Labarai
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas

Auren wanda ya samu tsaiko sakamakon wahalar da bisar shiga kasar Amurka ta yi wuya sakamakon kasar Amurka ta dakatar da bisar ta ga ‘yan Nijeriya har sai nan da wani lokaci.
Mahaifin mai jiran angwancewa, Malam Suleiman Isa, shi ne ya tabbatar da hakan ta wayar tarho da jaridar Daily trust, cewa yanzu haka matar da zai aura mai suna Jeanine Sanchez, ta na kokarin samo takardun izinin shiga kasar, amma da zarar ta samo za mu sanar da ranar da za a daura auren.
Matashi mai shirin zama ango a wannan watan na Maris, Isa Sulaiman, wanda ya ke aji na biyu mai karantar ilimin Geography a jami’ar Yusuf Maitama Sule, yanzu haka ya na nan ya na dakon ranar da za a saka auren su da ba Amurkiya, Jeanine Sanchez, sabuwar amaryar da zai aura.
A dai watan Janairun shekarar nan ne matashin mai shekaru 26 ya hadu da sahibar sa abar kaunar sa mai shekaru 46 ‘yar asalin kasar Amurka ta hanyar shafin Instgram wadda ta yi tattaki daga kasar Amurka ta kuma zo garin Panshekara dake karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano domin ta auri angon ta Isa Sulaiman.

Labarai
Cutar mashako ta bulla a wasu sassan Jigawa

Akalla mutum goma ne suka mutu bayan ɓarkewar cutar mashaƙo a kananan hukumomi 14 na jihar Jigawa.
Ma’aikatar Lafiyar jihar ce ta sanar wa manema labarai haka a Dutse, a yau Lahadi. Ta ce ana kuma zargin cewa mutum 91 sun kamu da cutar.
Babban sakatare a ma’aikatar, Dr Salisu, Mu’azu, ya ce zuwa yanzu, an tabbatar da mutum biyu da suka kamu da cutar a kananan hukumomin Kazaure da Jahun yayin da aka Ɗauki jinin wasu zuwa Abuja domin yin gwaji da tantancewa.
Mu’azu ya ce ɓarkewar cutar abin damuwa ne musamman ma ganin cewa ta ɓulla a yankunan da ba su taɓa yin riga-kafin ta ba.
A cewarsa, tuni ma’aikatar ta fara bincike domin tattaro bayanai daga yankunan da abin ya shafa.
Ya ce gwamnatin jihar tuni ta fara shiri don yin riga-kafi a yankunan domin kaucewa yaɗuwar cutar.

Hangen Dala
Hukuncin kotu:- Zamu daukaka Kara – Abba Gida Gida

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yace zasu ɗauki matakin ɗaukaka ƙara zuwa gaba domin tabbatar da adalci kan hukuncin da kotun sauraron korafe-korafen zabe ta yanke inda ta ayyana Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan da aka gabatar a watan Maris din 2023.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana a fadar gwamnatin Kano a daren laraba.
Gwamnan ya ƙara da cewa sun umarci lauyoyin su da su hanzarta wajen ɗaukaka ƙara ba tare da ɓata lokaci ba.
Ka zalika ya kuma ce wannan hukuncin bazai sanyar musu da gwiwa ba wajen ci gaba da gudanar da ayyukan da suka fara.
A ranar Laraba ne dai 20 ga watan Satumba 2023 kotun sauraron korafe-korafen zabe ta tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin Wanda ya lashe zaben Gwamnan Kano da aka gabatar a watan Maris. (more…)

Hangen Dala
Hukuncin zaben Kano:- An Kori ‘yan Jarida daga harabar kotu

Jami’an Ƴan Sanda sun hana ƴan Jarida shiga harabar Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe ta Kano.
Duk da asubanci da ƴan jarida suka yi, jami’an ƴan sanda sun yi ƙememe sun hana su shiga.
Ƴan sandan sun koro wakilan kafafen yaɗa labarai da dama zuwa can nesa da Kotun.
A yau ne dai za’a Yanke hukunci Kan karar da jam’iyyar APC ta shigar gaban kotun tana kalubalantar nasarar Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Ƙarin bayani na tafe.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Manyan Labarai4 years ago
Ba’amurkiya da masoyin ta sun hada cinkoso a kasuwar Sabon Gari