Connect with us

Labarai

Za a fara daukar mataki a kan masu yada tsiraici

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Usman Bin Affan dake Unguwar Kuntau Mallam Aminu Kidir Idris, ya yi kira ga al’ummar musulmai da su guji yada barna a doron kasa domin gudun fishin Allah (S.W.T)’

Mallam Aminu kidir, ya yi wannan kiran ne jim kadan bayan fitowa daga cikin shirin Shari’a a aikace na nan Gidan Rediyon Dala da safiyar yau Alhamis.

Yana mai cewa,”fitar da barna ga al’umma a gari ka iya janyo fishin Ubangiji S.W.T, domin haka akwai bukatar jama’a su kiyaye yin hakan, zai fi kyautatuwa mutane su rinka addua mai makon yadawa”.

Da yake nasa tsokacin a kan wani fai-fan bidiyo da a ka wallafa na yar wasan hausar nan Maryam Booth, a kafafen sada zumunta, shugaban gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam ta Humman Right Network Kwamred A-A Haruna Agayi, ya ce”Tun bayan da fai-fan bidiyon ya bulla mu ke kokari wajen ganin an nemawa mai hakki hakkin sa”. Inji AA Ayagi.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Kwamred A-A Haruna Ayagi, ya kuma ja hankalin wadanda suke yada bidiyo dama hotunan mutane da su dai na, domin kuwa duk wanda ya shiga hannun su sukan dauki matakin kai shi wajen jami’an tsaro domin daukan matakin da ya dace a kansa.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending