Connect with us

Labarai

Idan ba ka yi alwala yadda addini ya koyar ba da matsala –Mal Kidir

Published

on

Limamin masallacin, Usman Bin Affan dake unguwar Kuntau a yankin karamar hukumar Gwale, Malam Aminu Kidir Idris, ya bukaci a’lumma da su rinka kyautata alwalar su, daidai da koyarwar addinin musulunci.

Malamin ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Ibadat da ya ke zuwan muku a ranar juma’a na gidan rediyon Dala.

Ya ce” Matukar mutum ya yi alwala ba irin yadda addinin musulunci ya koyar ba, to wannan alwala ba ta inganta ba. Haka Kuma wajibi ne kowa ne musulmi ya rinka bibiyar littafan addini domin koyon yadda a ke alwala”. Inji Malam Kidir.

Labarai

Rahoto: Ma’aikatan jinya su kare kan su a kan Corona – Kungiyar ma’aikatan jinya

Published

on

Kungiyar ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta kasa reshen jihar Kano, ta bukaci ma’aikatan Jinya da Ungozoma da su ci gaba da kulawa da kan su yayin jinyar masu dauke da cutar Corona.


Shugaban kungiyar reshen jihar Kano, Kwamared Ibrahim Mai Karfi ne ya gargadi ma’aikatan yayin da kungiyar ta kai ziyara ma’aikatar lafiya ta jihar Kano a ranar Laraba.


Ya kuma ce, “Kamata ya yi idan al’umma sun ji yanayin su ya sauya, su yi kokarin tuntubar masana lafiya maimakon su je su sayi magani kai tsaye su sha”.

Continue Reading

Labarai

Rahoto: Matashi ya gurfana a kotu da zargin kisan kai

Published

on

Babbar kotun jiha mai lamba 3 karkashin mai shari’a Dije Abdu Aboki wani matashi ya gurfana akan zargin kisan kai.


Tun a ranar 24 ga watan Mayu na shekarar da ta gabata ne aka yi zargin matashin mai suna Muhammad Abdulmumin Dan Boy ya cakawa wani malamin makarantar Islamiyya wuka a kirji, sai dai a zaman kotun na baya matashin ya musanta zargin.


Domin jin cikakken rahoton saurari wannan.

Continue Reading

Labarai

Za mu ci gaba da tallafawa marayu da marasa ƙarfi – Sarkin Kano

Published

on


Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce, masarautar Kano ta na nan kan ƙudirin ta na ci gaba da tallafawa marayu da marasa ƙarfi.


Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar tallafawa marayu da mabuƙata ta Green Pasture and Home Innitiative.


Sarkin wanda ya samu wakilcin shugaban kwamitin lafiya na masarautar Kano, kuma Ɗan Kaden Kano Dr. Bashir Ibrahim Muhammad Ɗan Kade ya ce, dama haƙƙin masarautar ne kula da mabuƙata.Mista Ayo da Madam Comfort O-William na cikin jami’an ƙungiyar sun yi ƙarin haske kan dalilin kai ziyarar ta su ga mai martaba sarkin.

BS

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!