Connect with us

Labarai

A rinka kula wajen daukar ‘yan Bijilante – Ado Gwambo

Published

on

Mataimakin shugaban karamar hukumar Gwale Alhaji Ado Gambo Ja’en, ya yi kira ga mambobin kungiyar sintiri ta Bijilante da su kara kulawa da mutanen da suke dauka a cikin kungiyar domin kaucewa daukar bata gari.

Ado Gambo, ya yi kiran ne lokacin da al’ummar garin Ajawa suka kaddamar da wani ofishin sintiri ta Bijilante a unguwar ta Ajawa dake yankin karamar hukumar Gwale.

Ya ce, “Kulawa tare da tantance mutanen da za su dauka domin zama cikakkun ‘yan kungiya, zai taimaka matuka wajen kaucewa daukar bata gari.”  A cewar Ado Gambo.
A nasa jawabin Babban kwamandan sintirin a karamar hukumar Gwale Shehu Muhammad Rabi’u, jan hankalin ‘yan kungiyar ya yi da su gudanar da aikin su bisa doron doka.

Al’ummar yankin na Ajawa da suka samar da ofishin jami’an sintirin, sun bayyana makasudin daukar wannan mataki ta bakin Mallam Nazifi Jafar Yakasai, ya na mai cewa, “Mun samar da kwamitin sintirin Bijilante din ne a yankin domin inganta tsaro”. A cewar Malam Nazifi.

Bashir Musa shi ne kwamandan ‘yan Bijilante a unguwar ta Ajawa ya ce, “Zamu yi kokari domin kawar da bata gari da su ke addabar unguwar ta Ajawa”. Inji Bashir Musa.

Hukumomin tsaro da dama ne suka halarci bikin bude ofishin sintirin, ciki har da DPO na karamar hukumar Kumbotso Abubakar Cika Zaki.

 

 

 

 

 

 

 

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending