Connect with us

Labarai

An bada belin Mustapha Jarfa  

Published

on

A Alhamis din nan ne 20-02- 2020, kotun majistrate mai lamba 47 dake zaman ta a unguwar Gyadi-Gyadi ta sanya dan siyasan nan Mustapha Jarfa a hannun beli, bisa sharadin cewa sai ya kawo mai mataki na 14 a aikin gwamnati ko a karamar hukumar ko jiha ko kuma a tarayya tare da mutumin da ya biya haraji na shekara biyar, sharadi na uku shi ne ba zai yi magana a wata kafar sadarwa ba har sai an gama shari’ar. Idan kuma ya tserewa kotu wadanda suka tsaya masa za su biya naira dubu dari bibiyu.

Sai dai kasancewar bai cika sharudan ba, an sake mai da shi gidan ajiya da gyaran hali, inda a ka damka shi a hannun jami’in gidan, Babangida Sani da masu taimaka masa Nasir Ado da Mubarak Sani Karkarna.

Tun da fari dai a na zargin sa ne da tayar da hargitsi a cikin al’umma da barazana ga rayuwar mataimakin gwamnan Kano, Nasir Yusuf Gawuna da kuma bata masa suna harda zagi da cin mutuncin mataimakin gwamnan, ya kuma amsa laifin inda waccan lokutan majistrate mai lamba 34 ta yi masa hukuncin daurin shekara guda a gidan ajiya da gyaran hali ba kuma tare da zabin biyan tara ba.

A baya dai an gurfanar da shi ne a gaban kotun majistrate, mai lamba 34, dake zaman ta a Rijiyar zaki, inda yanzu kuma a ka canja masa kotun. Kamar yadda wakilin mu Abubakar sabo ya rawaito.

 

Hangen Dala

Zargin Almundahana:- An kama jami’in gwamnatin Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama Tasiu Al’amin-Roba, babban mataimaki na musamman (SSA), ga gwamnan jihar kano da kuma wani Abdulkadir Muhammad bisa zargin su da karkatar da kayan abincin tallafi a jihar Kano.

 

Kwamishinan ‘yan sandan, Hussaini Gumel, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN hakan a wata hira ta wayar tarho a ranar Lahadi cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani dakin ajiyar kaya da ke Sharada dauke da jakunkuna sama da 200.

 

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun yi awon gaba da shinkafa da masara a ma’ajiyar da ke Sharada.

 

“Tun daga lokacin ne muka fara bincike mai zurfi don gano buhunan masara ko shinkafa nawa aka diba aka sayar da su,” inji shi.

 

Gumel ya ce za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu bayan kammala bincike .

Continue Reading

Hangen Dala

An yiwa kasafin Kudin 2024 karatu na biyu

Published

on

Majalisar Dattawan Najeriya da ta Wakilai sun yi wa kasafin kuɗin ƙasar na 2024 karatu na biyu ranar Juma’a kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya gabatar musu da shi.

A ranar Laraba ne Tinubu ya je majalisar tare da gabatar da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin abin da gwamnatinsa za ta kashe a 2024, kuma ya nemi ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da shi.

Sai dai shugaban bai bayyana adadin abin da kowace ma’aikata da hukumomin gwamnati za su samu ba a lokacin da ya yi gabatarwar, abin da ya jawo cecekuce da muhawara a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘yan majalisar na kokawa yayin muhawarar da suka yi ranar Juma’a game da ƙarancin bayanai kan kasafin, wanda suka ce ya sa sun mayar da hankali ne kawai kan abubuwan da Tinubu ya faɗa a jawabinsa.

Jam’iyyun adawa sun soki kasafin da cewa “na yaudara ne”, yayin da Shugaba Tinubu ya yi masa laƙabi da “kasafin sabunta fata”.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Kano za ta Kara inganta aikin Jarida

Published

on

Gwamnatin jihar kano tace za ta hada Kai da kungiyar ‘yan jarida masu magana a Radio da Television na kasa wato Society of Nigerian Broadcasters domin kara inganta aikin Jarida.

 

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Baba Halilu Dan Tiye ne ya tabbatar da hakan lokacin da ake kaddamar da ‘ya’yan kungiyar anan kano.

 

Baba Halilu yace duba da muhimmancin da aikin jarida ke dashi a tsakanin al’umma ya sanya gwamnatin Kano za ta cigaba da baiwa bangaren muhimmanci.

Taron Wanda ya gudana a cibiyar ‘yan Jaridu ta Kano ya samu halartar Mafi yawa daga cikin shugabannin kafafen yada labaran Dake Kano.

Continue Reading

Trending