Connect with us

Labarai

Kano: Wata mata ta rotse kan facalar ta da tabarya

Published

on

Wata mata an yi zargin ta rotse kan facalar ta da tabarya, ta kuma kada ita a kan yaron cikin da ta dauke da shi, wadanda ke zaune a gida daya a unguwar Birget PRP a jihar Kano.

An yi zargin dai facalolin sabani ne ya gifta a tsakaninsu, inda matar kanin Khadija Isma’il, ta yi amfani da tabarya ta rotse kan matar wan mijin nata mai suna Jamila Shehu.

Bayan dai an kai al’amarin gaban alkali, kafin akai ga fara sauraron karar, sai aka rarrashi wacce aka yi wa rotsen har aka akai daidaiton cikin gida, da sharadin za’a dauki dawainiyar magungunata da suka shafi kanta da kuma yaron cikin nata, inda ana zuwa kotun sai ta ce ta yafe.

To amma daga baya tayi ikirarin an bar su da dawainiyar maganin, ta na ta faman wahala ga cuta taki ta kare, kullum ciwon kai babu barci, har takai an yi mata gwajin kwakwalwa, cikin da take dauke da shi kuma likita ya gwada ya ce yaron ya mutu, haka aka haife shi barai, sannan kuma ta zo ta na gwaba mata magana ta na cewar, wai ta yiwa banza harma ta na yi mata gwalo.

Kwanaki kadan da fauwar al’amarin, sai aka wayi gari ba’a ga wannan mata ba, inda matar ta bayyana cewar, garin ne ya yi mata zafi shi yasa tayi hijira.

Ya zuwa yanzu dai, da yake an gano ta, sai suka yanke shawarar a koma kotun ta shari’ar musulinci dake Goron Dutse, a bude karar a nema mata hakkinta.

Inda a zaman kotun na wannan lokaci kotun ta bukaci da aka kawo rubutacciyar sheda daga likita, ta kuma dage shari’ar zuwa 30 ga watan gobe.

A zantawar mu da mijin wadda ake zargin Idris Ahmad, bai yi musun cewa, matar tasa ta yi rotsen ko kaye akan yaron cikin ba, ya kuma tabbatar da cewa an yi sulhun sun kuma dauki nauyin maganin, amma duk wadanda ta ce taje ta biya a aljihunta, bada saninsu ta yi su ba, zancen fadar maganganu bayan sulhun kuwa, ya ce bashi da masaniya.

Alhaji Muhammad Bello Gadon Kaya shi ne shugaban kungiyar kare hakkin Dan adam da jin kai ta kasa wato Human Right Foundation of Nigeria, ya ce, suma sun ci karo da al’amarin a kotun kuma matar da mijinta sun shigar da korafi domin za su ci gaba da bin shari’ar.

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Mun kammala shirin tunkarar aikin Hajjin bana -Muhammad Danbatta

Published

on

Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano Muhammad Abba Danbatta, ya ce, ya zuwa yanzu hukumar ta kammala shirin ta tsaf domin tunkarar al’amuran aikin hajjin bana.

Alhaji Muhammad Abba Danbatta ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da gidan rediyon Dala da safiyar yau Laraba.

Yana mai cewa, “Duba da wannan yanayi ake ciki na fama da annobar Coronavirus, ya sanya hukumar samar da sabbin tsare-tsare domin ganin an gudanar da aikin hajjin bana lafiya”.

Kazalika ya kara da cewa, “Gwamnatin jihar Kano ta kara kawo sabbin hanyoyin gwaje gwajen maniyyata domin tabbatar da lafiyar su kafin tafiya aikin hajji”. A cewar Muhammadu Danbatta.

 

 

Continue Reading

Labarai

Matasa sai sun rinka riko da sana’ar hannu -Isma’il Unique

Published

on

Wani kwararren mai sana’ar dinki a jihar Kano Isma’il Abdullahi Adam mai gidauniyar taimakawa marasa karfi ya ja hankalin matasa da su kasance masu dogaro da kai ta hanyar riko da sana’o’in hannu.

Isma’il Abdullahi ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Wannan Rayuwa na gidan rediyon Dala wanda ya gudana a yau Laraba.

Ya ce, “Kamata yayi idan mutum ya tashi ace ya san inda zai je domin gudanar da wata sana’a maimako zama yana jiran zuwan samun aikin gwamnati”.

Kazalika, kara da cewa, “Akwai sana’o’inmu na gado da ya kamata al’umma su rinka zamanantar da su, su bunkasa maimakon watsi da su”. A cewar Isma’il Abdullahi.

Continue Reading

Labarai

Gwamnati sai ta kara tsaurara matakan shigowa Kano -Danbaito

Published

on

Wani Lauya mai zaman kansa a jihar Kano Barista Umar Usman Dan Baito, ya ce, kundin tsarin mulkin kasa sashi na 305, ya bawa Shugaban kasa damar da zai saka dokar ta baci a cikin kasar da yake mulki matukar hakan zai samar da mafita akan wani yanayi da kasar ta shiga.

Barista Dan Baito ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Shari’a a aikace na gidan Rediyon Dala, wanda ya gudana a yau Laraba.

Ya ce, “Dokar kasa ta kuma bayar da damar daukan mataki ga dukkanin mutumin da ya karya dokar da gwamnati ta sanya”. Inji Dan baito.

Dan Baito ya kuma yi kira ga gwamnatin Kano da ta kara tsaurara matakan tsaro kan dokar rufe iyakokin kano da aka yi, kasancewar duk da an rufe iyakokin, amma mutane suna cigaba da shigowa Kano ta barauniyar hanya daga wasu jahohinn kasar nan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish