Connect with us

Labarai

Kungiyar Arewa ta karrama Tijjani Adamu

Published

on

Kungiyar samar wa da matasa mafita a sana’o’in dogaro da kai wato Arewa Youth Enterprenuers ta karrama fitattu a jihar Kano masu bada gudunmawa ciki har da Tijjani Adamu na gidan rediyon Dala.

Kungiyar ta gudanar da taron karramawar ne a karshen makon da ya gaba ta, a yayin kaddamar da matasa dari biyu da suka koyi sana’o’in dogaro da kai da kuma gasar baje kolin fasaha a tsakanin matasan karo na farko.

A yayin taron an gudanar da jawabai kan sana’o’in dogaro da kai daga bakin shuwagabannin wasu kamfaninnuka masu zaman kan su da kuma malaman Jami’ar Bayero ta Kano.

Cikin taron akwai mawaka daga sassan jihohin kasar nan da suka baje hajar su ta waka a taron, sannan an nuna fasaha ta kere-kere ciki har da tukunyar iskar gas ta girki mai amfani da ruwa da bawon albasa da tumatur da kankana da kuma bawon lemon fata, inda aka cakuda su aka zuba a jarka, sannan aka sa iskar tif din taya wanda ya dinga bada iska ta zama iskar gas, ya zama wutar girki.

Sai kuma motoci da jiragen sama da kuma na’urar feshi a gona da matasan suka kera aka kuma basu lambobin yabo sakamakon abubuwan da suka kera.

Kungiyar ta Arewa Youth Enterprenuers ship, ta bakin shugaban ta, Balarabe Uba Abdullahi wanda aka fi sa ni da Balancy, ta ci alwashin tallafawa matasa masu basira a fadin Arewa tare da koya masu sana’o’in dogaro da kai a fadin kasar nan.

Labarai

An yankewa barawon wayar wutar lantarki hukunci

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gurfanar da wani matashi Muhammad Sabi’u a kotun majistret mai lamba 18, da ke unguwar Zangero karkashin mai shari’a Muhammad Idris.

Matashin ya gurfana ne a kotun, kan zargin kama shi ya sanya tsani a wani gida da ke unguwar Badawa da tsakar dare ya na yankar wayar wutar lantarki ya na zubawa a cikin buhu.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewar, kotun ta hori Muhammad Sabi’u da daurin watanni 6, ko kuma zabin tara na naira Dubu Talatin.

Continue Reading

Labarai

An ci gaba da shari’ar mutanen da su ka rataye makwabciyar su

Published

on

Kotun majistret mai lamba 18, da ke unguwar Zangero karkshin mai shari’a Muhammad Idris, ta ce a dawo da mutanen da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ya gurfanar da su a kotun, domin ci gaba da tuhumar su.

Cikin wadan a ke tuhuma sun hadar da Zakiyya Yahaya da Safiya Ishak da kuma Usman Tasi’u.

Tun a ranar Talatar da ta gaba ta ne mutanen su ka fara gurfana a gaban kotun a kan zargin hada baki da yunkurin kisan kai sakamakon rataye wata matar aure da su ka yi, amma kuma ba ta mutu ba.

Kunshin zargin da Dan sanda yake mu su ya bayyana cewar, mutanen sun hada baki sun je gidan wata mata Marsu’a Mukhtar, daga karshe kuma su ka rataye ta, ko da yake tun a ranar ta Talata sun musan ta zargin da a ke yi mu su.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, a kuma ranar ta Talata ce mai shari’a Muhammad Idris ya ce, a je a fadada bincike kasancewar mutum biyu daga cikin wadanda ke cikin kunshin tuhumar sun gudu.

 

 

Continue Reading

Labarai

An kama dan sandan da ya takurawa wata budurwa a Kano

Published

on

Wata mata da ke unguwar Hotoro bayan Depot ta kai korafin wani jami’in Dan sanda a shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano bisa zargin takurawa rayuwar ta da kuma cin zarafin ta da ya ke yi.

Matar ta kai korafin jami’in Dan sandan ne mai aiki a unguwar ta Hotoro ranar Alhamis domin a yi mata iyaka da shi.

Ta ce, “Akwai wani Dan sanda da a ke cewa Dan masani, to ya takurawa rayuwa ta, bayan an kai kara ta ya kamani a kan laifin da ba a bincike ni ba, ba’ a yi min komai ba, bayan na dawo gida kullum ya na bibiya ta ya na takurawa rayuwa ta. Ya taba zuwa ya same ni ba da kwakwkwaran sutura a jiki na ba, ya ce lallai sai na hau mota mun tafi, mutanen unguwa su ka fito su na ba shi hakuri ya ce, zai hada da su. Ni ba matar aure ba ce. Yanzu abubuwan sun yawa sai na kira dakin korafi na ‘yan sanda, kuma na zo na ga adalci karara, na gode wa Allah an taimaka min, kuma an kamo shi. Ba wani abu da yake kawo shi kawai in ya zo ya ce, in hau mota, ko kuma akwai kanne na mata guda biyu ya ce, suma lalle sai ya tafi da su”.

Ta kara da cewa, “Ya kamani ina jinin al’ada, na yi na yi ya barni in gyara jiki na, karshe ma’aikatan su ka ce ya barni in gyara jiki na ya ce a’a, har ya kasance su na kora ta saboda ina bata mu su wuri da jini, shi ne dalilin ya sa na kawo karar shi, ya na nan an kamo shi. Ni abun da na gani an taimake ni, kuma an gurfanar da shi a gaban manyan sa, kuma an yi adalci daidai gwargwado. Matakin da na ke so a dauka a raba ni da shi babu ni babu shi. Iya sanina abun da ya taba hada ni da shi ya taba cewa in bashi hadin kai naki”. A cewar matar.

A nasa bangaren Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, “Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, ya sa an kamo wannan Dan sanda kuma ya bada umarnin a yi binciken kwakwaf, duk wanda ya ke da gaskiya a ciki, za ta bayyana kuma za a yi adalci. Kai tsaye kowanne lokaci mu na bada lambar ofishin mu, ko kuma a zo kai tsaye, ko a je ofishin mu da ke kusa a sanar da D.P.O, shi kuma ya turo mutane zuwa ofishin na mu”. Inji DSP Kiyawa.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya kuma ja hankalin sauran jami’an ‘yan sanda da su yi aiki da gaskiya da rikon amana kamar yadda doka ta tanadar.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish