Connect with us

Siyasa

Abinda ya sa muka kori Gudaji Kazaure -APC

Published

on

Jam’iyyar APC a jihar Jigawa ta kori fitaccen dan majalisar nan Muhammad Gudaji Kazaure daga jam’iyyar.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabannin jam’iyyar APC na mazabar Yamma a karamar hukumar Kazaure su goma sha tara, ta ce shuwagabannin mazabar sun amince da korar Gudajin daga jam’iyyar.

Sanarwar mai dauke da kwanan watan ranar Laraba ta ce dukkanin shuwagabannin mazabar sun amince da wannan mataki na korar dan majalisar.

Sanarwar ta ce an kori Gudaji Kazaure ne saboda rashin bin dokokin jam’iyyar.

Gudaji Kazaure dai shi ne dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kazaure, da Roni, da Gwiwa da kuma ‘Yan Kwashi.

Labarai

Sayar da filin gidan rediyo: Mu na kalubalantar gwamnatin Kano – PDP     

Published

on

Jamiyyar PDP a Kano ta kalubalanci gwamnatin jihar Kano, kan batun zargin sayar da gidan rediyon manoma na unguwar Tukuntawa dake karamar hukumar birni.

Sakataren yada labaran jam’iyyar na Kano, Bashir Sanata ne ya bayyana hakan, ta cikin Shirin Hangen Dala.

Ya ce”Abun kunya ne a ce gwamnatin ta fito ta bayyana cewa rashin tsaro ne ya sanya ta za ta sayar da gidan rediyon manoma na Tukuntawa. Kamata ya yi gwamnatin APC ta yi koyi da abin da gwamnatin Rabiu Kwankwaso ta yi, na mayar da wasu wuraren da al’umma za su amfana”.

 

Continue Reading

Labarai

Wadanda ku ka zaba za su yi muku aiki yadda ya kamata- Ganduje

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya na da kwarin gwiwa jam’iyyar APC ce za ta lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 44 da kujerun kansiloli 484 a zaben kananan hukumomin ba tare da amfani da tursasa mai zabe ba ko tsoratar da shi.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan jefa kuri’ar sa a rumfar zaben shi mai lamba 008 a garin Ganduje, karamar hukumar Dawakin Tofa, ya ce”Jam’iyya mai mulki za ta lashe dukkanin kujerun la’akari da yawan fitowar jama’a da ya gani a cibiyar”.

A cewarsa, “Fitowar masu kada kuri’a da kuma gudanar da zaben cikin tsari abin birgewa ne, wanda hakan manuniya ce cewa zaben ya samu karbuwa a wurin mutane”. Inji Ganduje.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta rawaito cewa gwamnan ya kuma tabbatar da cewa wadanda suka zaba za su yi musu aiki yadda ya kamata.

Continue Reading

Labarai

Zaben kananan hukumomi: NBC ta gargadi ‘yan Jarida

Published

on

Hukumar kula da Kafafen yaɗa labarai ta ƙasa NBC, ta gargadi ‘yan Jarida da su kasance masu bin dokoki yayin gudanar da zaɓen kananan hukumomi da za’a yi a ranar Asabar 16-01-2021 mai zuwa a jihar Kano.

Daraktan hukumar mai kula da shiyyar Kano da Kaduna, Alhaji Abubakar Kumo ne ya bukaci hakan yayin ziyarar da ya kawo gidan rediyon Dala FM a ranar Laraba.

Yana mai cewa, “Matuƙar ‘yan Jarida, za su ƙara ƙaimi wajen bin dokoki a yayin gudanar da zaɓen, za’a ƙara samun ci gaba a fannin yaɗa labarai yayin gudanar da zaɓen”.

Ya kuma ce, “Babban maƙasudin kawo ziyarar shi ne, domin hukumar ta ƙara tunatar da ma’aikatan gidan, domin bin dokoki a yayin gudanar da ayyukan su musamman a lokutan zabe”. Inji Alhaji Abubakar Kumo.

Da yake nasa jawabin, mataimakin shugaban rukunin gidajen Freedom Radio, Adamu Ism’ila Garki, godiya ya yi da ziyarar da hukumar ta kawo, tare da kira ga kungiyoyin dake da hurumi cewa da su rinka kula da abubuwan dake faruwa a shafukan sada zumunta.

Wakiliyar mu Nafisa Isah Adam ta rawaito cewar, shugaban tashar Dala FM, Ahmad Garzali Yakubu ya ce sun karbi ziyarar hannu bibbiyu kuma suna fatan ci gaba da kulla alaka tsakanin hukumar ta NBC da kuma rukunin gidajen Radiyon.

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!