Connect with us

Labarai

Mustapha Jarfa ya kasa cika sharudan kotu

Published

on

Tun ranar Alhamis din nan ce, kotun majistrate mai lamba 47 dake zaman ta a unguwar Gyadi Gyadi a Kano ta sanya dan siyasa, Mustafa Jarfa a hannun beli, bisa wasu sharuda cewa, sai ya kawo mai mataki na 14 a aikin gwamnati ko a karamar hukuma ko jiha koma a tarayyar kasar Nijeriya, da kuma mutumin da ya biya haraji na shekara biyar sharadi na uku shi ne ba zai yi magana a wata kafar sadarwa ba, har sai an gama shari’ar, Idan kuma ya tesrewa kotu wadanda suka tsaya masa za su biya Naira dubu dari bibiyu kowannan su..

To sai dai kasancewar bai cika sharudan ba, an kuma kama shi tare da kai shi gidan ajiya da gyaran hali, inda a ka damka shi a hannun jami’in gidan, Babangida Sani da masu taimaka masa Nasir Ado da Mubarak Sani Karkarna.

Baki shi ke yanka wuya inji masu iya Magana, domin kuwa tun da fari a na zargin Mustapha Jarfa da ta da hargitsi a cikin al’umma da barazana ga rayuwar mataimakin gwamnan, Kano Nasir Yusuf Gawuna da kuma bata masa suna, wanda kuma tun a baya ya musanta zarge-zargen.

A cikin tuhumar da a ke yi masa a baya akwai zagi da cin mutumcin mataimakin gwamnan na Kano, ya kuma amsa laifin inda waccan kotun majistrate mai lamba 34 ta yi masa hukuncin daurin shekara guda a gidan ajiya da gyaran hali ba kuma tare da zabin biyan tara ba.

A baya dai an gurfanar da shi ne a gaban kotun majistrate, mai lamba 34, dake zaman ta a Rijiyar zaki, inda yanzu kuma a ka canja masa kotun, kamar yadda wakilin mu Abubakar sabo ya rawaito.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending