Connect with us

Labarai

Covid-19: Masu hannu da shuni su taimaka da sinadaren wanke hannu a Kano -Dr Nasir

Published

on

Covid-19: Masu hannu da shuni su taimaka da sinadaren wanke hannu a Kano -Dr Nasir

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen wadata asibitocin jihar da kayayyakin tsaftace hannu da sauran sinadarai domin tabbatar da tsaftar cibiyoyin lafiya.

Lokacin da ake mika kayan wanke hannaye

Babban daraktan hukumar kula da asibitocin jihar Kano, Dr. Nasir Alhassan Kabo ne ya bayyana hakan, yayin rabon kayan tsaftace asibitoci da marasa lafiya, a wani mataki na dakile shigowar cutar Coronavirus a fadin jihar Kano baki daya.

Dr. Nasir Alhassan Kabo ya ce” Shakka babu matakan kariya za su taimaka gaya wajen inganta lafiyar al’umma wadanda ke asibitoci da sauran mazaunan jihar”.

Wakilan asibitoci na karbar kayan sinadarin wanke hannu

Babban daraktan hukumar kula da asibitoci na jiha ya kara da cewa” Duba da cewa Gwamnati na iya bakin kokarin ta, akwai bukatar masu hannu da shuni su taimaka wajen samar da irin wadannan kayayyaki ga al’umma”. Inji Dr Nasir.

Wakilin mu Umar Idris Shuaibu ya rawaito cewa, hukumar kula da asibitoci ta jihar Kano ta raba kayayyakin kula da tsaftar hannaye da sauran sinadarai domin tabbatar da inganta lafiyar al’umma ga manyan asibitocin jiha da kuma cibiyoyin lafiya a matakin farko da dai sauran su.

 

Labarai

Ƴan kasuwa ku tsaftace magudanan ruwa bisa gabatowar Damuna – Ƙungiyar Amata ta kasuwar Singa

Published

on

An buƙaci ƴan kasuwa da su rinƙa tsaftace tare da gyara magudanan ruwa a cikin kasuwannin su, bisa yadda damuna ke ƙara gabatowa.

Shugaban ƙungiyar Amata reshen kasuwar Singa Alhaji Musa Ibrahim Ɗan gaske, ne ya bukacin hakan a zantawar sa da manema labarai, yayin kaddamar da tsaftace kasuwar da kuma gyara mugudanun ruwan kasuwar.

Alhaji Musa, ya kuma ce ta hanyar tsaftace magudanan ruwan ne za a gujewa kowacce irin ambaliyar ruwa a cikin kasuwanni.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Labarai

Ku tallafawa mazauna gidajen gyaran halin dan rage musu raɗaɗin rayuwa – Mallam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallacin Salafussaleh dake unguwar Ɗorayi ƙarama a jihar Kano, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’umma da su ƙara dagewa wajen tallafawa mazauna gidajen ajiya da gyaran hali, da masu buƙata ta musamman, domin rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.

Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya bayyana hakan ne yayin da suka tallafawa mazauna gidan gyaran hali na Goron Dutse, da kayayyakin Abinci, da kuma na gidan yara, a wani ɓangare na taya su bikin ƙaramar Sallah, wajen ganin sun samu farin ciki a bukukuwan ƙaramar sallar da aka gudanar.

Ya ce matuƙar masu hali za su rinƙa tallafawa mazauna gidan gyaran halin da abubuwan da suka sawwaƙa, babu makawa za’a rage musu wata damuwa ta yau da kullum.

Wakilinmu Yakubu Ibrahim Dogarai ya rawaito cewa, Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce daga cikin kayan abincin da suka kai wa mazauna gidajen akwai Tuwon Sallah, da garin Kwakwaki, da kuma sinadarin Ɗanɗano, da Sukari, domin ragewa mazaunan gidajen wani raɗaɗin rayuwa.

Continue Reading

Trending