Connect with us

Labarai

Kotu ta ci tarar Hisba a Kano

Published

on

Babbar kotun tarayya mai lamba biyu dake zaman ta unguwar Gyadi-Gyadi karkashin mai shari’ah, A.O Aguata ta umarci hukumar Hisba da kwamandan ta da kuma dagacin garin Utai dake karamar hukumar Wudil da su biya wani mutum Naira dubu dari uku.

Tun farko dai wani mutum ne mai suna, Yunusa Hamza, wanda ya yi karar hukumar ta Hisba da kwamandan na ta da kuma dagacin garin na Utai da surukan sa, sakamakon sun hana shi yin addini yadda ya fahimta, ta hannun lauyan sa Barista saleh Idris Bello.

Shi dai mutumin, Yunusa Hamza, ya fahimci ya yi sallah raka’a daya da sujjada daya, har kuma ya umarci matar sa ita ma ta yi yadda ya fahimta, inda surukan sa wato iyayen ta suka ce ba su yadda ba, har kuma suka kai karar sa wajan dagacin garin, shi kuma ya gayyato shi daga bisani kuma bayan ya cutura ya sa a ka ballo masa reshen bishiya ya dake shi da shi.

Sannn kuma ya tura su wajan ‘yan sanda inda su kuma suka ce ya na da damar yin addinin sa yadda ya ga dama domin dokar kasa ta ba shi dama, daga nan kuma su ka dunguma zuwa hukumar Hisba ta garin Wudil suka kuma turo su zuwa shalkwatar hukumar dake Kano a nan suka tsare shi har kawana shida suka kuma sa shi diban kasa a cewar sa, lamarin da ya garza zuwa kotu ta hannun lauyan sa Saleh Idris Bello.

Sai dai bayan zama daban-daban a kotun, ta kuma yi hukunci cewa hukumar Hisba da kwamandan ta da kuma wancan dagacin da su biya shi Naira dubu dari uku, duk da dai shi Naira miliyan biyar ya nema da su biya shi, sakamakon tsare shi da suka yi suka azabtar da shi baya ga sa shi aikin wahala da suka yi. Kamar yadda wakilin mu Abubakar sabo ya rawaito.

 

Labarai

Zamu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƴan Jarida – Hukumar Zaɓe ta Kano

Published

on

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSEC, ta sha alwashin aiki kafaɗa-kafaɗa da ma’aikatan Jarida, musamman ma da zaɓen ƙananan hukumomin jihar nan 44 da ke tafe.

Sabon shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Manumfashi, ne ya bayyana hakan, yayin ziyarar da tawagar ƙuniyar matasan ƴan Jarida, ta Kano Youth Journalist Forum, suka kai masa a ofishin sa yau Alhamis, yayin da ya shafe kwanaki huɗu da kama aiki.

Ya kuma ce, za su yi aiki da ma’aikatan Jarida musamman ma yayin gudanar da ayyukan zaɓen ƙananan hukumomin Kano 44, da ke tafe, domin wayar da kan al’umma da ma samun nasara yayin zaɓen da ma bayan sa.

Farfesa Manumfashi, ya kuma ƙar da cewa, akwai buƙatar kowa ya bayar da tasa gudummawar a harkar zaɓe, domin kuwa yanzu haka suna ci gaba da aiki wajen shirya zaɓen ƙananan hukumomin.

Da yake nasa jawabin shugaban ƙungiyar matasa ƴan Jaridar ta jihar Kano Musa Zangina Adam, ya ce sun kai ziyarar ne, domin su ƙulla alaƙar aiki a tsakanin su da hukumar, bisa yadda kowanne ɓangare yake buƙatar juna, tare kuma da bayar da gudunmawar da ya kamata.

Zangina, ya kuma ce a shirye ƙungiyar su take wajen ci gaba da bibiyar al’amuran da suka shafi al’umma, tare da nusar da mahukunta dan ganin an wadata su da kayayyakin more rayuwa.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Kano za ta inganta filaye da bunƙasa duk ɓangarorin wasannin matasa – Kwamishinan Matasa da Wasanni

Published

on

Sabon kwamishinan ma’aikatar wasanni da ci gaban matasa na Jihar Kano Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya bada tabbacin cewar Gwamnatin Jihar za ta ɗauki matakin inganta filayen tare da bunƙasa duk wasu ɓangarorin wasanni da matasa ke yi.

Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki yau Asabar, tare da kai ziyara a wasu filayen wasannin dake ihar Kano.

Daga cikin filayen wasannin da ya ziyarta akwai filin wasa na Sani Abacha da ke ƙofar Mata, da filin wasa na Kano Pillars da ke sabon Gari, da kuma filin wasa na Ado Bayero Square dake unguwar Sabon Gari, sai kuma filin wasa na Mahaha da ke ƙofar Na’isa.

Da yake jawabi bayan kammala ziyarar kwamishinan wasannin da ci gaban Matasa na jihar Kano, Mustapha Rabi’u Musa kwankwaso, ya ce ya gudanar da ziyarar ce domin sanin halin da filayen wasannin ke ciki.

A lokacin ziyarar kwamishinan na tare da mai bai wa Gwamnan Kano shawara a kan harkokin wasanni Ambasada Yusuf Imam Ogan Ɓoye, da shugaban magoya bayan ƙungiyar ƙwallon Ƙafa ta Kano Pillars Alhaji Rabi’u Abdullahi Kawo, da kuma mai riƙon Shugabancin hukumar wasanni ta jiha Malam Bala Sani Shehu.

Continue Reading

Labarai

Muna sane da ƙarancin Ruwa a wasu sassan Kano – Hukumar rarraba ruwan Sha

Published

on

Hukumar rarraba ruwan sha ta jihar Kano ta ce matsalar rashin samun ruwa da ake fuskanta a wasu sassan jihar Kano, yana da alaƙa ne da lalacewar wani abun kan Famfo a madatsar ruwan da ke Tamburawa.

Shugaban hukumar Injiniya Garba Ahmad Bichi, ne ya bayyana haka yayin zantawar sa da manema labarai, ya ce cikin guraren da za’a yiwa gyaran har da madatsar ruwa ta Challawa da Watari, da amincewar gwamnatin jihar Kano.

Injiniya Garba, ya kuma ce suna sane da ƙarancin ruwan da ake fuskan ta a wasu sassan jihar Kano, amma nan gaba kaɗan za kammala gyaran kan famfon, domin ganin an wadata sassan jihar Kano, da ruwan domin ganin sun samu wani sauƙi.

 “Mu ma a ɓangaren mu Bama jin daɗin yadda al’umma suke rasa ruwa a sassan jihar Kano, kuma nan da ranar Litinin mutane za su fita daga cikin wannan matsala ta rashin Ruwa, a yanku nan su, “in ji shi”

Garba Ahmad, ya kuma ƙara da cewa matsalar fashewar Fayif da aka samu a ci gaba da aikin gadar mahaɗar Ɗan Agundi, yanzu haka suna kan ɗaukar mataki tsakanin su da kamfanin da suka taka har ya fashe, dan ganin an gyara al’ummar da ake baiwa ruwa su ci gaba da damu.

Continue Reading

Trending