Connect with us

Labarai

‘Yan fashi sun kara kai hari a Kano

Published

on

Wasu da a ke zargin ‘yan fashi da makami ne sun harbe wani mai jiran kanti, a yankin Gwazaye kan titin ring road, a jihar Kano.

Al’amarin dai ya faru ne da misalin karfe Tara saura na daren jiya Lahadi a wani kantin sayar da kayan masarufi.

A na dai zargin cewa wasu mutane ne da ba a tabbatar da ko su waye ba, sun shiga wani Babban kanti a Titin Ring Road da ya ratsa Gwazaye zuwa Samegu a yankin karamar hukumar Kumbotso.

shaidun gani da ido sun bayyana cewar mutanen sun je ne a mota dauke da jakunkuna bayan kuma sun shiga kantin suka fara kwace wayoyi da kudaden masu siyayya daga bisani kuma suka yi awon gaba da cinikin da a ka yi a kantin wanda kuma bayan sun daki mai jiran kantin ne suka juya domin dai tserewa sai kawai ya yi musu ihu lamarin da ya sa barayi nan take suka harbe shi a gefen cikin sa.

Zubairu Ibrahim, shi ne mamallakin kantin da a ka yi fashin, ya shaidawa wakilin mu Abba Isah Muhammad, yadda lamarin ya kasance ya na mai cewa“Kudin da ‘yan fashin su ka sace sun tasamma fiye da dubu dari hudu.
Mai jiran kantin mai suna Isyaku Ibrahim shi kadai a ka jikkata kuma da alama ‘yan fashin sun so hallakashi ne, amma yanzu haka ya na samun kulawa daga likitoci domin ceto rayuwar sa”.

Zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sanda ba ta ce komai ba game da afkuwar lamarin.

Labarai

Mai horas da kungiyar Southampton ya kara rattaba sabon kwantiragi

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Southampton, Ralph Hasenhuttl ya kara rattaba sabon kwantiragi a kungiyar ta Southampton.

Ralph Hasenhuttl mai shekaru 52 dan kasar Austrian ya karbi kungiyar ne tun a watan Disamba na shekarar 2018 wanda ya tsallake da su fadawa zuwa ajin ‘yan dagaji.

Mai horaswar ya dai rattaba sabon kwantiragi na tsawon shekaru hudu wanda zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2024.

Southampton dai ita ce kungiya da ta taba kwasar kashin ta a hannu har tsawon kwallaye tara da a ka zura mata a raga a gasar wanda Leicester City ta lallasa ta.

Continue Reading

Labarai

Naji dadi matuka da za a dawo gasar Premier -Mai horas da Liverpool

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce ya ji dadi sakamakon dawowa da za a yi gasar Firimiya a ranar 17 ga watan Yunin nan.

Klopp ya tabbatar da hakan ne ayayin tattaunawar sa da gidan rediyon BBC ya na mai cewa ya yi kewar wasan sakamakon hutun da a ka tafi na dakatar da wasan a ranar 13 ga watan Maris.

Ya ce” Na yi rashi sosai wannan abun mamaki ne domin kuwa abu ne mai amfani a rayuwa ta kuma wanda nake so, fatan kawai mutane za su dafawa abun domin ganin an kai ga gaci”. A cewar Klopp.

Liverpool ita ce dai a kan gaba da maki 25 wanda idan ta lashe gasar wannan dai shi ne karo na farko tun cikin shekaru 30 ba ta lashe gasar ba.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Za a ci kasuwanni a ranar da a ka bude Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bada dama ga ‘yan kasuwar jihar Kano da su bude dukannin kasuwannin su a ranakun da a ka bude jihar Kano.

Kwamishin yada labarai na jihar, Kwamrade Muhammad Garba ne ya tabbatar da hakan cewa tuni gwamnati ta baiwa ‘yan kasuwar dama bayan ganawa da su ka yi da gwamnati.

‘Yan kasuwar za su bude kasuwannin na su ne tun bayan cikin tsawon kwanaki sama da 50 a rufe sakamakon bullar cutar Corona a jihar Kano.

Da dama dai wasu daga cikin ‘yan kasuwan sun ci kasuwar su a bayan fage musamman ma wasu daga cikin ‘yan kasuwar Kantin Kwari yadda su ka rinka yin kasuwanci irin samfurin tafi da gidan ka.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish