Connect with us

Labarai

Covid-19: Ganduje ya bada umarnin rufe hanyoyin shigowa Kano

Published

on

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin rufe hanyoyin shigowa jihar Kano ciki har da filin jirgin sauka da tashi na Malam Aminu Kano daga Ranar juma’a mai zuwa 27 da watan Maris din da muke ciki da misalin 12 na dare, ga duk mai son shigowa jihar Kano ko kuma fita daga jihar to yayi kokari tsakanin yau Alhamis da gobe Juma’a.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Kano Abba Anwar, ya fitar mai dauke da sa hannunsa, ta ce, duk wata zirga-zirga ta shiga jihar Kano an dakatar take, ciki har iyakokinta na sama wanda duk mai ziyara daya zo ta filin jirgin malam Aminu Kano, ba zai shiga cikin gari ba zai cigaba da kasancewa akillace a filin jirgin, ba tare da ya shigo cikin gari ba.

Sanarwar ta kara da cewa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce, matakin abu ne mai wahala sai dai kuma ya zama wajibi duba da yadda wannan cuta take kara yaduwa da kuma hadarinta, don haka al’ummar jihar Kano dana kasar nan suyi hakuri da matakin a wannan mawuyacin halin da ake ciki.

Gwamna Ganduje, ya kuma kara da cewa, Gwamnatin za ta dauki dukkan matakan da suka dace domin ganin ta kare jihar Kano daga yaduwar cutar, tare da yin kira ga al’umma da su bada hadin kai ga jami’an lafiya da masu ruwa da tsaki domin ganin an samu nasara ta yakar cutar a fadin jihar da kasa baki daya.

Haka zalika, Gwamna Ganduje ya kuma bukaci al’umma dasu kaucewa shiga cikin cunkoso da wanke hannu da sabulu tare da rubanya addua ta wannan annoba.

 

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending