Connect with us

Labarai

Hukumar shari’a ta bukaci al’umma su kara zage dantse kan tarbiyya

Published

on

Daraktan yada addinin musulunci na hukumar shari’a ta jihar Kano, Murtala Muhammad Adam, ya ce sai limamai sun bada gudunmawar su wajen dora al’umma bisa tarbiyya na wajen koyarwar alkur’ani da koyarwar sinar Annabi (S.A.W).

Murtala Muhammad Adam, ya bayyana hakan ne a yayin taron limamai na kananan hukumomin, Bagwai, Shanono, Bichi, Tsanyawa da kuma Kunchi a dakin taro na cibiyar addinin musulunci da ke karamar hukumar Bagwai.

Ya ce’’ Sai limamai sun daura al’umma a kan komawa kan gwadabe na magabata, sakamakon bakomai ba ne ya sanya musulmi ke cikin halin matsala a duniya, illa cewa Annabi ya fada cewa wannan abun zai same mu, idan muka sanya kin mutuwa a zuciyar mu’’.

Ya kara da cewar, ’’Wajibi ne sai kananan hukumomin sai sun taimakawa limamai da dukannin abun da su ke bukata na kayan aiki, yadda zai kasance an samar da malamai da za su koyar a cikin kauyuka’’. Inji Murtala Muhammad Adam.

Shi kuwa a nasa jawabin limamin masallacin Bichi, Malam Lawan Abubakar, ya ce ’’Aiki ne mai nauyi da a ka daura mana sakamakon al’ummar mu ta na jin kishirwa a bangaren addini, sannan su kansu masu hannu da shuni su ma su sauke nauyin da ya ke wuyan su, sakamakon cewa suna bukatar abubuwan hawa domin su shiga cikin kauyuka domin koyar da al’umma addinin musulunci’’. Inji Malam Lawan.

Bashir Imamu Shuwaki, shugaban hukumar shari’a na Kunchi, ya ce’’ Yanzu musulmi irin wadannan tarukan su ke bukata domin a fadakar da su abun da su ka shafi addinin musulunci baki daya, sakakamon gurbacewar tarbiya da a ke fama da ita a halin yanzu’’. Inji Shuwaki.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending