Connect with us

Labarai

An gargadi ‘yan Bijilante kan daukar doka a hannun su

Published

on

Shugaban kungiyar ‘yan sintiri ta vigilant Group of Nigeria, Usman Muhammad Jahun, ya gargadi mambobin kungiyar da su kauracewa dukan wadanda suka kama da zargin aikata laifi.

Usman Muhammad Jahun ya bayyana hakanne a ganwar su da gidan Rediyon Dala, ya na mai cewa” Dukan mai laifi baya daga cikin tsarin aikin, a dominn haka yanzu mu ke hadin gwiwwa da jami’an tsaro domin ci gaba da bayar da horon sanin makamar aiki ga ‘yan sintirin a fadin Nijeriya”. Inji Usman.

Ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi da su tabbatar da tsarin biyan alawus din wata-wata, ga ‘yan kungiyar domn kara mu su kwarin gwiwwa kan irin gagarumar gudunmawar da su ke bayarwa wajen samar da tsaro a tsakanin al’umma.

Shugaban kuingiyar ta vigilant group of Nigeria, Usman Muhammad Jahun, ya kuma kara da cewa” Duk da cewar akwai dokar gwamnatin jiha a dukkanin jihohin da ‘yan sintirin su ke gudanar da aikin su, yanzu haka kuma, akwi dokar kasa a matakin gwamnatin tarayya wadda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sanyawa hannu”. Inji Usman Muhammad.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Mun kammala shirin tunkarar aikin Hajjin bana -Muhammad Danbatta

Published

on

Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano Muhammad Abba Danbatta, ya ce, ya zuwa yanzu hukumar ta kammala shirin ta tsaf domin tunkarar al’amuran aikin hajjin bana.

Alhaji Muhammad Abba Danbatta ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da gidan rediyon Dala da safiyar yau Laraba.

Yana mai cewa, “Duba da wannan yanayi ake ciki na fama da annobar Coronavirus, ya sanya hukumar samar da sabbin tsare-tsare domin ganin an gudanar da aikin hajjin bana lafiya”.

Kazalika ya kara da cewa, “Gwamnatin jihar Kano ta kara kawo sabbin hanyoyin gwaje gwajen maniyyata domin tabbatar da lafiyar su kafin tafiya aikin hajji”. A cewar Muhammadu Danbatta.

 

 

Continue Reading

Labarai

Matasa sai sun rinka riko da sana’ar hannu -Isma’il Unique

Published

on

Wani kwararren mai sana’ar dinki a jihar Kano Isma’il Abdullahi Adam mai gidauniyar taimakawa marasa karfi ya ja hankalin matasa da su kasance masu dogaro da kai ta hanyar riko da sana’o’in hannu.

Isma’il Abdullahi ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Wannan Rayuwa na gidan rediyon Dala wanda ya gudana a yau Laraba.

Ya ce, “Kamata yayi idan mutum ya tashi ace ya san inda zai je domin gudanar da wata sana’a maimako zama yana jiran zuwan samun aikin gwamnati”.

Kazalika, kara da cewa, “Akwai sana’o’inmu na gado da ya kamata al’umma su rinka zamanantar da su, su bunkasa maimakon watsi da su”. A cewar Isma’il Abdullahi.

Continue Reading

Labarai

Gwamnati sai ta kara tsaurara matakan shigowa Kano -Danbaito

Published

on

Wani Lauya mai zaman kansa a jihar Kano Barista Umar Usman Dan Baito, ya ce, kundin tsarin mulkin kasa sashi na 305, ya bawa Shugaban kasa damar da zai saka dokar ta baci a cikin kasar da yake mulki matukar hakan zai samar da mafita akan wani yanayi da kasar ta shiga.

Barista Dan Baito ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Shari’a a aikace na gidan Rediyon Dala, wanda ya gudana a yau Laraba.

Ya ce, “Dokar kasa ta kuma bayar da damar daukan mataki ga dukkanin mutumin da ya karya dokar da gwamnati ta sanya”. Inji Dan baito.

Dan Baito ya kuma yi kira ga gwamnatin Kano da ta kara tsaurara matakan tsaro kan dokar rufe iyakokin kano da aka yi, kasancewar duk da an rufe iyakokin, amma mutane suna cigaba da shigowa Kano ta barauniyar hanya daga wasu jahohinn kasar nan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish