Connect with us

Labarai

Har yanzu ba a samu tsayayyen maganin Covid-19 ba –Dakta Basheer

Published

on

Shugaban makarantar jami’an kula da lafiyar muhalli dake jihar Kano Dakta Basheer Bala Getso, ya ce, daga lokacin da cutar Coronavirus ta bulla a fadin duniya har izuwa yanzu ba’a samu tsayayyen maganinta ba.

Dakta Basheer, ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da Gidan Rediyon Dala a yau Talata.

Yana mai cewa, “Babu shakka al’umma ya kamata su dauki matakan kare kan su domin kaucewa kamuwa da wannan cuta ta Coronavirus ta hanyar tsaftace hannaye da rage shiga cikin cunkoson mutane”.

Ya kara da cewa, “Jita-jitar da al’umma suke yadawa kan cewa, cutar ba gaskiya bace, suna fada ne domin radin kansu, amman cutar covid-19 gaskiya ce kamar yadda ta bayyana a cikin wasu daga cikin sassan jahohin kasar nan”.

Dakta Basheer Getso, ya kuma ce, “Suma iyaye mata akwai bukatar su kara tsaftace wuraren da suke aikace-aikacensu na yau da kullum domin dugun kamuwa da cutar ta Covid-19”. A cewar Dakta Basheer Getso.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Dakta Basheer Bala Getso, ya kuma shawarci al’umma da su rinka amfani da abunda za su rinka tsohe bakunansu musamman ma idan za suyi tari ko atishawa a cikin al’umma.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Mun kammala shirin tunkarar aikin Hajjin bana -Muhammad Danbatta

Published

on

Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano Muhammad Abba Danbatta, ya ce, ya zuwa yanzu hukumar ta kammala shirin ta tsaf domin tunkarar al’amuran aikin hajjin bana.

Alhaji Muhammad Abba Danbatta ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da gidan rediyon Dala da safiyar yau Laraba.

Yana mai cewa, “Duba da wannan yanayi ake ciki na fama da annobar Coronavirus, ya sanya hukumar samar da sabbin tsare-tsare domin ganin an gudanar da aikin hajjin bana lafiya”.

Kazalika ya kara da cewa, “Gwamnatin jihar Kano ta kara kawo sabbin hanyoyin gwaje gwajen maniyyata domin tabbatar da lafiyar su kafin tafiya aikin hajji”. A cewar Muhammadu Danbatta.

 

 

Continue Reading

Labarai

Matasa sai sun rinka riko da sana’ar hannu -Isma’il Unique

Published

on

Wani kwararren mai sana’ar dinki a jihar Kano Isma’il Abdullahi Adam mai gidauniyar taimakawa marasa karfi ya ja hankalin matasa da su kasance masu dogaro da kai ta hanyar riko da sana’o’in hannu.

Isma’il Abdullahi ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Wannan Rayuwa na gidan rediyon Dala wanda ya gudana a yau Laraba.

Ya ce, “Kamata yayi idan mutum ya tashi ace ya san inda zai je domin gudanar da wata sana’a maimako zama yana jiran zuwan samun aikin gwamnati”.

Kazalika, kara da cewa, “Akwai sana’o’inmu na gado da ya kamata al’umma su rinka zamanantar da su, su bunkasa maimakon watsi da su”. A cewar Isma’il Abdullahi.

Continue Reading

Labarai

Gwamnati sai ta kara tsaurara matakan shigowa Kano -Danbaito

Published

on

Wani Lauya mai zaman kansa a jihar Kano Barista Umar Usman Dan Baito, ya ce, kundin tsarin mulkin kasa sashi na 305, ya bawa Shugaban kasa damar da zai saka dokar ta baci a cikin kasar da yake mulki matukar hakan zai samar da mafita akan wani yanayi da kasar ta shiga.

Barista Dan Baito ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Shari’a a aikace na gidan Rediyon Dala, wanda ya gudana a yau Laraba.

Ya ce, “Dokar kasa ta kuma bayar da damar daukan mataki ga dukkanin mutumin da ya karya dokar da gwamnati ta sanya”. Inji Dan baito.

Dan Baito ya kuma yi kira ga gwamnatin Kano da ta kara tsaurara matakan tsaro kan dokar rufe iyakokin kano da aka yi, kasancewar duk da an rufe iyakokin, amma mutane suna cigaba da shigowa Kano ta barauniyar hanya daga wasu jahohinn kasar nan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish