Connect with us

Labarai

An cimma matsaya tsakanin ‘yan kasuwa da gwamnati kan wutar Solar

Published

on

Kwamishinan kasuwanci masana’antu da ma’adanai na jihar Kano, Alhaji Mahmud Muhammad Hantsi, ya bayyana cewa sabanin da aka samu a baya tsakanin ‘yan kasuwar Sabon Gari da shugabanin kasuwar kan na’ura mai amfani da hasken rana izuwa yanzu an samu dai-daito a tsakani.

Alhaji Mahmud Hantsi, ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai da hukumar ta gudanar a ranar Litinin,

Yayin zaman taron na sulhu

Ya ce” Gwamnati ta samar da na’urar mai amfani da hasken rana Solar ne ga ‘yan kasuwar ta Sabon gari domin kara samar da tsaro da kuma kare rayukan al’umma a cikin kasuwar. Kuma a yanzu haka mun samarwa da ‘yan kasuwar tsari na zamanantar da kasuwancin su a shafukan internet wanda kowan ne dan kasuwa zai iya yin rijistar kasuwancin sa ta shafukan”. Inji Hantsi.

Da yake nasa jawabin a yayin taron Shugaban kasuwar Sabon Gari, Alhaji Uba Zubairu Yakasai, cewa ya yi “Mun samar da na’urar SolaR a kasuwar ne da sanin gwamnatin jihar Kano”. A cewar Uba Zubairu,

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Kwamishinan Kasuwancin Alhaji Mahmuda Muhammad Hantsi, ya kuma shawarci ‘yan kasuwa da cewar, matukar su ka ga wani bakon abu da basu gamsu da shi ba daga lafiyar ‘yan kasuwar su sanar da manyan kasuwanni domin gudun kamuwa da cutar Corona Virus.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Mun kammala shirin tunkarar aikin Hajjin bana -Muhammad Danbatta

Published

on

Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano Muhammad Abba Danbatta, ya ce, ya zuwa yanzu hukumar ta kammala shirin ta tsaf domin tunkarar al’amuran aikin hajjin bana.

Alhaji Muhammad Abba Danbatta ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da gidan rediyon Dala da safiyar yau Laraba.

Yana mai cewa, “Duba da wannan yanayi ake ciki na fama da annobar Coronavirus, ya sanya hukumar samar da sabbin tsare-tsare domin ganin an gudanar da aikin hajjin bana lafiya”.

Kazalika ya kara da cewa, “Gwamnatin jihar Kano ta kara kawo sabbin hanyoyin gwaje gwajen maniyyata domin tabbatar da lafiyar su kafin tafiya aikin hajji”. A cewar Muhammadu Danbatta.

 

 

Continue Reading

Labarai

Matasa sai sun rinka riko da sana’ar hannu -Isma’il Unique

Published

on

Wani kwararren mai sana’ar dinki a jihar Kano Isma’il Abdullahi Adam mai gidauniyar taimakawa marasa karfi ya ja hankalin matasa da su kasance masu dogaro da kai ta hanyar riko da sana’o’in hannu.

Isma’il Abdullahi ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Wannan Rayuwa na gidan rediyon Dala wanda ya gudana a yau Laraba.

Ya ce, “Kamata yayi idan mutum ya tashi ace ya san inda zai je domin gudanar da wata sana’a maimako zama yana jiran zuwan samun aikin gwamnati”.

Kazalika, kara da cewa, “Akwai sana’o’inmu na gado da ya kamata al’umma su rinka zamanantar da su, su bunkasa maimakon watsi da su”. A cewar Isma’il Abdullahi.

Continue Reading

Labarai

Gwamnati sai ta kara tsaurara matakan shigowa Kano -Danbaito

Published

on

Wani Lauya mai zaman kansa a jihar Kano Barista Umar Usman Dan Baito, ya ce, kundin tsarin mulkin kasa sashi na 305, ya bawa Shugaban kasa damar da zai saka dokar ta baci a cikin kasar da yake mulki matukar hakan zai samar da mafita akan wani yanayi da kasar ta shiga.

Barista Dan Baito ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Shari’a a aikace na gidan Rediyon Dala, wanda ya gudana a yau Laraba.

Ya ce, “Dokar kasa ta kuma bayar da damar daukan mataki ga dukkanin mutumin da ya karya dokar da gwamnati ta sanya”. Inji Dan baito.

Dan Baito ya kuma yi kira ga gwamnatin Kano da ta kara tsaurara matakan tsaro kan dokar rufe iyakokin kano da aka yi, kasancewar duk da an rufe iyakokin, amma mutane suna cigaba da shigowa Kano ta barauniyar hanya daga wasu jahohinn kasar nan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish