Connect with us

Labarai

Covid-19: Da yawan ‘yan kasuwa ba Allah a ransu –Uba Zubairu

Published

on

Shugaban kungiyar shugabannin kasuwannin da su ke jihar Kano baki daya kuma shugaban kasuwar Sabon Gari, Alhaji Uba Zubairu Yakasi, ya ce idan ‘yan kasuwa ba su tausayawa al’umma ba a wannan lokaci ko ba don azumi ba, to babu shakka Allah ba zai tausaya mana ba.

Uba Zubairu ya yi wannan kiran ne a lokacin da rediyon Dala take ganawa da shi a kan halin da a ka shiga na lockdown.

Ya ce” Muaten mu gaskiya wallahi tallahi babu Allah a zukatan su, domin kuwa babu tausayi kayannan dukan su na gida ne, nawa a ke siyar da Sikari yanzu nawa a ka mayar dashi? nawa a ke siyar da Filawa na a ka mayar da ita? Nawa a ke siyar da shinkafa yanzu nawa a ka mayar da ita? Bamu da tausayi kuma, in dai ba mu tausaya ba a wannan karnin da a ka shiga ba, to wallahi mu ma ba za mu taba ganin daidai ba, Allah ya ce ka duba na kasa da kai ya tausaya maka shi kuma na kasa da kai sai ya girmamaka, da dukiyar da kake takama da duk arzikin da kake takama ba na ka bane, lokaci daya in Allah ya kifta shi Kenan ka gama. Ba kuma abun da za ka ce Allah, domin ya baka ne domin ka taimaki mutane ba wai don ka ci ba, duk wanda yake da arziki ya yi kokarin ya rabu da arzikin sa lafiya, ya kuma hadu da Allah lafiya, kuma muna jin abun da malamai ke fada duk arzikin da ka tara tun daga kan silasi za a tambaye ka, duk wanda ya takurawa wani sai Allah ya takura masa”. Inji Uba Zubairu.

Buhun Sikari a baya a na siyar da shi kasa da sha biyar, bayan kuma da a ka shiga Corona sai ya zama kasa da dubu ashirin, amma a iya zuwa jiya Alhamis buhun sikari ya kai dubu ashirin da shida zuwa da takwas, a yanzu a na siyar da ita dubu sha bakwai a iya jiya Alhamis wanda a ka kara mata Naira dubu biyar a kan kowa ne buhu.

 

 

 

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending