Connect with us

Duniyar Bollywood

Bollywood: Jarumi Rishi Kapoor na fim din Yeh Vaada Raha ya rasu

Published

on

Shahararren jarumin Bollywood, Rishi Kapoor, ya rasu sakamakon rashin lafiya ta cutar leukemia da ya ke fama da ita.

Rishi Kapoor mai shekaru 67 ya rasu ne a ranar Alhamis a wani asbiti dake Mumbai bayan an kwantar da shi a ranar Laraba.

Iyalan marigayin su ne suka tabbatar da rasuwar ta sa, wanda tuni shugaban kasar India, Narendra Modi ya bayyana jimamaen sa a kan rasuwar jarumin, inda ya ce” Kapoor mutum ne mai basira mai son ci gaban kasar sa kuma babban mutum domin kuwa ina tuna ganawar mu da mu ka yi da shi a shafin sada zumunta”. A cewar Modi.

Shi ma jarumi Amitabh Bachchan ya yi matukar kaduwa da mutuwar abokin na sa.

A fitowar jarumin na farko a fim din Mera Naam Joker ya lashe kyautar gwarzon jarumi a shekarar 1970 wanda ya kuma yi fina-finai da dama sama da 90 ciki akwai Yeh Vaada raha a shekarar 1982, ,“Laila Majnu, “Debt,” “Moonlight,” “Sometimes,” “Sea” and “Lightning.” Sannan kuma a shekarar 1999, ya zama darakta a fim din “Let’s Go Back.”

Ya rasu ya bar matar sa, Nitu Singh,  wacce ita ma ta taba fitowa a wasu fina-finan da ya yi yayin da yabar ‘yar sa da dan sa, jarumi, Ranbir Kapoor wanda tauraruwar sa ke haskawa a yanzu a masana’antar Bollywood.

Ko a jiya Laraba sai da Irrfan Khan jarumi a masana’antar ya rasa ransa sakamakon rashin lafiya da ya sha fama da ita, wannan dai shi ne babban rashi da masana’antar Bollywood ta girgiza a cikin makwannan.

Duniyar Bollywood

Kannywood: Mu kaucewa yin kalaman da ba su dace ba – Ali Nuhu

Published

on

Jarumi kuma mai shirya fim a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, ya gargadi ƴan masana’antar da su kaucewa yin amfani da kalaman da ba su dace ba.

Ali Nuhu ya yi kiran ne jim kaɗan bayan fitowa daga cikin shirin Bollywood na gidan rediyon Dala FM Kano, wanda ya mayar da hankali a kan shirin fim din sa mai suna Bana Bakwai, wanda ya gudana a safiyar yau Laraba.

Ya na mai cewa”Matuƙar ƴan masana’antar ta Kannywood za su ƙara tsaftace kalaman na su, babu shakka za a samu gyara masana’antar”.

Ali Nuhu ya kuma ce fim ɗin sa mai suna Bana Bakwai ya zo da sauye-sauye wanda za a iya dangantashi da fina-finan Bollywood na ƙasar Indiya, inda ya ce shirin yafi mayar da hankali ne wajen magance ta’addanci da garkuwa da mutane da a ke fama dashi.

“Shirin Bana Bakwai zai samar da aikin yi ga matasa da dama dake Arewacin Nijeriya, bisa yadda a ka tsarashi”. Inji Ali Nuhu.

Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa, Jarumin kuma mai shirya fim, Ali Nuhu ya ce, cutar Korona bairus ta kawo tasgaro a cikin masana’antar su ta Kannywood, ba dan haka ba da tuni sun kammala shirin.

Continue Reading

Duniyar Bollywood

Jarumin Bollywood Irrfan Khan ya rasu ya na da shekaru 53

Published

on

An haifi jarumi, Sahabzad Irfan Khan a jihar Rajasthan a ranar 7 ga watan Janairu na shekarar 1967 wanda ya halarci makarantar fim ta National School Of Drama. Kuma a gwajin fim din Shakespeare da Chekhov su ne su ka bashi damar shiga masana’antar Indiya. Haka kuma ya fito a fim din Piku tare da Amitabh Bachchan da Deepika Padukone da kuma fim din The Lunchbox.

Marigayin ya kuma fito a fim din Slumdog Millionaire da Life of Pi tare da The Amazing Spider-Man.

A shekarar 2018 ne a ka gano Irfan Khan na fama da cutar neuroendocrine tumour, ya kuma rasu ne a asibitin Mumbai a yau Laraba.

Kafin rasuwar sa yabar matar sa Sutapa Sikdar wacce take gabatar da shirye-shirye a gidan Talabijin da kuma dansa Babil da Ayan. A yayin da mahaifiyar sa Saeeda Begum ta rasu a wannan watan da mu ke ciki wato ranar 25 yau tazarar kwanaki hudu da rasuwar mahaifiyar sa ke nan a garin Jaipur ta na da shekaru 95.

 

 

Continue Reading

Trending