Labarai
‘Yan sanda sun horas da matasa a kan labaran karya

Rundunar ‘yan sanda jihar Kano da hadin gwiwar gidauniyar inganta ayyukan jami’an tsaro NPP sun gabatar da wani taron yini guda don bayar da horo ga matasa ‘yan jihar Kano masu fada aji a kafafan sada zumunta.
Taron wanda aka gabatar ajiya Laraba a birnin Kano, ya samu halartar masu amfani da kafafan sada zumunta daga bangarorin siyasa daban-daban da bangarorin addini na jihar Kano da sauran matasa masu amfani da shafukan.
Daga cikin wadanda suka gabatar da takarda a yayin taron sun hadar da Malam Ali Isah, wanda yayi bayani kan kafafan sada zumunta.
Sai kuma Basheer Sharfadi na nan Dala Fm wanda ya gabatar da takarda kan labaran karya da kalaman batanci a kafafan sada zumunta da hanyoyin magance su.
Daga bangaren jami’an Rundunar ‘yan sanda kuwa ASP, Yusuf Isah ya gabatar da makala kan gudummuwar da ake tsammanin ‘yan social media zasu gudanar ta jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya.
Sai ASP. Adamu M. Muhammad da ya gabatar da takardar sa akan irin abubuwan da ka iya zamowa laifi a kafafan na sada zumunta.

Labarai
Mu yawaita karanta Alƙur’ani da aikin alkhairi a watan Ramadan – Malam Ibrahim Bunkure

Limamin masallaacin Juma’a na Salafussalih dake unguwar Ɗorayi ƙarama Malam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’ummar musulmi da su ƙara himma wajen karanta Al-ƙur’ani mai girma, tare da aikata ayyukan alkhairi domin rabauta da rahamar Allah S.W.T a nan duniya dama gobe ƙiyama.
Mallam Ibrahim Bunkure ya bayyana hakan ne lokacin da yake tsokaci kan huɗubar Juma’ar da ya gabatar yau a masallacin.
Ya ce, kamata yayi musulmai su ƙara yin koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, domin zama ababen koyi a rayuwa.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya kuma shawarci al’umma da su ƙara kasancewa masu yafiya musamman a lokacin da aka yi mutu abinda bai musu daɗi ba, bisa mahimmancin da hakan yake da shi.

Labarai
Marayu na buƙatar tallafi sosai – Kwamared Abu Saleem

Shugaban ƙungiyar tallafawa Marayu da ci gaban al’umma ta ƙaramar hukumar Birnin Kano Kwamared Adam Umar Abu Saleem, ya ce ƙarancin samun tallafi daga masu ƙarfi ne ke sanyawa Marayu ke faɗawa cikin mawuyacin hali.
Kwamared Adam Abu Saleem na wannan jawabin ne yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM, lokacin musabaƙar Alƙur’ani mai girma na marayu ƴan ƙaramar hukumar Birni 5 yayin da ɗalibi dake Karkasara Ja’afar Aliyu Abubakar ya zama gwarzon shekara na ƙaramar hukumar wanda aka ɗauki nauyin al’amuran rayuwarsa baya ga kyaututtuka da ya samu, wanda Musabaƙar ta gudana cikin Firamen Salanta a ranar Asabar.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Adam ya ce sukan shirya Musaɓakar ne domin zaburar da Marayu akan harkokin karatun Alkur’ani mai girma, da kuma rage musu wani tunanin maraici da suke kasancewa a maban-banta lokuta.

Labarai
Lokacin zaɓe: Rundunar ƴan sanda ta shirya daƙile tayar da tarzoma – SP Kiyawa

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, ta shirya wajen samar da tsaro, tare da ɗaukar matakin da ya dace ga ɓata garin da suke shirin tayar da tarzoma.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u a yau juma’a, yayin da yake tsokaci kan shirin da rundunar su ta yi kan zaɓe.

-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya10 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano