Connect with us

Labarai

Covid-19: Shawarwarin da Kwankwaso ya bawa Buhari a kan Kano

Published

on

Wasu shawarwari da tsohon gwamnan Kano, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya baiwa shugaban kasa, Muhammadu bUhari a kan yadda Kano ta tsinci kanta da annobar Coronavirus.

  1. Na farko dole sai gwamnatin tarayya ta shiga cikin lamarin domin ceto rayukan mutane sama da miliyan 10 dake zaune a jihar Kano domin akwai bukatar duba halin da a ke ciki.
  2. Gwamnatin tarayya ta kasance ita ce da alhakin kula da al’amuran da su ka shafi cutar a jihar Kano.
  3. Gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamiti mai inganci a kan yaki da cutar Covid-19 wanda dukannin mambobin ta kwararru ne a harkarkar wanda za su duba al’amarin.
  4. A kalla sai an samar da cibiyoyin gwajin cutar guda biyar tare da wuraren gwajin cutar guda 10 a jihar Kano.
  5. Sannan kwamitin karta kwana sai ya horas da jami’an lafiya ta yadda zai rinka karbar kididdigar adadin mace-macen da a ka yi a dukannin makabartun jihar Kano, haka zalika sauran jami’an lafiya su bincika wajen ganin sun san musabbabin mutuwar da a ka yi a Kano. Sannan su duba dukannin marasa lafiya tare da wadanda su ka ziyarci jana’iza wajenn ganin an tattaro su an kuma killace su baki daya domin yi musu gwaji.
  6. Duk da an karyata adadin mutanen da su ka mutu, wannan mace-macen da a ka yi ba mamaki su na da alaka ko dai cutar Covid-19 ko kuma wata cutar ta daban, domin haka gwamnatin jiha da ta tarayya dole sai sun duba wannan lamarin mace-macen da ta duba kan musabbabin ta, sannan dukannin masana a harkar lafiya sai sun duba a duk lokacin da a ka samu wani ya mutu.
  7. gwamnatin tarayya ta turo kwararrun jami’an lafiya wadanda za su bincika a kan mace-macen da a ka samu a jihar Kano.
  8. Tallafin kamata ya yi ya zaman a kowa da kowa kamar yadda matsalolin yunwa da talauci da cutar ta haifar ba wai sun takaita ga iya ‘yan wata jam’iyar siyasa ba.

Labarai

NAHCON ta sanya ranar fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa Saudiyya

Published

on

Yanzu haka hukumar Aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta 15 ga watan nan na Mayun 2024, a matsayin ranar da za’a fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana, zuwa ƙasa mai tsarki.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin shugaban hukumar ta NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, a wajen taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah, da ya gudana yau Alhamis birnin tarayya Abuja.

“Maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke Farali daga ƙasar nan a ƙasa mai tsarki; za su shafe aƙalla kwanaki huɗu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji, “in ji Arabi”.

Daga bisani shugaban hukumar aikin hajjin Jalal Ahmad Arabi, ya kuma bayyana cewa za ayi jigilar maniyyata aikin hajjin ne daga cibiyoyi 10 a faɗi ƙasar nan.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Laraba, 1 ga watan Mayun 2024, a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata na wannan shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.

Olubunmi, ya kuma sake nanata buƙatar ganin ma’aikata sun jajirce da yin aiki yadda ya kamata a dukkanib matakai daban-daban.

Continue Reading

Labarai

Wahalar Fetur ta haifar mana da koma baya a sana’ar mu – Mai Motar Haya

Published

on

Wani mai sana’ar tuƙin motar Haya, da kuma lodin fasinjoji mai suna Kabiru Muhammad, mazaunin ƙaramar hukumar Munjibir, ya ce ƙarancin motocin Haya da ake samu a yanzu, yana da alaƙa da wahalar man Fetur da ake fuskanta a sassan Najeriya.

A zantawar mutumin da wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il, ta cikin shirin rahotanni daga ƴan Zazu na yau Talata, ya ce a baya har motoci hamsin suke yiwa lodin fasinjoji su tashi, amma a yanzu Mota ɗaya suke iya cikawa sakamakon ƙarancin Fetur da ake fama da shi.

Ya kuma ce ƙaranci tare da tsadar man fetur ɗin da ake fama da shi, sun haddasa musu koma baya a sana’ar su, baya ga batun kuma matsalar da suke fuskanta da fasinjoji wajen biyan kuɗin Mota.

Wakiliyarmu da ta bibiyi shirin na ƴan Zazu Ummi Bala Ahmad ta rawaito cewa, matuƙin motar Kabiru Muhammad, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jahohi, da su yi abinda ya kamata dan ganin farashin man Fetur ɗin ya sauka, domin al’umma su samun sauƙi.

Continue Reading

Trending