Labarai
Daurarru na da damar yin zanga-zangar lumana- DSC Musbahu
Mai magana da yawun gidajen ajiya da gyaran hali jihar Kano DSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya ce, mazauna gidajen ajiya da gyaran hali suna da damar yin zanga-zanga a cikin gidan domin suna da ‘yanci a ciki kamar kowa.
DSC Musbahu Lawan, ya bayyana hakan ne jim kadan bayan fitowa daga cikin shirin shari’a a aikace na gidan rediyon Dala a yau Talata.
Ya na mai cewa, “Matukar mazauna gidan ajiya da gyaran halin suna da wani korafi kuma suna ganin ta hanyar zanga-zangar za sufi samun mafita, to za su iya bin hanyar da ake bi domin gudanar da zanga-zangar lumana a gidan”.
Ya kuma kara da cewa, “Idan har mazauna gidan su ka yi zanga-zangar ba bisa ka’ida ba, akwai hukunci da hukumar gidan za ta dauka akan wadanda sukayi”. Inji DSC Musbahu
Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, DSC Musbahu Lawan kofar Nasarawa, ya kumace, hukumar gidan ba ta amince mazauna gidan su hada kungiya su yi zanga-zangar ba domin kuwa yin hakan kaucewa doka ne kuma za su iya fuskantar fushin hukuma.
Labarai
Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa
An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.
Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.
Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.
Hangen Dala
Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano
A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.
Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.
Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.
Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.
Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.
Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito
Labarai
Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure
Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.
Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.
Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.
Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.
-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su