Connect with us

Labarai

Rashin kula ke jawo cutar hawan jinin ido ta Glaucoma- Dr. Umar

Published

on

Wani kwararren likitan ido a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, Dakta Umar Farouq Ibrahim, ya ce, cutar hawan jinin ido da aka fi sani da GLAUCOMA cuta ce da ake gadon ta tun daga iyaye.

Dakta Umar Faruk ya bayyana hakan ne da safiyar yau Talata a wani bangare na makon cutar dake gudana a jihar Kano.

Ya kara da cewar, “Akwai bukatar mutane su rinka ziyartar likitocin idanu da zarar sun ji yanayin idanuwansu ya canja maimakon amfani da magunguna barkatai ko zuwa wurin wadanda ba kwararru ba a fannin duba lafiyar ido”.

Dakta Umar Faruk Ibrahim, ya kuma ce, “Hanyar kare kai daga cutar ta hawan jinin idon ita ce wanke idanu sosai tare da ziyartar liikita a kowacce shekara”. A cewar Dakta Umar Faruq

Wakiliyar mu Aisha Ibrahim Abdul, ta ruwaito cewar, ana cigaba da wayar da kai game da illar cutar ta hawan jinin idanu a sassan jihar Kano domin dakile ta.

 

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Labarai

Dilolin Wiwi sun yanki mai unguwa da Wuƙa, tare da cizon shi a hannu, kan ya shana su sha da siyar da wiwi a Kano

Published

on

Wasu matasa da ake zargin ƴan Daba ne, kuma dilolin Wiwi, sun kai wa mai unguwar yankin Bachirawar Tukwane ƙarshen kwalta hari da muggan makamai.

Tun farko dai mai unguwar yankin Malam Mustapha ya shawarci matasan ne, da su dai na ɗaurin tabar Wiwi, da siyar wa a kofar gidajen mutane lamarin da ya tunzura matasan.

Matasan dai sun rutsa mai unguwar Bachirawar ne inda suka yi yunƙurin hallaka shi, bayan da suka yanke shi da Wuƙa, tare da cizon sa a Hannu, sai dai ‘yan ƙungiyar bijilante na yankin sun kawo masa ɗauki inda suka kama wani matashi mai laƙabin Kokuwa.

A lokacin ne kuma mutanen yankin suka yi yunƙurin ɗaukar doka a hannu, sai dai mai unguwar Bachirawa Malam Mustapha dan Bachirawa Gabas Malam Abdulkadir Dandiyo, sun kuɓutar da matashin inda aka mika shi ofishin ƴan sanda, ragowar matasan suka tsere.

Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar yankin Dakta Jibrin Sagir, ya ce a shirye suke su tinkari duk wani ɓata gari a yankin da yake addabar su.

Continue Reading

Labarai

Mata ku ƙara kula da tsaftar jikin ku a gidan auren ku – DCG Dr. Khadijah Sagir Sulaiman

Published

on

Mataimakiyar babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano a ɓangaren Mata, DCG Dakta Khadijah Sagir Sulaiman, ta shawarci matan aure da su ƙara kulawa da tsaftar jikin su musamman kan abinda ya shafi bakunansu, da kuma gaɓoɓin da suke riƙe Gumi a wannan yanayi na zafi da ake ciki.

Dakta Khadijah Sagir, ta bayyana hakan ne yayin rangadin bibiyar auren gatan da gwamnatin jihar Kano ƙarkashin Injiniya Abba Kabir Yusuf, tayi a baya, wanda ta fara da ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a jiya Lahadi, ina zaman ya gudana a ofishin Hisbah na ƙaramar hukumar.

DCG Khadijah, ta kuma ce matuƙar matan auren za su ƙara kulawa da tsaftar jikin nasu, hakan ka iya taimaka musu wajen ƙara wanzuwar zaman lafiya a tsakanin su da mazajen su.

Da take nata jawabin mataimakiyar kwamandan Hisbah ta ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a ɓangaren mata Malama Saratu Sheikh Nasiru Kabara, cewa ta yi, ziyarar rangadin abu ne da tayi farin ciki, kasancewar bata taɓa samun makamanciyar ziyarar ba sama da shekaru 15 da fara aikin ta a can.

Wakiliyarmu Hadiza Balanti Ceɗiyar ƴan Gurasa ta rawaito cewa, yayin ziyarar rangadin bibiyar auren gatan Dakta Khadijah Sagir Sulaiman, ta kuma rarraba wa matan auren kayan goge baki, da kuma abubuwan da ke ɗauke sansanar jiki mara daɗi wato alumun, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending