Connect with us

Labarai

Ma’aikatar muhalli za ta kulla kawance da kasuwannin Kano

Published

on

A yunkurin da ta ke yi na tsaftace muhalli da share magudanan ruwa, ma’aikatar muhalli ta jihar Kano, ta ce za ta hada karfi da shugabancin kasuwanni domin ganin ta tsaftace birnin Kano da kewaye.

Kwamishinan muhalli na jihar, Dakta Kabiru Getso ne ya bayyana hakan ya yin wata ganawa da shugabannin kasuwannin Kantin Kwari, Yan Lemo da kuma Rimi da suka kai masa ziyara a ofishin sa.

Dakta Kabiru Getso wanda babban sakataren hukumar, Hussam Musa Karry, ya wakilta ya ce” Makasudin ganawar hukumar da ‘yan kasuwa baya rasa nasaba da tattara shawarwarin hanyoyi da za a bi wajen tsaftace jihar Kano daga kazanta. Ganin cewar al’ummar Kano yan kasuwa ne, sun fi shafe tsawon lokutan su a kasuwanni, wannan ta sanya hukumar ke nazarin bijiro da hanyoyin tsaftace harkokin kasuwanci ta hanyar rage yawan datti a wuraren kauwancin”. Inji Getso.

Hakazalika ya kara da cewa” Za a samu nasarar hakan ne kadai idan yan kasuwar suka baiwa sabon tsarin kawar da bola hadin kai, ta hanyar killace ta waje guda”. Inji Getso.

A cikin jawaban su, shugabannin kasuwannin sun sha al’awashin rungumar tsarin hannu bi-biyu domin kaiwa ga nasara.

Labarai

Rashin amfani da ƙananun kuɗaɗe na (Coins) yana kawo tsadar kayan masarufi – Masanin tattalin arziki

Published

on

Wani masanin tatttalin arziki a jihar Kano Dakta Ibrahim Ahmad Muhammad, ya ce rashin amfani da ƙananun kuɗaɗe na (Coins) kwandaloli, hakan kan haifar da koma baya musamman ma ga ƙasashen da basa amfani da su.

Dakta Ibrahim Ahmad Muhammad, wanda kuma shine shugaban sashin koyar da ilimin banking and finance na jami’ar tarayya ta Dutse, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Doka Gatan Al’umma na nan gidan rediyon Dala FM Kano, da ya gudana a yau Litinin.

“Dai na amfani da ƙananun kuɗaɗe na (Coins) yana kawo tsadar kayan masarufi, kuma idan mutum yaje sayen kayan masarufin zai fuskanci hakan, “in ji Dr. Ibrahim”.

Ya ƙara da cewa duk da cewar dai na amfani da ƙananun kudaɗen (Coins) da zarar an inganta harkar wutar lantarki, babu makawa za’a samu sauƙi saboda masu ƙananun masana’antu za su rage kashe kuɗi.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa Dakta Ibrahim Muhammad Ahmad, ya kuma bukaci hukumomi da su mayar da hankali akan noma da sanya kishin kasa a gaba, domin samar da ci gaba ga al’umma.

Continue Reading

Labarai

Zamu magance ƙalubalen da ake samu a fannin ilimi mai zurfi – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jahar kano ta sha alwashin mangance dukkanin wani ƙalubale a fannin ilimi mai zurfi a fadin jihar Kano.

Kwamishinan ilimi mai zurfi Dakta Ibrahim Yusif kofar mata, ne ya
bayyana hakan a yayin taron yaye daliban kwalejin ilimi ta Aminu
Kano (AKCOE), da ya gudana a ranar Alhamis.

Y kuma ce yanzu haka tattaunawa tayi nisa a hukumance akan bukatar kwalejin dan ganin ta samu wadataccenf ilin da za ta gina jami’a.

Dakta Ibrahim kofar mata ya bayyana gamsuwa da tsarin da kwalejin take bi wajen gudanar da karatu, inda ya kuma ja hankalin dalibai 40 da suka karbi shaidar kammala karatun NCE,
da su zama ababen koyi.

Da yake nasa jawabin shugaban kwalejin Dr. Ayuba Ahmad Muhammad, ya ce da zarar sun shiga sabon tsari za su fara da daukar dalibai yan asalin jahar Kano mutum dubu daya kyauta, tare da biyawa ‘yan makarantar
kudi sama da Naira miliyan 300 yan asalin jahar kano dan
karfafawa matasa gwiwa.

Wakilinmu Yusif Nadabo Isma’il ya rawaito cewa al’umma da dama ne suka samu damar halartar taron daga guraren daban-daban na jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

Continue Reading

Labarai

Bama jin daɗin yadda wasu iyaye suke hana ƴaƴan su maza auren mu – Budurwa mai larurar Ƙafa

Published

on

Wata matashiyar budurwa mai buƙata ta musamman dake da lalurar Ƙafa Samira Ahmad Tijjani, ta nuna rashin jin daɗin ta, bisa yadda mafi yawan iyaye suke nunawa masu lalurar ƙyama, wajen hana ƴaƴan su auren masu lalurar ƙafar lamarin da yasa al’amarin ke matuƙar ɓata musu rai.

A zantawar wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, da budurwar ta ce, mafi yawancin su mata masu lalurar ƙafar sun ma fi mata masu lafiya iya Girki, da sauran ayyukan yau da kullum.

Ta ci gaba da cewa, “Amma abin takaici sai a rinƙa nuna mana ƙyama, ko kuma wariya musamman ma wajen neman aure, bayan kuma ba mu muka yiwa kan mu halitta ba, “in ji Samira”.

Ta kuma ce abinda wasu daga cikin iyaye suke yi musu kan nuna ƴaƴan su ba za su aure mai lalurar Kafa ba, basa jin daɗin hakan, shi yasa ma ta fito domin ta sanarwa al’umma domin gujewa hakan.

A cewar ta, “Ko nima nayi soyayya mara misaltuwa da samari masu lafiyar Ƙafa, amma mahaifiyar ɗaya daga cikin su ta ce ita ba wai bata sona ba, amma tana jin kunyar ta tuna ni a cikin mutane cewar a zummar matar ɗan ta”.

Daga bisani dai ta yi kira ga al’umma da su dai na nuna ƙyamar ko kuma nuna wariya a gare su, bisa yadda iyayen su suke matuƙar shiga cikin damuwa a duk lokacin da aka nuna musu wariyar.

Continue Reading

Trending