Connect with us

Labarai

Covid-19: Halin da Kano ke ciki abun tsoro ne -Ganduje

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da cutar Covid-19 ya yi watsi da jihar Kano duk da mawuyacin halin da jihar ta shiga.

Ganduje ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, ya ce lamarin da a ke ciki a Kano ya na da ban tsoro.

Ya ce “Halin da a ke ciki yanzu, wato mu na da babbar matsala, kuma zan iya cewa da kai wannan hali a yanzu haka dai gaskiya ba shi da kyau kuma abin tsoro ne. Babban abun da a ka dogara da shi a kokarin dakile Corona a jihar shi ne gwaji, wanda kumae an shafe kwanaki biyar zuwa shida wadanda a ka dauki samufurin su ba su san matsayin su ba. Kayan da ma a ke daukan (samfurin) a kai Abuja sun yi karanci, kuma ba kaya ne wanda gwamnati za ta je kasuwa ta saya ba. Yanzu haka wadanda a ka dauki samfurin su ba su san matsayin su ba, kuma za su ci gaba da hulda da mutane”.

Ya kuma ce “Saboda haka wannan babbar matsala ta kwamitin shugaban kasa na Abuja, shi kansa babban daraktar (hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa NCDC ya zo nan Kano ya kwana, to amma tun da ya tafi ba mu sake jin duriyar sa ba”. A cewar Ganduje.

Sai dai kuma kwamitin na shugaban kasa kan yaki da cutar Corona ya musanata wadannan zarge-zargen, inda ya ce su na bai wa Kano kulawa ta musamman.

 

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending