Connect with us

Labarai

Covid-19: Ganduje ya bada umarnin rufe hanyoyin shigowa Kano

Published

on

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin rufe hanyoyin shigowa jihar Kano ciki har da filin jirgin sauka da tashi na Malam Aminu Kano daga Ranar juma’a mai zuwa 27 da watan Maris din da muke ciki da misalin 12 na dare, ga duk mai son shigowa jihar Kano ko kuma fita daga jihar to yayi kokari tsakanin yau Alhamis da gobe Juma’a.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Kano Abba Anwar, ya fitar mai dauke da sa hannunsa, ta ce, duk wata zirga-zirga ta shiga jihar Kano an dakatar take, ciki har iyakokinta na sama wanda duk mai ziyara daya zo ta filin jirgin malam Aminu Kano, ba zai shiga cikin gari ba zai cigaba da kasancewa akillace a filin jirgin, ba tare da ya shigo cikin gari ba.

Sanarwar ta kara da cewa, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce, matakin abu ne mai wahala sai dai kuma ya zama wajibi duba da yadda wannan cuta take kara yaduwa da kuma hadarinta, don haka al’ummar jihar Kano dana kasar nan suyi hakuri da matakin a wannan mawuyacin halin da ake ciki.

Gwamna Ganduje, ya kuma kara da cewa, Gwamnatin za ta dauki dukkan matakan da suka dace domin ganin ta kare jihar Kano daga yaduwar cutar, tare da yin kira ga al’umma da su bada hadin kai ga jami’an lafiya da masu ruwa da tsaki domin ganin an samu nasara ta yakar cutar a fadin jihar da kasa baki daya.

Haka zalika, Gwamna Ganduje ya kuma bukaci al’umma dasu kaucewa shiga cikin cunkoso da wanke hannu da sabulu tare da rubanya addua ta wannan annoba.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Za muyi maganin masu shigowa Kano ta barauniyar Hanya -Ganduje

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce, basu gamsu da yadda direbobi har yanzu suke shigowa jihar Kano ta barauniyar hanya da fasinjoji ba, a don haka zasu dauki matakan dakile ratsen da direbobin suke yi.

Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a zantawarsu da wakilinmu Abba Isah Muhammad, yayin wata ziyarar ganin yadda iyakar shigowa jihar Kano take gudana, a jiya Litinin.

Ya kuma ce, “Duk barauniyar hanyar da ake bi domin shigo da fasinjoji za mu toshe ta, inda direbobin kan ajiye fasinjojin a baya, sai su shigo su hadu a hanya su karaso da su cikin jihar Kano”. A cewar Ganduje.

Wani mai sana’ar Achaba mai suna Ibrahim mazaunin Kwanar Dangora ya ce, “Da safe na tashi naga an rufe gate, kuma samun kudi ada yafi, yanzu ba gashi kaga ana wucewa ba, daga nan kwanar Dangora, wasu na karbar dari biyar amma ni dari biyu nake karba”.

Haka zalika, wani mazaunin Tunkuna a karamar hukumar Kiru, Abdullahi Idris ya bayyana cewa, “Muna ganin halin da masu tafiya ke shiga, wani ma zai sauka bashi da abinda zai ci, kuma ga ma’aikata in an bi nan su tare. mu nan da ake tare wa ba zai taru ba, sai dai duk hayyoyin nan a rufe. Akwai hanya mai zuwa Faki, Jan Marmara dake jihar Kaduna zaka iya haurowa ka shigo Kano”.

Shima wani direban mota, Muhammadu Kabir, ya ce, “mu dai jihar Kano Alhamdulillahi. mu na kaucewa jami’an tsaro mu shigo jihar Kano, amma komai yana iya faruwa, tunda an ce cuta ce da take bin iska, bayan an sa dokar shigowa jihar Kano da fasinjoji, na shigo Kano yafi sau biyu”.

Continue Reading

Labarai

Yadda kasuwar garin Dawakin Kudu ta ci a yau

Published

on

Yayin da jami’an lafiya da mahukunta suke bada shawarwarin takaita cakuduwa da al’umma da kuma yawaita wanke hannu domin kaucewa kamuwa da cutar Coronavirus, Dala FM ta ziyarci babbar kasuwar garin Dawakin Kudu dake jihar Kano.

A yayin ziyarar dai, mun iske al’umma na ci gaba da gudanar da harkokinsu ba tare da wani tsaiko ba, babu wasu matakai na hana cakuduwa ko wanke hannu da ake dauka a kasuwar, kamar yadda ‘yan kasuwar suka bayyana mana.

Wannan na zuwa ne yayin da manyan kasuwanni a kwaryar birnin Kano suka dauki matakai takaita cakuduwa da kuma tilasta wanke hannu ga masu zuwa kasuwannin.

Garin Dawakin Kudu dai bashi da nisa da kwaryar birnin Kano, domin kuwa tafiya ce mai nisan kilo mita ashirin da biyu, kuma al’umma na zirga-zirga daga garin zuwa birnin Kano a koda yaushe.

Dala FM, tayi kokarin jin ta bakin sarkin kasuwar, amma hakan ya ci tura, Kasuwar dai tana ci ne a duk ranar Talata, wanda take samun ‘yan kasuwa masu shigowa daga kauyuka daban-daban a cikin jihar Kano

 

Continue Reading

Labarai

Kudin trader money sun yiwa ‘yan Nijeriya kadan

Published

on

Wani masanin tattalin arziki a Kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi Dakta Abdussalam Muhammad Kani, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kara yawan alkaluman kudaden da zata baiwa ‘yan Kasa rance da ake kira Trader Money.

Dakta Kani ya bayyana hakan ne yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala.

Yana mai cewa, “Naira dubu goma da gwamnatin zata bayar sun yi kadan, idan akayi la’akari da halin matsin tattalin arziki da al’ummar kasa ke ciki”.

Ya kara da cewa, “Matukar gwamnatin ta kara yawan kudaden to babu shakka al’ummar wannan Kasa zasu amfana da tsarin matuka”. A cewar Dakta Kani.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish