Connect with us

Labarai

Kotu ta dakatar da Muhuyi daga binciken sarkin Kano

Published

on

Babbar kotun tarayya karkashin, mai shari’a Lewis Alagua, ta dakatar da hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano da shugaban ta Muhuyi Magaji Rimin Gado daga bincike a kan sarkin Kano Muhammad Sanusi na biyu.

Cikin kunshin umarnin wanda sarkin Kano ya shigar da karar Muhuyi da hukumar sa da kwamishinan shari’a da gwamnan Kano, mai shari’a, Alagua, ya bayyana cewar kowa ya tsaya a matsayar sa yanzu magana ta dawo kotu.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Ismail ya ruwaito cewar, mai shari’a, Alagua ya sanya ranar 18 na watan Mayu domin jin kowane bangare ya gabatar da jawaban sa.

Hukumar karbar korafe-korafe ta gayyaci sarkin Kano cewar, ya bayyana a gabanta domin amsa wasu tambayoyi dangane da wasu zarge-zarge a ranar litinin mai zuwa.

Ko dayake yanzu maganar ta koma kotu. Ko a watan da ya gabata babbar kotun tarayya mai lamba biyu ta soke wani bincike da hukumar ta yi inda kotun ta ayyana cewar an tauyewa sarkin ‘yancin sa da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba shi

Labarai

Mu takaita dogon buri a cikin al’amuran mu – Limamin Tukuntawa

Published

on

Babban limamin masallacin Juma’a na Jami’urrasul dake unguwar Tukuntawa gidan maza a karamar hukumar Birni, Malam Abubakar Ahmad Sorondinki, ya ja hankalin al’umma da su guji son zuciya da kuma dogon buri a cikin al’amuran abin duniya domin cikin abubuwan da su ke halakar da Dan Adam.

Malam Abubakar Sorondinki, ya yi jan hankalin ne yayin hudubar juma’ar da ya gabatar, a masallacin Juma’a na Jami’urrasul.

Ya ce, “Manzon Allah ya gargadi al’umma da su takaita buri a cikin al’amuran su, saboda haka lallai kullum mu rinka tunanin ajalin mu ya na tare da mu, yin hakan zai kara mana tsoron Allah da kuma nisantar duk abin da zai sabawa Allah”. Inji Malam Abubakar Sorondinki.

Continue Reading

Labarai

Masu siyar da kayan masarufi su ji tsoron Allah kada su kara kudi – Aminu Gyaranya

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Amirul Jaishi, Malam Aminu Abbas Gyaranya, ya ce, al’umma su guji alfasha da rigima a watan auzmin Ramadan domin lokaci ne ibada da zikirai a ko’ina.

Ya ce, “Ana bukatar a yawaita ciyarwa da bayar da taimako, domin manzon Allah (S.W.A) ya na ninka kyautar sa watan Ramadan”.

Malam Aminu Gyaranya, ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa masu sayar da kayan masarufi, da su ji tsoron Allah kada su karawa kaya kudi su saukaka domin Allah zai ba su lada.

Continue Reading

Labarai

Watan Azumi: Mahukunta su nemi hanyar saukaka rayuwar al’umma – Limamin Gwazaye

Published

on

Limamin masallacin Juma’a na Ammar Bin Yasir dake unguwar Gwazaye, Malam Zubair Almuhammady ya yi kira ga mahukunta da su nemo hanyar da za su saukakawa rayuwar al’umma a watan azumin Ramadan.

Almuhammady, ya yi kiran ne a cikin hudubar juma’a da ya gabatar a masallacin na Ammar Bin Yasir.

Ya na mai cewa, “Allah ya jibintawa mahukunta al’amuran al’umma gaba daya, saboda haka akwai bukatar su nemo hanyar da za su saukakawa al’umma domin jin dadin rayuwa a watan azumi”.

Ya kuma ce, “Su sani cewa, kowane shugaba mai kiwo ne kuma Allah zai tambaye shi wannan amanar kiwon da ya ba shi a ranar gobe kiyama, saboda haka al’umma ba za su samu nutsuwa ba har sai sun sami abinci da kuma samar da tsaro a wannan lokaci”. Inji Malam Zubair.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!