alhamis.

Wani mazaunin kasuwar, ya ce”Misalin karfe 3 da wasu mintina na dare a ka kawo wutar lantarki sai wayar wutar ta yi bindiga sai wutar ta shi, kuma shi ne musabbabin tashin wutar, kuma kimanin shaguna 15 ne suka kone kawo yanzu. Mun kuma sanarwa da hukumar kasha gobara ta jihar Kano, ta zo wurin da gaggawa ta kuma kasha wutar, kuma a yanzu haka ta yi asarar tarin dukiy”. Inji wani dan kasuwar da ya ganewa idanun sa.

Haruna Hassan cewa ya yi” Musabbabin tashin wutar a kan idanun sa wutar lantarki ce ta yi bindiga, kuma wannan wutar lantarki ta kona shaguna da dama”. Inji Hassan.

Jamin hulda da jama’a na hukumar kasha gobara ta jihar Kano, PFO Sa’idu Muhammad Ibrahim, y ace” Mun sami kira daga kasuwar Singa mai suna Mubarak Umar da karfe hudu, kuma mun je mun tarar da wuta na ci mun samu nasarar kasha ta, zuwa yanzu dai shago biyu ne suka kone sai kuma shagunan wucan gadi goma 11 sun kone, kuma yanzu muna binciken adadin asarar da a ka yi a kasuwar kuma babu wata asarar rai da a ka samu a ciki”. Inji Sa’idu Muhammad.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending