Connect with us

Labarai

Covid-19: Gwamnati ta kara kaimi wajen yaki da Corona -SEDSAC

Published

on

Kungiyar bunkasa ilimi da al’amuran jama’a da demokradiyya SEDSAC, ta al’umma na da rawar da za su taka wajen dakile yaduwar cutar Coronavirus a cikin zamantakewar al’umma wajen kulawa da yaduwar cutar ta hanyar rage cinkoso.

Cikin wata sanarwa mai kunshe da sa hannun babban daraktan kungiyar, Kwamrade Hamisu Kofar Na’isa, ya sanyawa hannu a ka kuma rabawa manema labarai, kungiyar ta ce kamata ya yi gwamnati ta sa dokar ta bace wajen hana zirga-zirgar ababan hawa a dukannin titinan jihohin kasar nan baki daya domin gudun yada cutar a cikin jihohin Nijeriya.

Sanarwa ta kuma ce gwamnati da ta kara tsaurara matakan kariya sosai domin yakar cutar Covid-19 domin kuwa cutar ta na da matukar hadari ga rayuwar al’ummar Nijeriya da ma duniya baki daya.

Sannan ta kuma bukaci al’umma da su ci gaba da bin umarnin jami’an lafiya da kuma shawarwarin su, gudun kamuwa da cutar ta Covid-19 tare da bin duk wasu hanyoyi da za a magance yafuwar cutar domin kare lafiya baki daya.

Haka zalika, ta kuma ce tabbas wannan cuta ta Covid-19 ta kawo tasgaro a fannin a fannin da sauran al’amura, domin haka kamata ya yi gwamnati ta dauki matakin gaggawa domin farfado da fannin ilimi da sauran al’amura baki daya.

Sannan ta kuma shawarci gwamnatin tarayya da ta jiha da ta rage kudaden gudanar da manyan ayyukan gwamnati na wannan shekarar sakamakon farashin man fetur da ya yi kasa domin al’umma su amfana. Sakamakon cewa halin da a ke ciki na wajen tattalin arizki Nijeriya ta dogara da man fetur domin haka rage farashin man ba zai shafi tattalin arikin kasar nan ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Labarai

Mun kammala shirin tunkarar aikin Hajjin bana -Muhammad Danbatta

Published

on

Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano Muhammad Abba Danbatta, ya ce, ya zuwa yanzu hukumar ta kammala shirin ta tsaf domin tunkarar al’amuran aikin hajjin bana.

Alhaji Muhammad Abba Danbatta ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da gidan rediyon Dala da safiyar yau Laraba.

Yana mai cewa, “Duba da wannan yanayi ake ciki na fama da annobar Coronavirus, ya sanya hukumar samar da sabbin tsare-tsare domin ganin an gudanar da aikin hajjin bana lafiya”.

Kazalika ya kara da cewa, “Gwamnatin jihar Kano ta kara kawo sabbin hanyoyin gwaje gwajen maniyyata domin tabbatar da lafiyar su kafin tafiya aikin hajji”. A cewar Muhammadu Danbatta.

 

 

Continue Reading

Labarai

Matasa sai sun rinka riko da sana’ar hannu -Isma’il Unique

Published

on

Wani kwararren mai sana’ar dinki a jihar Kano Isma’il Abdullahi Adam mai gidauniyar taimakawa marasa karfi ya ja hankalin matasa da su kasance masu dogaro da kai ta hanyar riko da sana’o’in hannu.

Isma’il Abdullahi ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Wannan Rayuwa na gidan rediyon Dala wanda ya gudana a yau Laraba.

Ya ce, “Kamata yayi idan mutum ya tashi ace ya san inda zai je domin gudanar da wata sana’a maimako zama yana jiran zuwan samun aikin gwamnati”.

Kazalika, kara da cewa, “Akwai sana’o’inmu na gado da ya kamata al’umma su rinka zamanantar da su, su bunkasa maimakon watsi da su”. A cewar Isma’il Abdullahi.

Continue Reading

Labarai

Gwamnati sai ta kara tsaurara matakan shigowa Kano -Danbaito

Published

on

Wani Lauya mai zaman kansa a jihar Kano Barista Umar Usman Dan Baito, ya ce, kundin tsarin mulkin kasa sashi na 305, ya bawa Shugaban kasa damar da zai saka dokar ta baci a cikin kasar da yake mulki matukar hakan zai samar da mafita akan wani yanayi da kasar ta shiga.

Barista Dan Baito ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Shari’a a aikace na gidan Rediyon Dala, wanda ya gudana a yau Laraba.

Ya ce, “Dokar kasa ta kuma bayar da damar daukan mataki ga dukkanin mutumin da ya karya dokar da gwamnati ta sanya”. Inji Dan baito.

Dan Baito ya kuma yi kira ga gwamnatin Kano da ta kara tsaurara matakan tsaro kan dokar rufe iyakokin kano da aka yi, kasancewar duk da an rufe iyakokin, amma mutane suna cigaba da shigowa Kano ta barauniyar hanya daga wasu jahohinn kasar nan.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish