Connect with us

Labarai

Covid-19: An rufe wata makaranta mai zaman kanta a Kano na din din din

Published

on

Hukumar kula da makarantu ma su zaman kan su a jihar Kano, sun garkame wata makaranta mai zaman kanta mai suna, Brilliant Academy sakamakon kin bin umarnin da gwamnatin Kano ta yi na rufe makarantu a fadin jihar.

Shugaban hukumar, Musa  Abba Dan Kawu, ya tabbatar da rufe makarantar bayan da tawagar hukumar da suke da alhakin bibiyar ganin an rufe duakkanin makarantu a jihar Kano saboda cutar Corona.

Makarantar mai suna, Brilliant Academy dake unguwar rijiyar Zaki an dai bada umarnin rufe ta na din din din.

Rufewar ta biyo bayan zargin  kin bin umarnin gwamnati da mahukuntan makarantan suka yi, na cigaba da harkokin su, na koyo da koyarwa a safiyar Litinin.

Daliabn makarantar da suka zo makarantar da kayan makaranta a ranar da aka ce kada a bude makarantu a Kano.

Wakilin mu Abubakar Sabo da ya ganewa idanun sa a lokacin da daliban ke kai kawo a harabar makarantar, ya kuma ji ta bakin mahukuntan makarantar  sun ce,  sun bude makarantar ne domin su sanar da yaran halin da a ke ciki ba wai sun bude da nifin yin karatu ba.

Hakan ce ta sanya wakilin na mu ya garzaya hukumar inda shugaban ta, Dan kawu ya tabbatar da rufewar, kuma cewa ba za su saurarawa kowacce makaranta da ta yi kunnen kashi da umarnin gwamnati.

Daga bisani Dan kawun ya bukaci al’umma da su taimaka musu wajan sanar da su da zarar sun ga wata makaranta a bude da zummar za su yi karatu a wannan lokacin da gwamnati ta ce a rufe makarantu.

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending