Connect with us

Labarai

Covid-19: Makwabtan wasu kamfanoni sun koka kan cinkoson ma’aikata

Published

on

Wasu mazauna yankin dake makwabtaka da masana’antu a unguwar Ja’en sun koka kan yadda wasu masana’antu har yanzu basu rage cinkoso ba a cikin masana’antun su sakamakon fargabar barkewar cutar da suke ganin zai iya taba lafiyar iyalen su da ma al’ummar yankin.

Cikin zantawar da wakilin mu Abubakar Sabo, sun shaida masa cewa “Hakan kamar an kashe maciji ne ba a sare kan sa ba, sakamakon yadda ake tara al’umma sama da dubu biyu a gwamuste suna aiki ba kakkautawa, kuma an bukaci al’umma da su yi tazara na tsawon mita uku, domin haka suke bukatar a rufe kamfanin baki daya har sai hali ya yi, domin lafiya yafi kudi tun da har an rufe makarantu duk a kan cutar Corona” A cewar wani Mr Austine.

Haka zalika guda daga cikin yankin, Sani Idris Rabi’u Ja’en ya ce” Su har yanzu kamfani ba a ce komai a kan su ba, domin in har za a hana makarantu kamata ya yi su ma a dakatar da su, domin kuwa akwai barazana ga lafiyar al’umma”. Inji Sani.

Masana lafiya dai na kokarin jan hankalin al’umma cewa da su takaita shiga cinkoso da gwamutsa a cikin mutane domin ganin an dakile yaduwar cutar ta Covid-19 a Nijeriya,  wanda itama kanta gwamnatin jihar Kano ta dauki wannan gabaran na dakile yaduwar cutar a fadin Kano baki daya.

Labarai

Mai horas da kungiyar Southampton ya kara rattaba sabon kwantiragi

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Southampton, Ralph Hasenhuttl ya kara rattaba sabon kwantiragi a kungiyar ta Southampton.

Ralph Hasenhuttl mai shekaru 52 dan kasar Austrian ya karbi kungiyar ne tun a watan Disamba na shekarar 2018 wanda ya tsallake da su fadawa zuwa ajin ‘yan dagaji.

Mai horaswar ya dai rattaba sabon kwantiragi na tsawon shekaru hudu wanda zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2024.

Southampton dai ita ce kungiya da ta taba kwasar kashin ta a hannu har tsawon kwallaye tara da a ka zura mata a raga a gasar wanda Leicester City ta lallasa ta.

Continue Reading

Labarai

Naji dadi matuka da za a dawo gasar Premier -Mai horas da Liverpool

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce ya ji dadi sakamakon dawowa da za a yi gasar Firimiya a ranar 17 ga watan Yunin nan.

Klopp ya tabbatar da hakan ne ayayin tattaunawar sa da gidan rediyon BBC ya na mai cewa ya yi kewar wasan sakamakon hutun da a ka tafi na dakatar da wasan a ranar 13 ga watan Maris.

Ya ce” Na yi rashi sosai wannan abun mamaki ne domin kuwa abu ne mai amfani a rayuwa ta kuma wanda nake so, fatan kawai mutane za su dafawa abun domin ganin an kai ga gaci”. A cewar Klopp.

Liverpool ita ce dai a kan gaba da maki 25 wanda idan ta lashe gasar wannan dai shi ne karo na farko tun cikin shekaru 30 ba ta lashe gasar ba.

Continue Reading

Labarai

Covid-19: Za a ci kasuwanni a ranar da a ka bude Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bada dama ga ‘yan kasuwar jihar Kano da su bude dukannin kasuwannin su a ranakun da a ka bude jihar Kano.

Kwamishin yada labarai na jihar, Kwamrade Muhammad Garba ne ya tabbatar da hakan cewa tuni gwamnati ta baiwa ‘yan kasuwar dama bayan ganawa da su ka yi da gwamnati.

‘Yan kasuwar za su bude kasuwannin na su ne tun bayan cikin tsawon kwanaki sama da 50 a rufe sakamakon bullar cutar Corona a jihar Kano.

Da dama dai wasu daga cikin ‘yan kasuwan sun ci kasuwar su a bayan fage musamman ma wasu daga cikin ‘yan kasuwar Kantin Kwari yadda su ka rinka yin kasuwanci irin samfurin tafi da gidan ka.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish