Connect with us

Labarai

Jami’ar Bayero ta musanta labarin bullar Corona a makarantar

Published

on

Jami’ar Bayero dake jihar Kano, ta musanta labarin da ake yadawa cewa an samu bullar cutar Coronavirus a makarantar.

Hakan na cikin wata sanarwa da Jami’ar ta fitar a karshen makon da ya gabata, wadda ke cewa babu kanshin gaskiya cikin zargin.

Sanarwar mai dauke da sa hannun wani jami’i a ofishin yada labarai na jami’ar ta Bayero Malam Lamara Garba ta ce, babu wani lamari dake kama da haka da ya faru a jami’ar.

Tun farko dai jami’ar ta Bayero ta umarci dalibanta a ranar Juma’ar da ta gabata da su koma gida sakamakon umarnin da Gwamnatin tarayya ta bayar domin dakile yaduwar cutar Corona.

Jami’ar ta kuma yi  kira ga al’umma da su kaucewa duk wani labari daka iya fita, idan ba jami’ar ce ta sanar da shi ba.

 

Labarai

An yankewa barawon wayar wutar lantarki hukunci

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gurfanar da wani matashi Muhammad Sabi’u a kotun majistret mai lamba 18, da ke unguwar Zangero karkashin mai shari’a Muhammad Idris.

Matashin ya gurfana ne a kotun, kan zargin kama shi ya sanya tsani a wani gida da ke unguwar Badawa da tsakar dare ya na yankar wayar wutar lantarki ya na zubawa a cikin buhu.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewar, kotun ta hori Muhammad Sabi’u da daurin watanni 6, ko kuma zabin tara na naira Dubu Talatin.

Continue Reading

Labarai

An ci gaba da shari’ar mutanen da su ka rataye makwabciyar su

Published

on

Kotun majistret mai lamba 18, da ke unguwar Zangero karkshin mai shari’a Muhammad Idris, ta ce a dawo da mutanen da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ya gurfanar da su a kotun, domin ci gaba da tuhumar su.

Cikin wadan a ke tuhuma sun hadar da Zakiyya Yahaya da Safiya Ishak da kuma Usman Tasi’u.

Tun a ranar Talatar da ta gaba ta ne mutanen su ka fara gurfana a gaban kotun a kan zargin hada baki da yunkurin kisan kai sakamakon rataye wata matar aure da su ka yi, amma kuma ba ta mutu ba.

Kunshin zargin da Dan sanda yake mu su ya bayyana cewar, mutanen sun hada baki sun je gidan wata mata Marsu’a Mukhtar, daga karshe kuma su ka rataye ta, ko da yake tun a ranar ta Talata sun musan ta zargin da a ke yi mu su.

Wakilin mu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, a kuma ranar ta Talata ce mai shari’a Muhammad Idris ya ce, a je a fadada bincike kasancewar mutum biyu daga cikin wadanda ke cikin kunshin tuhumar sun gudu.

 

 

Continue Reading

Labarai

An kama dan sandan da ya takurawa wata budurwa a Kano

Published

on

Wata mata da ke unguwar Hotoro bayan Depot ta kai korafin wani jami’in Dan sanda a shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano bisa zargin takurawa rayuwar ta da kuma cin zarafin ta da ya ke yi.

Matar ta kai korafin jami’in Dan sandan ne mai aiki a unguwar ta Hotoro ranar Alhamis domin a yi mata iyaka da shi.

Ta ce, “Akwai wani Dan sanda da a ke cewa Dan masani, to ya takurawa rayuwa ta, bayan an kai kara ta ya kamani a kan laifin da ba a bincike ni ba, ba’ a yi min komai ba, bayan na dawo gida kullum ya na bibiya ta ya na takurawa rayuwa ta. Ya taba zuwa ya same ni ba da kwakwkwaran sutura a jiki na ba, ya ce lallai sai na hau mota mun tafi, mutanen unguwa su ka fito su na ba shi hakuri ya ce, zai hada da su. Ni ba matar aure ba ce. Yanzu abubuwan sun yawa sai na kira dakin korafi na ‘yan sanda, kuma na zo na ga adalci karara, na gode wa Allah an taimaka min, kuma an kamo shi. Ba wani abu da yake kawo shi kawai in ya zo ya ce, in hau mota, ko kuma akwai kanne na mata guda biyu ya ce, suma lalle sai ya tafi da su”.

Ta kara da cewa, “Ya kamani ina jinin al’ada, na yi na yi ya barni in gyara jiki na, karshe ma’aikatan su ka ce ya barni in gyara jiki na ya ce a’a, har ya kasance su na kora ta saboda ina bata mu su wuri da jini, shi ne dalilin ya sa na kawo karar shi, ya na nan an kamo shi. Ni abun da na gani an taimake ni, kuma an gurfanar da shi a gaban manyan sa, kuma an yi adalci daidai gwargwado. Matakin da na ke so a dauka a raba ni da shi babu ni babu shi. Iya sanina abun da ya taba hada ni da shi ya taba cewa in bashi hadin kai naki”. A cewar matar.

A nasa bangaren Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, “Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, ya sa an kamo wannan Dan sanda kuma ya bada umarnin a yi binciken kwakwaf, duk wanda ya ke da gaskiya a ciki, za ta bayyana kuma za a yi adalci. Kai tsaye kowanne lokaci mu na bada lambar ofishin mu, ko kuma a zo kai tsaye, ko a je ofishin mu da ke kusa a sanar da D.P.O, shi kuma ya turo mutane zuwa ofishin na mu”. Inji DSP Kiyawa.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya rawaito cewa, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya kuma ja hankalin sauran jami’an ‘yan sanda da su yi aiki da gaskiya da rikon amana kamar yadda doka ta tanadar.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish