Connect with us

Labarai

Wasu bata gari sun farwa ‘yan sintiri da sara a Kano

Published

on

Guggun matasan da a ke zargi sun farwa ‘yan sintirin yankin unguwar Danbare Da yankin karamar Hukumar Kumbotso da tsakar daren ranar Lahadi da misalin karfe 2:30 na dare.

Lamarin da ya jawo matasan da ba a iya gane ko su waye ba, sun hau yan Bijilanten da sara da makamai inda suka rinka saran su a kai nan da nan suka fadi shame-shame da jini a jikin su.

Mujitapha mai kula da yankin Dan inji a yankin na Danbare ya na daya daga cikin wadanda a ka sara ya ce” Muna cikin zagaye a tsakiyar dare da yake bamu da yawa a jiyan sai muka hangi wani gida an sa dogon tsani sai muka dauko shi zamu kai ofishin mu sai muka hadu da mutane kawai sai suka hau saran mu da makami duk da ina da maganin karfe”.

Bashir Salisu Yusuf shi ma ya na cikin wadanda a ka sara a kai ya ce” Sun zo unguwar mu Kwamandan mu ya kirawo mu domin mu shiga gidan mu gani, sai muka dako tsanin muna tafiya sai muka hadu dasu, mua haska fitilar chochilan sai suka haska mu munza ta abokan aikin mu ne, muna zuwa sai suka fara sarar mu a kai dukan mu mutane hudu kamar wani icen girki duk wanda a ka sara sai ya fadi kasa, yanzu haka guda daga cikin mu har yanzu bai san inda yake ba mai suna Haruna, kuma har yanzu ba za mu fasa aiki ba, ko za su kashe mu sai mun kare ran rayukan al’umma”. Inji Bashir.

Mai unguwar ta Danbare D Saifullahi Abba Labaran, a zantawar su da wakilin mu, ya ce” Mutane hudu a ka illata daya kuma a yanzu haka ya na asibit cikin wani mawuyacin hali, kuma al’umma su ta ya su da addu’a su kuma jami’an tsaro su shigo cikin lamarin su”. Inji Saifullahi.

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending