Labarai
An yi ram da likitar bogi a Kano

A cigaba da zagayen tantance nagartar ayyukan lafiya a birnin Kano da kewaye, hukumar dake sanya ido kan asibitoci masu zaman kansu (PHIMA) ta bankado asirin wata likitar bogi a ranar Alhamis 20-02-2020.
Da yake jawabi ga manema labarai, babban sakataren hukumar, Dakta Usman Tijjani Aliyu, ya bayyana cewa sun gudanar da zagayen ne da hadin gwiwar bangaren mata na asibitin Abdullahi Wase, inda suka samu nasarar bankado asirin wata likitan bogi mai suna Samira Abubakar.
Dakta Usman ya ce” Likitar bogin na amfani da lasisin ma’aikaciyar jinya ta na gudanar da aikin fida da zubar da ciki ga masu juna biyu. Baya ga cajin marasa lafiya kudade da suka wuce kima. Likitar ta bogin na amfani da dalibai masu matakin karatu na sakandire a matsayin ma’aikatan jinya a asibitin na ta mai suna ‘Family Maternity’ dake yankin ‘Yan Kaba a kan titin Hadeja. Yanzu mun kulle asibitin domin baiwa ‘yan sanda damar gudanar da bincike a gabanin gurfanar da wanda a ke zargin a gaban kotu, duk da cewa ta cika wandon ta da iska lokacin da tawagar hadin gwiwar suka yiwa asibitin dirar mikiya”. Dakta Usman.

Labarai
Za mu ci gaba da karɓar tsofaffin kuɗi a Singa har nan da kwanaki 2 – Habibu Fantiya

Wani ɗan kasuwa dake kasuwar Singa a jihar Kano ya ce, Alhaji Habibu Yusuf Abdullahi Fantiyahar zuwa nan da kwanaki biyu za su ci gaba da karbar kudade a shagunansu, sai dai idan bankuna sun yi musu barazanar daina karbar tsofaffin kudi za su dakata.
Alhaji Habibu Yusuf Abdullahi Fantiya, ya bayyana hakan ne a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abubakar Sabo, yana mai cewar, al’umma daga garuruwa daban-daban sun shigo kasuwar, idan suka daina karɓar tsofaffin kuɗi za a cutar da su.
Akwai cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Labarai
Buhari zai tafi kasar Senegal

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari zai tafi ƙasar Senegal ranar Talata domin halartar taron ƙasa da ƙasa kan harkokin noma karo na biyu da za a gudanar a birnin Dakar.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adesina ya fitar ranar Litinin.
Taron wanda shugaban Senegal kuma shugaban ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU, Macky Salla zai karɓi baƙunci – an shirya shi ne domin samar da kyakkyawan yanayin noma domin ciyar da haniyar Afirka.
Mista Adesina ya ce maharta taron za su tattauna batun shigar da abinci da sauran kayan amfanin gona zuwa wasu ƙasashen, ciki har da Najeriya.
Ya ƙara da cewa yayin da nahiyar Afirka ke da mutum miliyan 249 da ke cikin ƙagin yunwa, taron – wanda shugabannin ƙasashen Afirka da ministocin kuɗaɗen da na noma na nahiyar, da ƙungiyoyin duniya za su halarta – zai saka aniyar kawar da yunwa a nahiyar Afirka nan da shekarar 2030.
Daga cikin tawagar da za ta yi wa shugaba Buhari rakiya zuwa taron har da ministan harkokin ƙasashen waje, Geoffrey Onyeama, da ministan noma da raya karkara, Dakta Mohammad Mahmood Abubakar, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasar Ambassada Ahmed Rufai Abubakar.

Labarai
Mun ƙara tsaurara matakan tsaro domin tunkarar zaɓen 2023 – NDLEA

A yayin da ya rage kwanaki 39 a fara fita babban zaɓen 2023 da ke ƙara gabatowa a ƙasa, hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA reshen jihar Kano ta ce, yanzu haka ta ƙara tsaurara matakan tsaro a gurare daban-daban na Kano domin kawar da masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.
Shugaban hukumar Alhaji Abubakar Idris Ahmad ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala a yau Litinin, inda ya ce shirin na hukumar ya shafi yayin da bayan zaɓen 2023 dake tafe.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su ƙara jan ƴaƴansu a jiki yayin da zaɓen 2023 ke ƙara ƙaratowa don kaucewa faɗawarsu cikin mawuyacin hali.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar, shugaban hukumar NDLEA ɗin na Kano Alhaji Abubakar Idris Ahmad, ya kuma ce yin amfani da miyagun kwayoyi ya kan sanya mutum yayi duk abinda ya wuce hankali bisa fita da suke yi daga hayyacinsu, a dan haka matasa su kaucewa sanya kan su a cikin harkokin shaye-shayen.

-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya8 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano