Connect with us

Labarai

Covid-19: Mu tallafawa makotan mu da kayan abinci -Mai unguwar Danbare

Published

on

Mai unguwar yankin Danbare (D) a karamar hukumar Kumbotso, Saifullahi Abba Labaran, ya ce halin da a ke ciki kamata ya yi al’umma da su zauna su hada kai domin tallafawa juna wajen ganin marasa karfi a cikin al’umma sun samu abin kaiwa baki domin tsiratar da rayuwar su.

Saifullahi Abba Labaran, ya yi wannan kalaman ne lokacin da yake ganawa da gidan rediyon Dala a ranar Litinin din nan.

Ya na mai cewa ”Wannan halin da mu ke ciki sai dai mu ce innalilahi wa’inna ilaihi raji’un, ita masifa idan tazo in an san farkon ta ba a san karshen ta ba, to ni gaskiya kira da na ke yi da jama’a ba wai iya na Danbare ba Kano baki daya, kar mu daurawa gwamnati baki daya wannan nauyin na wannan masifar da a ke ciki a yanzu, shawarar da na ke bawa jama’a ya kamata mu hada kai da jama’ar gari da dagatai da masu unguwanni da limamai, mu zauna mu samu tallafi da za mu taimakawa al’ummar mu, sakamakon wannan rufe iyakar da a ka yi an shi ga wani yanayi, ba wai rufe iyakar kasa ba, rufe iyakar jihohi da a ka yi Kano gari ne na kasuwanci kowa in ka zauna da shi sai dai ka ji a na cewa ba kasuwanci ba harkar makarantu yara da matasa kowa na gida filayen wasanni duka an rufe. Ka ga idan ba zama mu tallafawa al’umma ba, ya kasance idan ka na da dafaffan abinci ka tallafawa makocin ka wanda ba shi da shi, sakamakon wanda zai fita sai da safe zai ci, mu kuma muna kusa da al’umma”.

“Al’umma na cikin unguwa wadanda su ke da hali su siyo kayan abinci ka zo ka rabawa al’umma hakan zai taimakawa al’umma sosai, sannan bangaren wanke hannu da rage shiga cinkoso a dai na, kuma mu na iya kokarin mu wajen baiwa al’umma shawara da su rinka siyan abun wanke hannu su na ajiyewa a wajen kasuwancin su”. Inji Saifullahi.

Saifullahi Abba Labaran mai unguwar Danbare D

 

Labarai

Rashin amfani da ƙananun kuɗaɗe na (Coins) yana kawo tsadar kayan masarufi – Masanin tattalin arziki

Published

on

Wani masanin tatttalin arziki a jihar Kano Dakta Ibrahim Ahmad Muhammad, ya ce rashin amfani da ƙananun kuɗaɗe na (Coins) kwandaloli, hakan kan haifar da koma baya musamman ma ga ƙasashen da basa amfani da su.

Dakta Ibrahim Ahmad Muhammad, wanda kuma shine shugaban sashin koyar da ilimin banking and finance na jami’ar tarayya ta Dutse, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Doka Gatan Al’umma na nan gidan rediyon Dala FM Kano, da ya gudana a yau Litinin.

“Dai na amfani da ƙananun kuɗaɗe na (Coins) yana kawo tsadar kayan masarufi, kuma idan mutum yaje sayen kayan masarufin zai fuskanci hakan, “in ji Dr. Ibrahim”.

Ya ƙara da cewa duk da cewar dai na amfani da ƙananun kudaɗen (Coins) da zarar an inganta harkar wutar lantarki, babu makawa za’a samu sauƙi saboda masu ƙananun masana’antu za su rage kashe kuɗi.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa Dakta Ibrahim Muhammad Ahmad, ya kuma bukaci hukumomi da su mayar da hankali akan noma da sanya kishin kasa a gaba, domin samar da ci gaba ga al’umma.

Continue Reading

Labarai

Zamu magance ƙalubalen da ake samu a fannin ilimi mai zurfi – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jahar kano ta sha alwashin mangance dukkanin wani ƙalubale a fannin ilimi mai zurfi a fadin jihar Kano.

Kwamishinan ilimi mai zurfi Dakta Ibrahim Yusif kofar mata, ne ya
bayyana hakan a yayin taron yaye daliban kwalejin ilimi ta Aminu
Kano (AKCOE), da ya gudana a ranar Alhamis.

Y kuma ce yanzu haka tattaunawa tayi nisa a hukumance akan bukatar kwalejin dan ganin ta samu wadataccenf ilin da za ta gina jami’a.

Dakta Ibrahim kofar mata ya bayyana gamsuwa da tsarin da kwalejin take bi wajen gudanar da karatu, inda ya kuma ja hankalin dalibai 40 da suka karbi shaidar kammala karatun NCE,
da su zama ababen koyi.

Da yake nasa jawabin shugaban kwalejin Dr. Ayuba Ahmad Muhammad, ya ce da zarar sun shiga sabon tsari za su fara da daukar dalibai yan asalin jahar Kano mutum dubu daya kyauta, tare da biyawa ‘yan makarantar
kudi sama da Naira miliyan 300 yan asalin jahar kano dan
karfafawa matasa gwiwa.

Wakilinmu Yusif Nadabo Isma’il ya rawaito cewa al’umma da dama ne suka samu damar halartar taron daga guraren daban-daban na jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

Continue Reading

Labarai

Bama jin daɗin yadda wasu iyaye suke hana ƴaƴan su maza auren mu – Budurwa mai larurar Ƙafa

Published

on

Wata matashiyar budurwa mai buƙata ta musamman dake da lalurar Ƙafa Samira Ahmad Tijjani, ta nuna rashin jin daɗin ta, bisa yadda mafi yawan iyaye suke nunawa masu lalurar ƙyama, wajen hana ƴaƴan su auren masu lalurar ƙafar lamarin da yasa al’amarin ke matuƙar ɓata musu rai.

A zantawar wakilinmu na ƴan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, da budurwar ta ce, mafi yawancin su mata masu lalurar ƙafar sun ma fi mata masu lafiya iya Girki, da sauran ayyukan yau da kullum.

Ta ci gaba da cewa, “Amma abin takaici sai a rinƙa nuna mana ƙyama, ko kuma wariya musamman ma wajen neman aure, bayan kuma ba mu muka yiwa kan mu halitta ba, “in ji Samira”.

Ta kuma ce abinda wasu daga cikin iyaye suke yi musu kan nuna ƴaƴan su ba za su aure mai lalurar Kafa ba, basa jin daɗin hakan, shi yasa ma ta fito domin ta sanarwa al’umma domin gujewa hakan.

A cewar ta, “Ko nima nayi soyayya mara misaltuwa da samari masu lafiyar Ƙafa, amma mahaifiyar ɗaya daga cikin su ta ce ita ba wai bata sona ba, amma tana jin kunyar ta tuna ni a cikin mutane cewar a zummar matar ɗan ta”.

Daga bisani dai ta yi kira ga al’umma da su dai na nuna ƙyamar ko kuma nuna wariya a gare su, bisa yadda iyayen su suke matuƙar shiga cikin damuwa a duk lokacin da aka nuna musu wariyar.

Continue Reading

Trending